Siddabarun Zamani: Daga Kimiyya da Fasaha Zuwa Dabarbarun Daburta Tunanin Bami

    Citation: Sani, A-U. & Jaja, M. B. (2020). Siddabarun Zamani: Daga Kimiyya da Fasaha Zuwa Dabarbarun Daburta Tunanin Bami. In Al-Nebras International Journal 4th Edition, Vol. 2. Pp 28-41. ISSN Online: 2705-1501, ISSN: Print: 9876-5432.

    Siddabarun Zamani: Daga Kimiyya da Fasaha Zuwa Dabarbarun Daburta Tunanin Bami

    Abu-Ubaida SANI1
    Department of Languages and Cultures
    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
    Mail: abuubaidasani5@gmail.com
    Phone: +2348133529736

    And

    Muhamamad Bala JAJA2

    Department of Nigerian Languages and Linguistics

    Kaduna State University, Kaduna

    Tsakure

    Wannan ɗan bincike ya mayar da hankali ne kan nazartar tasirin zamani kan ayyukan siddabarun Bahaushe, musamman siddabarun ‘yan damfarara. Ya waiwaici sha’anin siddabarun Bahaushe a da, daga nan sai ya karkata zuwa ga nazarin tasirin zamani musamman kimiyya da fasaha a kan ayyukan na siddabaru. Waiwaitar yadda siddabaru ya kasance a da, ya bayar da hasken kaiwa ga nazarin yadda siddabaru yake kasancewa a yau. An ɗora aikin kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Karen bana shi ke maganin zomon bana.” An bi hanyoyi da dabarun gudanar da bincike da suka haɗa da hira da kuma kallace-kallacen bidiyoyin da suke ɗauke da siddabarun zamani da aka gabatar a tarurruka daban-daban. An kuma nazarci waɗansu fitattun rubuce-rubuce da aka gabatar kan siddabarun zamani. Binciken ya fahimci cewa, a yau al’ummar Hausawa ta waye ta yadda ba za a iya bin tsofaffin hanyoyin damfara a damfare ta ba. A ɓangare guda kuma, ana amfani da siddabarun zamani musamman ta taimakon kimiyya da fasaha wajen aiwatar da siddabaru da damfara a zamanance. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwarin cewa ya kamata a sanya kwas da ke magana game da siddabaru da damfara a jami’o’i domin wayar da kan al’umma don tsallake wa tarkon yaudara. A ɓangare guda kuma, tararrukan ƙara wa juna sani za su taka irin tasu muhimmiyar rawar wajen wayar da kan al’umma da fargar da su.

    1.0 Gabatarwa

    Ɗaya daga cikin siffofin al’ada shi ne sauyawa. Ayyukan siddabaru na daga cikin al’adun da al’ummomin duniya ke shan faman karo da su a harkokin rayuwarsu, cikin waɗannan al’ummu kuwa har da Hausawa. A matsayinsa na wani ɓangare na al’ada, siddabaru na samun sauye-sauye ta fuskoki daban-daban. Hakan kuwa dole ne ya ja hankalin ɗalibai da manazarta da masana al’ada. Shin ‘yan siddabaru na gargajiya ne ke taka rawar kiɗan zamani wajen zamanantar da harkokinsu na siddabaru? Ko dai wasu ne daban da suka ƙoshi da zamani ke shiga harka a matsayin haye? Ko ma dai yaya abin yake, tabbataccen al’amari ne cewa, ‘yan siddabaru sun kasance masu ɗimbin hikima da fasaha. Ko banza dai tsantsar hikima suke amfani da ita wajen daburta tunanin bami.

    Abubakar, (2007:23) ya rawaito cewa, tun wajejen 1995 shugaban kamfanin Microsoft’ Bill Gates ya yi hasashen wani mataki da za a riska na dunƙulewar duniya, ta yadda kowa zai iya sarafa bayanai da ilimin da ya shafi fannonin rayuwa daban-daban cikin sauƙi, kuma cikin taƙaitaccen lokaci. Ya yi wannan bayani ne cikin littafinsa mai suna The Road Ahead. Haƙiƙa wannan ya shafi ɓngarorin rayuwa gaba ɗaya. Daga ciki kuwa har da lamuran siddabaru da sihiri. Ana samun siddabaru da sihiri ne a zamantakewa da hulɗatayyar rayuwa ta yau da kullum. Wannan na nuna cewa, yayin da aka samu tsarin game duniya, su ma sha’anonin na siddabaru da sihiri za su sauya zane.

    Wannan takarda za ta mayar da hankali wurin binciko ire-iren sauye-sauyen da aka samu a duniyar siddabarun Bahaushe. A ciki ne za a duba ko zamani (musamman abin da ya shafi kimiyya da fasaha) ya yi tasiri a harkokin Hausawa na siddabaru? Baya ga haka, za a dubi yadda siddabaru ya kasance a duniyar yau. Kai-tsaye, za a nazarci wasu nau’o’in siddabarun da aka gudanar a manyan taruka musamman tarukan nuna baiwa na Amurka da na Biritish da na Larabawa da kuma na ‘yan Cana (wato,American Got Talent da British Got Talent da Arab Got Talent da kuma Chinese Got Talent). A ire-iren waɗannan taruka, ana amfani da kimiyya da fasaha tare da zunzurutun dabaru irin na zamani yayin gudanar da ayyukan siddabarun.

    1.1 Manufar Bincike

    Wannan bincike na da ƙudurin nazartar sauye-sauyen da zamani ya kawo a duniyar siddabaru. Kai tsaye zai mayar da hankali kan:

    i.                    Waiwaitar siddabarun Bahaushe a da.

    ii.                  Nazartar tasirin kimiyya da fasaha cikin ayyukan siddabaru.

    iii.                Nazartar siddabarun Bahaushe a zamanin yau.

    1.2 Ra’in Bincike

    Wayo da dabara su suka mamaye duniyar siddabaru da damfara., su ne kuma ke jagorancin tafiyar. A ɓangare guda kuma, Bahaushe ya yi zarra a fagen wayo da hikima a duk duniyar baƙar fata (Bunza, 2019).[1] A bisa waɗannan dalilai, za a iya hasashen cewa, siddabaru ba fararriyar al’ada ba ce ga Bahaushe. Al’ada ce gadajjiya wanda binciken tarihinta zai kai ga binciken tarihin asalin Bahaushe na gaba ɗaya. Lura da haka, za a iya samun tunanin Bahaushe da ke wakiltar lamuransa na siddabaru da damfara. Wato ba sai an je kale daga wasu ɓangarorin ilimi na daban ba.

    An ɗora wannan bincike bisa karin maganar Bahaushe da ke cewa: “Karen bana shi ke maganin zomon bana!” Bincike ya nuna cewa, mafi yawan waɗanda ake damfara ta hanyar siddabaru sun kasance masu ɗauke da ɗaya ko fiye na daga cikin halayen da ke ƙasa:

    i.                    Kwaɗayi.

    ii.                  Son banza.

    iii.                Son abin duniya fiye da kima.

    Ire-iren waɗannan ɗabi’u nasu ke ba wa ‘yan damfara damar rufe musu idanu ta hanyar ayyukan siddabaru da ke nuna cewa za su samu babbar riba. A duk lokacin da al’umma suka gane salailan siddabarun da ake amfani da su a damfare su, su kuwa masu yin siddabarun kan tanadi wasu sababbin dabarun da za su tafi da hankalin al’umma. Ke nan dai, karen bana sai ya yi maganin zomon bana kafin ya kuɓuta daga irin tanade-tanaden da ake masa. Amfani da abubuwan da zamani ya zo da su musamman na kimiyya da fasaha ya ba wa ‘yan siddabaru damar fito da sababbin hanyoyin damfarar ‘ya’yan zamanin.

    1.3 Dabarun Bincike

    Hausawa sun ce: “Ta wurin da fata ta fi taushi ta nan akan mayar da gaban jima.” Domin samun nagartaccen bincike, an bi manyan hanyoyi guda biyu a lokacin da ake tattara bayanan wannan bincike. Hanya ta farko ita ce, tattaunawa (hira). An tattauna da masana al’adun Hausawa, musamman abin da ya shafi siddabaru da dangoginsa. Bayan nan kuma, an tattauna da wasu daga cikin waɗanda ke da kusanci da ilimin gani-da-ido kan lamuran siddabaru. An tattara bayanan da suka bayar tare da nazartar su bakin gwargwado.

    Hanya ta biyu da aka yi amfani da ita kuwa ta shafi binciken intanet(internet research/surfing). An duba bidiyoyin siddabaru daban-daban waɗanda aka gudanar a manyan tarurrukan da aka gabatar a ƙasashe daban-daban. Daga cikinsu akwai:

    i.                    Bidiyoyin da ke ɗauke da siddabaru, waɗanda aka yi amfani da kimiyya da fasaha wajen shirya su.

    ii.                  Bidiyoyin da ke ɗauke da sirrin yadda aka gudanar da wasu fitattun siddabaru a manyan tarurrukan duniya.

    iii.                Bidiyoyin da ke koyar da yadda ake amfani da kimiyya da fasaha domin aiwatar da siddabaru.

    iv.                An kuma karanta littattafai da muƙalu da ke ɗauke da sirrikan yadda ake gudanar da wasu nau’ukan siddabaru, musamman na zamani.[2]

    Domin layar binciken ta sami kyakkyawan rufi, da aka kammala nazarin ire-iren waɗannan bidiyoyi, an tattara bayanan da aka tsinto a cikin su tare da tsara su cikin aikin. Waɗannan hanyoyin da aka yi amfani da su a matsayin dabarun bincike, sun taimaka matuƙa wajen fito da sigogi da salailan siddabarun zamani tarwai tamkar tsaba a kan faifai.

    2.0 Siddabaru a Duniyar Bahaushe ta Jiya da ta Yau

    Dabara na nufin amfani da wayo da hikima da azanci. Jam’in dabara shi ne “dabaru.” Yayin da ka samu dabaru da yawa kuwa, musamman cikin salon da ka iya daburta tunanin mai kallo ko mai sauraro, sai masana suka kira shi da “siddabaru.” Bunza (2011:2-3)

    2.1 Bahaushen Siddabaru a Da

    A ra’ayin wannan bincike, tarihin samuwar siddabaru tsakanin Hausawa daɗɗe ne, daɗewarsa da ta kai na tarihin Hausawan kansu. Dalili kuwa, daɗaɗɗen tarihin Bahaushe cike ya ke da misalan yadda ya shahara a fagen yin amfani da dabaru a abin da ya shafi al’amuran rayuwarsa daban-daban. Ana iya tsintar tsattsafin misalan waɗannan dabarbaru nasa cikin:

    i.                    Tatsuniyoyinsa.

    ii.                  Wasanninsa na gargajiya.

    iii.                Almararsa.

    iv.                Rubuce-rubucen zubensa.

    v.                  Waƙoƙinsa na gargajiya.

    vi.                Hikayoyinsa.

    vii.              Tarihin gwagwarmayar Hausawa.

    2.1.1 Siddabaru a Tatsuniyoyin Bahaushe

    A tatsuniyar zomo da kura da ‘ya’yanta, an ga tarin dabarbarun da zomo ya yi amfani da su. Tun lokacin da ya lura da kura daga bakin kogo take miƙa wa ‘ya’yanta abinci, a nan ya ɗana tarkon yi mata dabo ta hanyar siddabaru.[3] Dabarar farko da ya yi shi ne, ya isa wurin ‘ya’yan na kura a matsayin baƙo. Haka kuma, ya ce ai sunansa “Ku Duka!”[4] Zomo ya yi siddabaru na biyu yayin da ‘ya’yan kura ke fitowa daga kogon. Lokacin da ya tabbatar da asiri ya tonu, sai ya haɗe kunnuwansa biyu ya rufe fuskarsa, sannan ya ce da kura: “Riƙe mini takalmana kafin in fito.” Kura kuwa da ke hasale ta kama kunnuwan zomo ta yi wurgi da shi can gefe (a tunaninta takalma ne). Zomo ya tashi ya arce.[5] A wata tatsuniyar makamanciyar wannan, kura ta yi amfani da ɗan botoromi guda ɗaya inda ta gabatar da shi a matsayin guda goma sha tara. Wannan kuwa ba tsafi ba ne, illa tsantsan dabaru, wato dai siddabaru.[6]

    2.1.2 Siddabaru a Wasannin Gargajiya

    Wasa dai na nufin duk wata magana da aka furta ko wani aiki da aka aikata da nufin raha da nishaɗi. Yayin da aka ce wasannin gargajiya kuwa, ana nufin wasannin Hausawa da suka kasance sanannu. Daga cikinsu akwai waɗanda suke da takamaiman wuri da lokacin aiwatarwa, wasu kuma har da sanannun kayan wasa da ake amfani da su yayin gudanar da wasannin.

    A ɓangaren wasannin gargajiya, misalan siddabaru sun fi shurin masaƙi yawa. Akwai siddabaru da ya shafi yadda ake gudanar da wasannin kansu, akwai kuma waɗanda suka shafi waƙoƙin cikin wasannin. Za a tsinci irin wannan misalai na siddabaru yayin da aka nazarci wasan “Allah Raini.”[7]Wasan a karan kansyana da salo da siga na siddabaru. Dalili kuwa shi ne, ta shafi zurfafa tunani da amfani da dabaru domin gano inda wani ya ɓuya (alhali kuwa idanuwan wanda zai yi wannan hasashe a rufe suke). Bayan nan, wasan ya shafi fayyace wanda ya tsallake Allah raini, alhali idanunsa na rufe. Haƙiƙa, kai tsaye za a iya kallon wannan a matsayin siddabaru.

    Akan samu matakin siddabaru na gaba a cikin wannan wasa na Allah Raini yayin da aka yi amfani da ɗankore. Allah raini zai haɗa baki da wanda zai rufe masa idanuwa. Za su tanada wasu alamu na musamman da ke wakiltan dukkanin yaran da ke wasar. Misali (1):

    1.      Idan na taɓa kunnenka na dama, to Audu ne ya tsallaka ka.

    2.      Idan na taba kunnenka na hagu, to Musa ne ya tsallaka ka.

    3.      Idan na taba ƙeyarka, to Balarabe ne ya tsallaka ka.

    Yayin da aka yi wannan shiri, sai a tarar da cewa, nan da nan Allah raini zai gane duk wanda ya tsallaka shi. Bayan haka ma, Allah raini na amfani da ɗaya ko fiye daga cikin ‘yan wasan a matsayin ‘yan kore. Misali (2):

    “Ni Ɗanjummai zan tabbatar da cewa na tsaya a gaban Ciwake. Yayin da na zo tsallaka ka, to zan taɓa guiwarka da ƙafata. Mutumin da ke bi mini, zai kasance Ciwake, saboda haka sai ka ambaci sunansa.”

    Wani wasan kuma da ake samun siddabaru shi ne “ wasan’yar Ɓoyel.”[8] Shi ma wannan wasan zubi da tsarinsa akwai hoton siddabaru a ciki. Dalili kuwa shi ne, ya shafi ɓoye abu cikin hikima, tare kuma da yin amfani da hikima wurin gano abin da aka ɓoye ɗin. Bayan wannan, ɗaya daga cikin ‘yanwasan na iya shirya zamba a ransa. Yadda ake hakan kuwa shi ne, mai tafiyar[9] zai ƙi sanya ’yarsa[10] a kowanne daga cikin tsubi-tsubin ƙasar. A maimakon haka, zai shammaci sauran ‘yan wasan ya ɓoye ‘yar tasa a wani wuri. Yayin da abokan wasansa suka nuna tsibin ƙasar da suke tsammanin ‘yar ta ke, sai a ce ba nan ba ne. Idan sun duba kuwa za su tarar da lallai ba ta ciki. Shi kuma zai nuna musu ɗaya daga cikin sauran tsibi-tsibin ƙasar a matsayin nan ne ‘yar ta ke. A wannan lokacin ne kuma zai sake shammatansu ya sanya ‘yar a ciki. Da zarar an duba, sai a tarar da ita.

    2.1.3 Almara

    A cikin almarar Bahaushe ma akan tsinci misalan siddabaru, musamman waɗanda suka shafi lissafi. Daga cikin fitattun almarar Bahaushe da ke ɗauke da misalan siddabaru akwai:

    1.      Almarar tsallake kogi tare da kura da akuya da dawa/ciyawa.[11]

    2.      Almarar tafiya da raƙuma huɗu a jere, waɗanda ɗaya na cin naman raƙumi, ɗaya na cin naman mutum, ɗaya na cin kanwar bayan raƙumi, ɗayan kuma lafiyarsa ƙalau.[12]

    3.      Tsallakar da mayu uku tare da ‘ya’yansu ruwa.[13]

    Dukkanin waɗannan almarorin wasa ƙwaƙwalwa (da ma wasu makamantansu), an yi amfani da dabarbaru na musamman yayin gina su. An samar da wani rikitaccen al’amari mai buƙatar zurfafa nazari wajen warware shi. Da ma dai, ɗaya daga cikin ɗabi’un ɗan siddabaru shi ne “tsananin wayo.”

    2.1.4 Hoton Siddabarun Bahaushe a Rubutun Zubensa

    Rubutun zuben Bahaushe wani babban fage ne da ke tabbatar da cewa ya daɗe yana aiwatar da ayyukan siddabaru. Imam, (1998: 66-74) ya kawo hoton siddabaru ƙarara a littafin Magana Jarice 2. A cikin labarin “Jarabawar da aka yi wa Sarkin Ɓarayi Nomau,” ya nuna wasu matakan siddabaru da Sarkin Ɓarayi Nomau ya gabatar. Nomau ya nuna bajintar siddabaru yayin gudanar ƙasaitattun nau’o’in sata guda uku da aka sanya masa a matsayin gasa. Waɗanda suka ƙunshi satar zobe da ta bargon sarki, da kuma satar limamin gari sukutum.[14]

    A littafin Ruwan Bagaja, an ga yadda Imam, (1999: 22) ya bayyana siddabarun da Abubakar ya gabatar a garin Tegi. Ta hanyar siddabarun ne ya yi maganin Sarkin Zagi da ya kasance yana damun sarkin garin Tegi kullum da dare. Ya yi dabarar shigewa ɗakinsa ba tare da ya ankara ba. Sannan ya bayyana gare shi a matsayin mutuwa. Kasancewar Sarkin Zagi bai tsammaci ganin wani mahaluƙi ba a wannan lokaci ya sa ya damfaru da cewar mutuwar ce da gaske.

    2.2 Ko Siddabarun Bahaushe Ya Sanya Rigar Zamani?

    Kamar yadda yake a tunanin Bahaushe cewa: “karen bana shi ke maganin zomon bana,” da alama wannan zomo na da saurin sauya salailan rayuwa. Hakan na nuna cewa, dole wannan kare ya farga tare da taka rawar kiɗan zamani in har yana son tsira. Ba abin mamaki ba ne yadda ta kasance ‘yan siddabaru ke amfani da abubuwan da zamani ya zo da shi, domin gudanar da ayyukansu na siddabaru.[15]Da zarar wani sabon al’amari ya faru, ko wani sabon ci gaban zamani ya samu, sukan yi saurin amfani da wannan dama a matsayin hanyar damfara.[16] Kafin al’umma su farga, har an ci kasuwa an watse. Ko da an gano wannan hanya daga baya, sai ya zamana cewa an yi abin nan ne da Hausawa ke cewa: “Ko yanzu kasuwa ta watse, Ɗankoli ya ci riba.”

    Bunza, (2019)[17] ya bayyana cewa, hanyar nuna jariri a cikin kwali (ko wani abu mai kama da wannan) da ‘yan damfara suke yi a da tsantsar siddabaru ce ba tsafi ba. A wancan lokaci, kan mutane bai waye da ‘yar bebin roba ba. ‘Yan siddabarun na samo bebin roba (‘yar tsana) su sanya cikin akwati ko kwali/bandiri (ko wani abu mai kama da wannan). Za su nemi wani ya leƙa ciki. Da zarar ya leƙa, sai ya tarar da ‘yar bebin nan. Nan kuwa zai razana. A tunaninsa, jinjirin gaske ne.

    Da tafiya ta yi tafiya, musamman lokacin da aka fara samun bunƙasar kimiyya da fasaha, sai ayyukan siddabaru da damfara suka ɗauki sabon salo. Masu amfani da siddabaru domin gudanar da ayyukan damfara sai suka sauya taku. Sun sanya rigar zamani game da ayyukansu na siddabaru da damfara. Wani babban abin lura amma shi ne, mafi yawan siddabaru da damfara da ake aiwatarwa ta hanyar amfani da kayayyakin zamani, to baƙi ne ga Bahaushe. Ya koye su ne daga baƙin al’ummu na kusa da na nesa.

    2.2.1 Waya (Kiraye-Kiraye Da Saƙonnin Kar-ta-kwana )

    A nan, na zaɓi na yi wa wannan fasalin fashin goro, wato fito da irin yadda masu siddabaru ke amfani da wayar salula ta hanyoyi mabambanta domin cimma muguwar manufarsu.Samuwar waya ya buɗe wani sabon babi a duniyar siddabaru da damfara. Manyan hanyoyin da damfarar waya ta ƙunsa su ne (i) kira, da (ii) saƙon kar-ta-kwana. Misali (3):

    1.      Ana kiran mutum ta waya da sunan iskoki ne suka kira shi. Za a riƙa faɗa masa abubuwa game da tarihinsa da mu’amalarsa da wuraren hulɗatayyarsa da sauransu. Wannan zai ba shi mamaki matuƙa, a rashin sanin cewa da ma an riga an karance shi sosai kafin a fara harƙallar. Wani lokaci kuwa “da ɗan gari akan ci gari.” Yayin da aka samu bami ko kwaɗayayye, sai “a ci wawa a tashi.”

    2.      Ana iya kiran mutum da sunan cewa wani ɗan uwansa ya yi haɗari ko ya shiga cikin wani mawuyacin hali. A irin wannan yanayi, za a nuna cewa ana buƙatar wani abu na gaggawa kamar kuɗi ko wasu bayanai. Wanda bai yi farga ba, sai a yi farga da shi.

    3.      Akan turo wa mutum saƙo da sunan cewa daga wata ma’aikata ce, ko wani muhimmin wuri. Za a buƙaci ya tura wasu bayanai masu muhimmanci kamar waɗanda suka shafi bayanan bankinsa da makamantansu. A irin haka ne za a damfari wanda bai mayar da hankali ba.

    2.2.2 Intanet

    Kafar intanet da ake ce wa “yanar gizo” ta kasance tamkar wata duniya ce mai zaman kanta. A kan intanet akwai tarin bayanan da suka wuce sau shurin masaƙi. Akwai kuma kafafen sada zumunta iri-iri, kai ka ce garuruwa ne. Siddabaru da damfara a duniyar intanet sun shafi manyan ɓangarori guda biyu wato (i) kafafen intanet, da (ii) kafafen sada zumunta.

    2.2.2.1 Kafafen Intanet

    Tsangarwa, (2006:85) ya ba da ma’anar intanet da cewa:“Fasahar sadarwa ce da ta haɗa kwamfutoci a duniyance, kuma take ba su damar musayar bayanai a tsakaninsu.” Akan samar da kafafen intanet na yaudara. Ana musu tsari na musamman da za a iya amfani da su domin satar bayanan duk wanda ya yi amfani da kafar. A shekarar 2012 an samu yawaitar wannan nau’in yaudara a tsakanin Hausawa. A lokacin kafar sada zumunta ta 2go na tashe. Ana yaudarar mutane da cewa za su samu kyautar kuɗi ko wani abu da ake kira gocredit, wanda da shi ne ake iya samun damar tura saƙonni a “ɗakuna” (rooms).[18]

    A yanzu haka, a kullum sai an samu adadi mai yawa daga cikin Hausawa waɗanda aka tura musu saƙonni ta imel ko wata kafa ta intanet. Saƙon na iya kasancewa:

    1.      Ana iya ba da wani liƙau (link) da zai kai mutun zuwa wata kafar intanet ta daban. A can za a bukaci ya sanya wasu bayanai domin ya samu wani alfanu kamar kuɗi ko kwamfuta da sauransu. Bayanan da ake nema na iya shafar na bankinsa ko lambobin sirrin imel ɗinsa, da dai makamantansu. Daga nan ne kuma za a yi amfani da waɗannan bayanai nasa wajen aikata masa ta’asa.

    2.      Ana turo saƙonni a matsayin ana neman a haɗa wata harƙallar kasuwanci da wanda aka tura wa saƙon. A nan, za a nuna masa cewa, kasuwanci ne da za a samu riba sosai. A wurin kwaɗayi, sai ƙuda ya mutu.

    3.      Saƙon kuma na iya kasancewa na harƙallar kuɗi kai tsaye. Misali, mai turo saƙon na iya nuna cewa, shi mazaunin ƙasar waje ne. Yana son zuwa ƙasar da wanda aka turo wa saƙon yake. A dalilin haka, yana son lambar asusun banki da zai turo wasu kuɗinsa masu yawa. Daga tunanin cin banza, sai banza ta sha mutum.

    2.2.2.2 Kafafen Sada Zumunta

    Wani babban abin da intanet ta zo da shi, shi ne kafafen sada zumunta. A yau akwai kafafen sada zumunta na intanet sama da ɗari uku. A kullum kuwa suna ƙara yawa ne. Fitattu daga cikin kafafen sada zumuntar da Bahaushe ke amfani da su, sun haɗa da:

            i.            Facebook.

          ii.            Instagram.

        iii.            Lindin.

        iv.            Twitter.

          v.            Whatsapp.

    Kafafen na da muhimmanci matuƙa. Daga cikin amfaninsu akwai:

    1.      Suna taimakawa wajen sada zumunci cikin sauƙi.

    2.      Suna taimakawa wajen ɗebe kewa.

    3.      Suna taimakawa wajen samun rubuce-rubucen ilimi.

    4.      Suna taimakawa wajen samun labaran abubuwan da ke faruwa yau-da-kullum.

    5.      Suna taimakawa wajen haɗa abota da soyayya.

    6.      Suna taimakawa wajen rage yawon banza.

    Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Kowane allazi da nasa amanu.” Ɗaya daga cikin manyan matsalolin waɗannan kafafen sada zumunta shi ne harkokin siddabaru da ke kai wa ga damfara.Kamar yadda ra’in binciken ya ke (Karen bana shi ke maganin zomon bana), mafiya rinjayen masu amfani da kafafen sada zumunta ‘yan zamani ne. ‘Yan siddabaru da damfara na samun damar amfani da wannan kafa kasancewar:

    a.       Talauci ya yi yawa a tsakanin samari Hausawa. Kodayake da man babban makamin damfara shi ne lasa wa mutum zuma a baki.

    b.      Son banza na ƙara yawaita tsakanin matasa. Wannan ya shafi samari da ‘yammata. ‘Yan mata da ke da kwaɗayin abin duniya, an sha samun lokutan da aka lalata musu rayuwa ta hanyar yaudarar su ta kafar sada zumunta. Jaridar Hausa Legit ta rawaito labarin wata budurwa da aka damfara aka ɓata wa lokaci a kafar sada zumunta ta Facebook. Ta yi soyayya ta tsawon lokaci inda sai har ta niƙi gari ta tafi garin wanda suke tarayya ta kafar sada zumunta, sai ta tarar da cewa ɗan shekara 12 ne. Jaridar ta ce:

    Budurwar ta bayyana cewa bayan zuwanta jihar Enugun ta gano cewa ashe da yaro ɗan shekara 12 take magana duk wannan lokacin. Usman, (2019: 1).

     

    c.       Kwaɗayin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare ya yi yawa a zuciyar matasa. Miyagu kuwa suna amfani da wannan dama wajen damfarar matasan ta kafafen sada zumunta. Shafin gwamnatin Kanada ya wallafa jan kunne ga al’umma game da wannan nau’in damfara. Ya yi wallafar ranar 19/12/2018. A ciki an lissafo nau’ukan ƙarairayi daban-daban da ‘yan damfara ke amfani da su ta kafafen sada zumunta domin damfarar al’umma.[19]

    d.      A kafafen sada zumunta, akan samu sauƙin yaɗa bayanai. Sannu a hankali har ya kai ga wanda zai faɗa tarkon ‘yan damfara. Kusan a kullum mutum ya buɗe kafafen sada zumunta, sai ya ci karo da ire-iren tarkunan da ‘yan damfara ke ɗanawa. Sun baza homa suna jiran makararren kifin da tsautsayi zai ritsa da shi. A ƙasa an kawo misalan wasu daga cikin tarkunan ‘yan damfara da aka ɗauko daga kafar sada zumunta ta Whatsapp:

    Hoto 1: Hoton da aka ɗauko daga Whatsapp wanda ke ɗauke da tarkon ‘yan damfara. Sun nuna cewa, yayin da mutum ya sanya wani adadin kuɗi, to zai samu ninkinsu.

    2.3 Kamanceceniyar Siddabaru Da Damfarar Bahaushe Jiya Da Yau

    Duk da cewa akwai bambance-bambance tsakanin ‘yan siddabarun gargajiya da na zamani, musamman masu amfani da siddabaru domin damfara, akwai kamanceceniya sosai a tsakaninsu. A ƙasa an zayyano wasu daga cikin waɗannan ɓangarori da suka yi tarayya:

    1.      Dukkaninsu na da manufa guda ne, wato damfare tunanin mutum ko mutane domin su samu abin da suke buƙata daga gare su.

    2.      Dukkaninsu na amfani da ‘yan kore. Da ma dai akwai nau’o’in kore da ‘yan kore daban-daban.

    3.      Dukaninsu na amfani da kayan aiki. Wannan ya shafi sutura da jaka da makamantansu.

    4.      Dukansu na bin matakan nazartar halayyen al’umma musamman domin sanin ɓangarorin da suke da rauni. Hakan ne zai ba su damar ɓullo musu ta fuskokin da ba su tsammata ba.

    2.4 Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Siddabaru da Damfarar Bahaushe ta Jiya da ta Yau

    Jad 1: Bammbacin da ke tsakanin Siddabarun Bahaushe Jiya da Yau ta Fuskar ‘Yan Siddabarun

     

    ‘Yan Damfarar Gargajiya

    ‘Yan Damfarar Zamani

    1.       

    Yawanci masu ilimin addini ne. An fi samun gardawa cikin harkokin siddabaru.

    Yawanci masu ilimin boko ne da kuma ilimin sarrafa kwamfuta.

    2.       

    Damfarar gargajiya ta fi faruwa gaba-da-gaba. Wato dole ɗan damfara ko ‘yan korensa su haɗu da wanda za a damfara.

    Hanyoyin siddabaru da damfarar zamani na ba da damar a damfari mutum ba tare da an haɗu gaba-da-gaba ba.

    3.       

    Yawanci baƙi ne ke damfarar gargajiya. Suna da salon “A ci wawa a tashi.”

    Wanda ake tare da shi ma na iya bin hanyoyin damfarar zamani domin aiwatar da damfara, dalili kuwa shi ne, ba dole ne a gan shi ba.

    4.       

    Suna amfani da kore da ‘yan kore na gargajiya, kamar mutane da dabbobi da tsuntsaye da sauransu.

    Suna amfani da nau’ukan kore da ‘yan kore na zamani kamar kwamfutoci da sinadarai da injuna.

    5.       

    Suna amfani da nau’o’in kayan aiki irin na gargajiya.

    Suna amfani da nau’o’in kayan aiki irin na zamani, yawanci waɗanda suka shafi kimiyya da fasaha.

     

    Jad 2: Bambance-bambance tsakanin Siddabarun Bahaushe Jiya da Yau ta Fuskar Ayyukan Siddabarun:

     

    ‘Yan Siddabarun Gargajiya

    ‘Yan Siddabarun Zamani

    1.       

    Dole sai an yi gaba-da-gaba da mutumin ko mutanen da za a yi wa siddabaru.

    Ana iya aikata siddabaru har a damfari mutum ba tare da an yi gaba-da-gaba da shi ba.

    2.       

    ‘Yan kore sun haɗa da mutane da abubuwa da ana iya kallonsu kuma a taɓa su.

    ‘Yan kore sun fi shafar bayanai a kafafen sadarwa ko na’urori.

    3.       

    Galiban suna aiwatar da siddabarun da wasu wasannin motsa jiki, saboda garin-da-garin da aka yi da waɗanda ake so a damfara.

    Babu wani wasannin motsa jiki da ake aiwatarwa, saboda ba a tare ake da wanda ake so a damfara ba.

    4.       

    Lissafo wasu ƙasashe da aka je tallar magani, da nufin nuna wa bami ba iya garinsu aka tsaya ba.

    Akan yi ƙoƙarin Lissafo wasu ƙasashe da irin hanyoyin da suka yi amfani da su wajen harkokin zuba jari, da nufin kama hankalin mai son banza.

    5.       

    Akwai salon jejjera magunguna tare da sanya layu da guraye (kurhuna) a jiki da nufin tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.

    Ba a maganar magani irin na ganyaye da saboda ba da su aka aje jigon damfarar ba. Sai dai ƙaryar nuna wayewa da nuna ilimin boko da sanin ilimin kwamfuta da kuma yanar gizo.

    6.       

    Bayar da kyautar magani musamman ga wanda ya nuna ya taɓa amfani da maganin (ɗankore) na daga cikin ɗabi’unsu.

    Kasancewar ba a tare ake ido da ido da ɗan koren ba, babu batun bayar da kyautar abin da ake bayarwa.

    7.       

    An fi aiwatar da shi a kasuwanni da dandali da kuma wurin da ake shagalin wasu bukuwa.

    Ana aiwatar da shi ne a shafukan sada zumunta da sauran kafafen yanar gizo.

     

    3.0 Siddabaru A Duniyar Kimiyya Da Fasaha

    Sakamakon irin sauyawar da zamani ya yi, sai masu siddabaru suka ɗauki wani sabon salo domin su cigaba da damfarar al’umma. Kasancewar duniyar yau tana tafiya da ilimin kwamfuta tare da yanar gizo, sai suka koma suka tsirawa waɗannan hikimomi da ilmomi ido tare da nazartar yadda ake amfani da su. Wannan sai ya ba su damar kutsawa cikin ayyukan wasu ma’aikatun da ke da harkokin kuɗaɗe tare da ɗaukar salailan da suke amfani da su wajen hulɗa da abokan hulɗarsu da nufin damfarar su. Abin ya kai ga suna iya yin sojan-gona ta hanyar turo saƙon kar-ta-kwana ga al’ummomi daban-daban domin neman su bayar da kai bori ya hau. Abin ya kai ga akan turo wa masu hulɗa da bankuna da ma waɗanda ba sa hulɗar da bankunan saƙonnin neman su tura lambobin asusun ajiyarsu na bankuna ko lambobin katin cirar kuɗinsu na banki da makamantansu, wannan sabuwar ɗabi’a ta tashi da masu son banza da yawa. Hausawa sun ce: “Sabon salo, in ji kaza da ta ji ana shiƙa da daddare.” A yau an fara samun ‘yan damfara suna shiga irin ta ma’aikatan banki, su je gidan mutum su yi sallama da shi su nemi ya ba su lambobin asusun ajiyarsa na banki, kafin ya ankara sun tashi da shi.

    A ɗaya ɓangaren kuma, suna ƙirƙirar hukumomi na ƙarya tare da tallata guraben neman aiki ga al’umma, wannan Fasaha da kimiyyar zamani tana shan wasu masulla.

    4.0 Sakamakon Nazari

    Haƙiƙa Bahaushe ya daɗe yana ta’ammuli da siddabaru. Kusan abu ne mai wuya a iya tantance farkon lokacin samuwar wannan al’ada gare shi. Adabin Bahaushe na ɗauke da hotunan wasu nau’ukan siddabarunsa. Ana samunsu cikin adabinsa na ka da kuma rubutattu. Sai dai siddabaru a Bahaushiyar al’ada bai kasance nau’i guda ba. Ya shafi na baka da kuma wanda ake gudanarwa a aikatace. Siddabaru ya kasance wani babban makami ga ‘yan damfara. Tarin dabarbarun siddabaru suke amfani da shi wajen damfare tunanin waɗanda suke faman tatsa.

    A yau kuwa, kimiyya da fasaha sun samar da wani sabon babi ga siddabarun Bahaushe. Wannan ya fi shafar aikataccen siddabaru kai tsaye, wato siddabarun aiki ba na baka ba. A yau, na’urori irin su kwamfuta da wayar salula sun kasance ja-gaba a cikin ‘yan koren ‘yan siddabaru. Wannan ne kuma ya sa damfarar zamani ta ɗauki wani sabon salo. A yau ba sai baƙo ne ke iya damfarar al’umma ba. Ɗan gida ma na shiga rigar kimiyyar da fasaha, ya fake ya aiko zamba tambkar daga nesa. A irin wannan lokaci, har ma yakan iya shiga cikin ‘yan jaje bayan an riga an ci wawa an tashi.

    Yawanci damfarar zamani masu ilimin kwamfuta ke jagorancinta. Hausawa da ke cikin wannan harkar na ɗaukar hannu daga al’ummu baƙi na kusa da na nesa. Wasu daga cikin salailan damfarar a finafinan Turawa ake nuna su. Wasu kuwa ana kallon su a tarurrukan nuna bajinta na duniya irin su American Got Talent da British Got Talet da Arab Got Talent da Chinese Got Talent damakamantansu. Wasu kuwa akan same su ne daga al’ummun kusa. Tuni jihar Lagos da ke tarayyar Nijeriya ta yi ƙaurin suna a wannan ɓangare na damfarar zamani.

    4.1 Kammalawa

    ‘Yan siddabaru musamman waɗanda ke amfani da hanyoyin da siddabarun ya tattaro domin damfara sun kasance masu tsananin wayo. Bugu da ƙari kuma, suna da saurin nazartar yanayi tare da ƙoƙarin tafiya da zamani a koyaushe. Da zarar zamani ya buga tambari, suna kan gaba wajen taka rawarsa. Wannan ne ya sa suke da saurin samar da sababbin hanyoyin damfara musamman yayin da aka fahimci tsoffin da suke amfani da su. Kamar yadda ya kasance waɗanda suka fi faɗawa tarkon damfara kwaɗayayyu ne da ‘yan zalama, sai abin ya kasance “Karen bana shi ke maganin zomon bana.” Lura da haka, wannan bincike na ba da shawarar cewa:

    1.      A riƙa karantar da dabarun ‘yan siddabaru da damfara a manyan makarantu a matsayin kwas. Wannan zai taimaka wajen wayar wa jama’a kai tare da fitar da su daga sharrin tarko da ƙangin damfarar ‘yan siddabaru.

    2.      A riƙa gudanar da tarurrukan ƙara wa juna sani da wayar da kai dangane da siddabaru da damfara. Hakan zai taimaka wajen ƙara wayar da kan al’umma a matakin ɗaiɗaiku.

    3.      Yana da kyau hukumomin da ke da alhakin daƙile harkokin almundahana da zambar kuɗaɗe su haɗa kai da sauran hukumomin gwabnati tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin a gudu tare a tsira tare.

    4.      Akwai buƙatar hukumomin EFCC da ICPC da dangoginsu su haɗa kai da masana Harsunan Nijeriya domin fassara irin dabarun da suke ganowa ‘yan damfara na amfani da su cikin manyan Harsunanmu na Nijeriya.

    5.      Yana da kyau ‘yan majalisunmu na ƙasa da hukumomin shari’a su tsaya tsayin daka wajen ganin an sabunta dokokin ‘yan damfarar zamani tare da aiki da dokar ga duk wanda aka kama da hannu dumu-dumu yana aikata irin wannan ta’asa.

    Manazarta

    Tuntuɓi masu takarda domin samun manazarta.



    [1]Bunza, (2019) ya bayyana cewa: “A duk yankin Afirka al’umma guda ce ta yi kusa da wayon Bahaushe. Ita ce Asanti da ke ƙasar Ghana.” Ya bayyana wannan a hirar da aka yi da shi a  shirin “Baƙonmu na Mako” a gidan rediyon FM da ke Gusau a Jahar Zamfarar Nijeriya.

    [2]Waɗannan rubuce-rubuce sun haɗa da na Down, (1939); Hoffmann, (1980); Vere, (1981); Herlily, (2001); Gardner, (2014); Chiviriga, (2014) da makamantansu.

    [3]A nan zomo ya yi amfani da “lura” wanda kuwa ɗaya ce daga cikin fitattun halayen ɗan siddabaru.

    [4]Wannan dabara ce irin ta ‘yan siddabaru tare da ɗimbin hangen nesa. Zomo ya san da cewa, duk lokacin da kura ta kawo abinci, to a dukkanin ‘ya’yan ta kawo wa.

    [5]A nan zomo ya nuna wani hali na ‘yan siddabaru, wato “saurin nemo mafita ga matsala.”

    [6]A duba rataye domin kallon tatsuniyar a kammale.

    [7]Wannan ma wasa nna dandali. Misalin yara biyar zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawan mutanen zai iya kai wa goma ko ma sama da haka. Yana tafiya da waƙa, sannan akan yi amfani da kayan wasa yayin gudanar da shi. Kasancewar wasan na dandali ne, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Kayan wasan da ake tanada yayin gudanar da wasan su ne kallabi ko tsumma.

     

     

    Yadda Ake Wasa

    Mutum xaya zai zauna ya miƙe ƙafafunsa. Wannan shi ake kira Allah raini. Wani yaron kuma zai tsaya a bayansa ya rufe masa idanu. Idan ana amfani da kallabi ko tsumma, to da shi za a rufe idanu. Idan kuma babu, to akan rufe ne da hannuwa. Sauran yara kuwa za su jeru a layi. Daga nan wanda ya rufe wa Allah raini ido zai yi inkiya da baki cewa a taho a tsallaka ƙafafunsa. Yaron da ke tsaye a layi zai taho a hankali ya tsallaka shi. Daga nan kuma sai wanda ya rufe wa Allah raini ido ya tambaye shi:

    “Allah raini wa ya tsallaka ka?”

    Shi kuma zai ambaci sunan wanda yake tunanin shi ne ya tsallaka shi. Idan ya faɗa daidai, to zai tashi. Wanda aka ambaci sunan nasa kuwa zai zo ya zauna, wato ya zama Allah raini. Idan kuwa bai faɗi sunan daidai ba, to wani daban zai zo ya tsallaka. Wani lokaci wanda ya rufe wa Allah raini ido zai iya ishara da baki cewa kada kowa ya tsallaka. Sannan sai ya tambaya Allah raini wanda ya tsallaka shi. A nan idan ya ce: “babu,” to ya yi nasara. Idan kuwa ya ambaci sunan wani daban, to ya faɗi.

    Idan yara suka gama tsallaka shi baki ɗaya ba tare da ya gane wanda ya tsallaka shi ba, to wanda ya rufe masa ido zai ba da dama wa yara su je su ɓuya. Yayin da yara suka ɓuya, wanda ya rufe masa ido zai ambaci wuraren da suka ɓuɓɓuya. Amma ba zai fayyace takamaimai waɗanda suka ɓuya a wuraren ba. Misali, wanda ya rufe wa Allah raini ido zai ce:

    “Bayan bishiya, bayan dakali, gefen alamanke …”

    Sai kuma a tambayi Allah raini ya faɗi sunayen waɗanda suka ɓuya a waɗannan wurare. Shi kuwa zai yi ƙoƙarin yin hakan. Misali zai ce:

    “Musa ne a bayan bishiya.”

    Idan ya faɗa daidai to za a ce wa Musa:

    “Taho bisa sayyadarka.”

    Idan kuwa bai faɗa daidai ba, to za a ce Allah raini ya je ya goyo shi ya taho da shi.

     

    Wasu Dokokin Wasa

    i.              Duk wadda Allah raini ya ambaci sunansa bayan ya tsallaka shi (ya tsallaka Allah raini), to shi ne zai zama Allah raini.

    ii.             Yayin da Allah raini ya fahimci ba a tsallaka shi ba, kuma ya faɗi hakan, to wanda ya ƙi tsallakawar shi ne zai zama Allah raini.

    iii.            Idan mutane suka gama Tsallake Allah raini ba tare da ya ambaci sunan kowa ba, to za su je su ɓuya.

    iv.            Yayin da Allah raini ya ambaci sunan wani ɗan wasa a matsayin ya ɓuya a wani wuri, sai kuma aka yi rashin dace ba a nan ya ɓuya ba, to zai je ya goyo wanda ke ɓoye a wannan wuri.

    v.             Wanda aka ambaci sunansa da wurin da ya ɓuya, to shi ne zai zama Allah raini.

    [8]Hanyar da ake gudanar da wannan wasa, yara  ne za su yi tsubi-tsubin ƙasa kimanin uku ko huɗu ko sama da haka. Daga nan mai tafiya zai riƙe ‘yarsa da yatsu. Zai  riƙa sanya hannunsa da gaggawa cikin wannan tsubi-tsubin ƙasa. Zai riƙa yi cikin gaggawa yadda ba za a riƙa ganin lokacin da zai bar ‘yar a ɗaya daga cikin tsubi-tsubin ƙasar ba.

    A yayin da mai tafiya ke canza ‘yar daga tsubin ƙasa zuwa wani tsubin, zai fakii don abokan wasansa ya a je ‘yar a ɗaya daga cikin tsubin ƙasar. Sai kuma a cigaba da tamkar bai ajiye ‘yar tasa ba. Bayan ya kammala sai ya ba da dama ga bokin wasansa da ya nemo tsubin da ya bar ‘yarsa. Idan ya nuna daidai, to ya ƙwace saboda haka shi zai cigaba da tafiya. Idan kuwa bai nuna daidai ba, to wanda ke wasa ne zai cigaba.

    [9]“Mai tafiya” a nan na nufin yaron da ke riƙe da ‘yar tafiya, wanda shi ne zai ɓoye ta a wannan lokaci.

    [10]A nan, “’ya” na nufin tsakuwa ko wani abu mai kama da wannan, ita ce ake ɓoyewa a cikin tsubin ƙasa.

    [11]Kai ne ka zo tsallake rafi, kuma kana tare da kura da akuya da dawa. Idan kana tare da su, kura ba za ta ci akuya ba, sannan akuya ba za ta ci dawa ba. Da zazar ka gusa kuwa, to kura za ta cinye akuya. Idan kuwa akuya da dawa aka bari, to akuyar za ta cinye dawa. A bakin rafin da za ku tsallake kuwa, kwale-kwale guda ne, sannan abubuwa biyu kacal zai iya ɗauka a lokaci guda. Wato zai iya ɗaukar mutum da kuma nau’in abu guda (ko kura ko dawa ko akuya). Saboda haka, dole ka tsallakar da abubuwan da kake tare da su ɗaya bayan ɗaya. To yaya za ka yi hakan ba tare da wata matsala ta samu ba?

    [12]Wani falke ne wata rana ya shiga ruɗani. Ya daɗe ƙwarai yana harkokinsa da raƙuma, ya saba da sha’aninsu sosai. Amma wata rana sai maigidansa ya aike shi kai kanwa daga Agadas ta Nijar zuwa Sakkwato ta Nijeriya. Uku daga cikin raƙuman nan kuwa na musamman ne. Domin ɗaya daga cikinsu, yana cin naman raƙumi ɗan uwansa. Saboda haka, a duk lokacin da ake tafiya, idan dai a jere ne, dole ne ya kasance a gaba. Da zarar wani raƙumi ya shiga gabansa, to zai cinye shi. Raƙumi na biyu kuwa yana cin kanwa ne. Saboda haka, yayin da ake tafiya a jere, dole ne ya kasance a gaba, domin da zarar wani raƙumi mai kanwa ya shiga gabansa, to zai cinye kanwar. Raƙumi na uku kuma yana cin mutum ne. Saboda haka, dole idan ana tafiya da shi a jere, ya kasance a gaba, domin da zarar mutum ya shiga gabansa, to zai cinye shi. Sai raƙumi na uku kuma wanda lafiyarsa ƙalau.

    A nan wannan falke ya fara tunanin yadda zai bi da waɗannan raƙuma, ba tare da wata matsala ta faru ba. Yaya zai tsara tafiyar?

    [13]Wasu masu ne guda uku Allah ya yi su abokan juna. Shi dai da ma maye ba ya cin maye ɗan uwansa. Kowanne daga cikinsu yana da ɗa. Sai dai Allah ya yi ‘ya’yan nasu ba mayu ba ne. watarana sai tafiya ta kama waɗannan mayu uku da ‘ya’yansu. Suna tafe suna taɗi na abota. Amma kowannensu a ankare yake, ba zai taɓa kuskuren bazawa ko nan da can ya bar ɗansa kusa da ɗaya daga cikin mayun ba. Domin kuwa, da zarar uban ɗaya daga cikin ‘ya’yan baya kusa, to sunansa nama.

    Suna cikin tafiya sai suka iso wani madaidaicin kogi. Ruwa ya kawo maƙil. Suka duba haka, sai ga jirgin ruwa, amma ba matuƙi. Sannan jirgin mutane biyu kaɗai yake iya ɗauka. Saboda haka, dole ne su riƙa shiga ta bibbiyu, sannan idan biyun da suka shiga suka haye, ɗaya daga cikinsu ya dawo da jirgin. Da haka da haka har su ƙetare gaba ɗaya. To a nan fa dambarwar take. Ta yaya ne za a yi hannan hayi ta bibbiyu ba tare da wani maye ya tafi ya bar ɗansa an cinye shi ba?

    [14]Domin samun cikakken labarin, sai a duba Imam, A. A. (1994). Magana Jari Ce 2. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

    [15]A nan musamman ana magana kan ‘yan damfara da ke amfani da siddabaru a matsayin tsaninsu na kai wa ga nasara.

    [16]Za a iya tunawa da tarihin samuwar madubi ga Bahaushe. A lokacin da  ya ga hotonsa cikin badubi, sai ya fashe da kukan tunanin ai babansa da ya daɗe da rasuwa ne. Wannan ya sa yake karɓar madubi a matsayin furfuren dukiya mai tarin yawa.

    [17]An samu wannan bayani daga bakinsa, yayin da yake gabatar da lacca a ajin ‘yan digiri na biyu, a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, ranar 24 ga watan Oktoba, shekara ta 2019.

    [18]A 2go, rooms sun kasance kafafe da ke haɗa mutane da dama. Duk wanda ya tura saƙo, to sauran mambobin za su gani. Mai gocredit ne kaɗai ke iya tura saƙo arooms.

    Pages