AURE A ƘUNSHIYAR KARIN MAGANA
Na
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Karin magana wani dunÆ™ulallen zancen hikima ne mai cike da fasahar hoton rayuwar al’umma game da al’amuransu na yau da kullum. Reshe ne daga cikin rassan adabin baka, wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi da al’adun Hausawa waÉ—anda suka shafi aure, haihuwa, tarbiyya, zumunci, zamantakewa, tsarin jama’a da sauransu. Ya kasance wani madubi ne da ake iya hango abubuwan da Hausawa suka bai wa muhimmanci a rayuwarsu. Rayuwar aure kuwa, wani mataki ne da Hausawa suke bai wa matuÆ™ar muhimmanci. Hakan shi ya sa suka lulluÉ“e shi da karin magana masu yawa, tun daga matakin neman aure har zuwa rabuwa.
Ganin yadda yanayin zamantakewar auren Hausawa da kuma karin magana da aka gina game da shi, su ne suka haifar da tunanin rubuta wannan littafin. Littafin ya mayar da hankali kan bincike tare da nazarin al’adun zamantakewar aure daga cikin rumbun Karin maganar Hausa. Littafin ya samu jagorancin bayanan da aka kalato daga masana da marubuta da manazarta da magabata a wurare daban-daban.
Littafin ya mayar da hankali kan nazartan tarin karin maganar Hausa waÉ—anda suke Æ™unshe da al’adu da yanayin zamantakewar aure da sauran lamura da suka danganci rayuwar iyali. Ta haka, an yi Æ™oÆ™arin fitar da hoton al’adun zamantakewar aure tare da bayyana su dalla-dalla, bisa tsarin mataki-mataki. An yi haka ne daidai da ire-iren saÆ™onni daban-daban da suke Æ™unshe cikin falsafa a Æ™unshiyar karin magana.
An raba littafin zuwa babuka guda shida. Babi na farko ya yi magana game da gurabun aure da karin magana a rayuwar Hausawa. Ya tabbata cewa, aure É—aya ne daga cikin muhimman matakan rayuwar al’ummar Hausawa. A É“angare É—aya kuwa, karin magana ya kasance tamkar gishirin zance ga Hausawa, sannan wani muhimmin É“angare na adabinsu.
Babi na biyu ya kawo hoton aure da jinsin ma’aurata a cikin karin magana. Wato ya duba yadda karin magana na Hausa suke Æ™unshe da saÆ™onnin da suka shafi aure. Haka kuma, an nazarci waÉ—anda suka shafi jinsin ma’aurata, wato maza da mata. Daga ciki har da waÉ—anda suke magana game da halayen maza da mata a zamantakewar aure.
Babi na uku, ya mayar da hankali kan taurarin gidan aure a mahangar karin magana. Taurarin gidan aure su ne rukunonin mutane daban-daban da ake samu a gidan aure, ko waÉ—anda suke da alaÆ™a da aure. Sun haÉ—a da ango da amarya da surukai da agola da ‘yar riÆ™o da ‘yar zaman É—aki da sauransu, waÉ—anda duk sun shafi mutanen da suke zama a gidan aure. A É“angare É—aya kuwa, akwai waÉ—anda sunayensu sun samu ne ta hanyar danganta su da aure, duk da ba a gidan auren suke ba. Misalansu sun haÉ—a da gwauro da tuzuru da ake sanya musu sunayen sakamakon rashin yin aure.
Babi na huÉ—u kuwa ya karkata kan hoton zamantakewar aure a cikin karin magana. Ya yi duba zuwa ga yadda zamantakewar aure take kasancewa. Ya haÉ—a da halayen maza da mata a gidan aure da kuma hoton kyawawa da munanan halayya da ake nunawa a gidan aure.
Babi na biyar ya shafi nazarin wasu muhimman batutuwa da suke da alaÆ™a da aure. Sun haÉ—a da kishi, wanda ya rabu zuwa fuskokin da suka haÉ—a da kishi tsakanin kishiyoyi da kishi da uwar miji da kishi da ‘ya’yan kishiya da makamantansu. Sauran muhimman batutuwa masu alaÆ™a da zaman aure sun haÉ—a da maraici da zawarci da sauran makamantansu. An duba hotonsu daga cikin taskar karin magana.
Babi na shida shi ne na ƙarshe. Ya nazarci hoton saɓani da sulhu a cikin karin magana. Kasancewar harshe da haƙori ma sukan saɓa, a har kullum ba a rasa ɗan bambancin fahimta ko ƙaramin saɓani da yake bijirowa a cikin zamantakewar aure. Wasu lokutan, akan samu manyan matsalolin saɓani da har sai iyaye da waliyai sun saka baki, wani lokaci ma har a dangana da kotu. Daga taskar karin magana, an duba yadda sulhu yake cin tura a wasu lokutan. Haka kuma, an nazarci wasu kare-karen magana da suka shafi lumana da ƙanƙan da kai a cikin zamantakewa.
