Game Da Rayuwa

  Abu-Ubaida Sani
  Abu ne mai matuƙar kyau na sama ya lura da buƙatu da muradun zucin waɗanda ke ƙasa da shi. Ya ba shi damar fitar da waɗannan muradu ta hanyar sake masa fuska da ba shi damar bayyana tunani da ra’ayoyinsa. Wannan zai taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwar yara da bunƙasar kaifin basirarsu. (Sani, A-U. 2023)


  Abu-Ubaida Sani
  Wata hanyar gane muradu da buƙatun zuci na yara ita ce lura da alamomi da za su iya nunawa yayin da kawaici da kunya da sauran tanade-tanaden al’ada suka dabaibaiye ƙwarin guiwarsu. (Sani, A-U. 2023)


  Abu-Ubaida Sani
  Tauye tunani da muradun matasa ba tare da bayyana musu dalilin hakan da kuma yi musu ishara da mafifin zaɓi ba, na iya haifar musu da daƙushewar kaifin tunani da sallama rayuwa da fafutukan samun nagartaccen gobe da kuma sakankancewar da ka iya kaiwa ga wofantar zuciya. (Sani, A-U. 2023)


  Abu-Ubaida Sani
  Tara dukiyar da rayuwa da mutuwa ba za su amfana da ita ba, abu ne mai wahalar bayani a matsayin hankali ko hauka! (Sani, A-U. 2023)


  Abu-Ubaida Sani
  Abu mafi burgewa a duniya bai dogara kan halin farin ciki da walwala da kake ciki ba, ya fi dogara kan adadin mutane da sauran halittu da ke samun farin ciki da sauƙin rayuwa dominka - ballantana a lahira! (Sani, A-U. 2023)

  Pages