Hausa Gagara Gasa

  Wannan waƙa ta taɓo wasu ci gaba da Harshen Hausa ya samu wanda ya sa harshen ɗaukakuwa sama da tsaransa. 

  hausa

  Amshi: Harshen Hausa ya yi fice,
                Ya rufe ƙofa ko ta ina. 

  Da sunan Allah mai girma shi ke iko ko a ina,
  Ka ƙara basira a ƙwaƙwalwa tawa da ke a cikin kaina,
  Na tsaro zance ra-ra-ra da babu kure ciki ko sauna,
  A kanta fasahar ‘yan Hausa da ta rufe ƙofa ko ta ina. 

  Ninka salati ga rasulu manzo mai ƙarshen girma,
  Muhammadu ɗan Abdullahi mai ƙima mai alfarma,
  Har da iyalai na gidansa da sahabu mazaje sha-fama,
  Da sauran masu biyar sunna a faɗin dunya ko ta ina. 

  Wani ya ji ina ta zubar zance a kanta fasahar ‘yan Hausa,
  Na ce dukka a tsaranta ta fi gaban kanwar lasa,
  Sai ko ya ce ‘yar Hausar ce ta zamto gagara gun gasa?
  Na ce masa tabbas kuwa Hausa ta rufe ƙofa ko ta ina. 

  Na ce mar ba na maganata sai fa da hujja mai ƙarfi,
  Zauna sannan saurara in ba ka bayani don zai fi,
  Idan da abokai ka kira su ku ji ni a tare ba laifi,
  ƙarshen zancena tabbas ku gane ficenta ko ta ina. 

  Da fari a harsunnan dunya Hausa tana a sahun farko,
  A jerin dukkan harsuna gurbin sha ɗaya taɗ ɗauko,
  It ace ta ɗaya a sahu na gaba idan a Afirka ka sauko,
  A Afirka ƙwarai kuwa ta yi fice, ta rufe ƙofa ko ta ina. 

  Harshen fari yawan jama’a shi ne Madarin birnin Sin,
  Hausawa a ƙiyasinsu miliyan ɗari da daɗin hamsin,
  A baƙar fata ba mai wannan sai ita ɗai Hausar yasin,
  Ko a fagen adadin jama’a ta rufe ƙofa ko ta ina.

   A dukka baƙaƙen al’umma ba mai wayon Hausawa,
  Suna gaba gun wasan dambe ko kuma filin kokawa,
  Sun san kan wasa da maciji har kura su yi ɗaurewa,
  Ko a fagen wasan tauri sun rufe ƙofa ko ta ina. 

  A fannin sana’a sun yi fice tun tarihi can baya,
  Saƙa, fawa, dukanci, gyartai ke fafan ƙwarya,
  Noma, ƙira, wanzanci Hausawa ba sa baya,
  Har a fagen su ko a sakai sun rufe ƙofa ko ta ina. 

  Fage na gini tun can baya Hausawa sun yo suna,
  Ganuwa su ke tsara ta su nemi tsari gun ‘yan ɓarna,
  Leƙa ginin fadojinmu ka gane akwai manyan magina,
  A Afirka karan kaf Hausawa mun rufe ƙofa ko ta ina.

  Tsari na gida a gina a shiga Afirka a da ba tamkar mu,
  Rumbu gefe ga madafi can ga bayi sai dai mu,
  Can zaurukka can bishiya nan ɗakunnan matanmu,
  Zaman gandu ma mun yi fice mun rufe ƙofa ko ta ina.

  In ko abinci ka so magana mu ne ja-gaba gun tafiya,
  Ganyaye, saiwa, tsaba, duk na nan kaya-kaya,
  Nama, kifaye nan ma ana yin kiwo ko a saya,
  Nau’i-nau’i na abinci mun rufe ƙofa ko ta ina.

  Mu leƙa adab fannin waƙa Hausa take farko a gaba,
  Yawan kasafi na mawaƙa don ba ay yi ya harshen Hausar ba,
  Aji da aji na mawaƙa duk ba ai yi kamar mu a tsari ba,
  A wannan fannin Hausawa mun rufe ƙofa ko ta ina.

   Muna da mawaƙan al’umma akwai ko na fada a Hausawa,
  Akwai na maza ga nan sha’awa sai sana’a ku yi jerawa,
  Muna da na talla da barkwanci ko aiki aka aikawa,
  Daɓe da daka da kaɗi da niƙa da sauran aiki ko a ina.

  Ana ko karantar shi harshen a nan ƙasa da wajen Hausa,
  Ingila, China da Amurka wassu suna yi a Faransa,
  Yawan adadin farfesoshi da daktocinmu a fanninsa-
  Ya sa ni nake ta bugan ƙirji da nuna ficenmu ta ko ta ina.

  Ana digiri kan ita Hausa FUGUS da UDUS ka ji zancena,
  ABU ga BUK, KASSU da BASUG duk su na,
  Akwai UNIMAID ga UMYUK can har da SLUK a hasashena,
  Ana yi har can FUK ta rufe ƙofa ko ta ina.

  Ka ga ana Hausa a FULAB har da su FUDMA can su ma,
  Ga FUG, GSU su ma sun ce ba dama,
  NSUK, YSU, YMSU a Kano ma,
  Fannin nazari da karatu mun rufe ƙofa ko ta ina.

  Haƙiƙa bayan ita Hausa ba mu da harshe mai wannan-
  Yawan masana da na ɗalibbai babu kamarta a ƙasar nan,
  Yawan littaffai, kundaye ba ta da tamka kuma sannan-
  Ko a yawa na fagen nazari ta rufe ƙofa ko ta ina.

  Abin da ya saura guda ɗai ne za ni faɗo shi ku saurara,
  Hausa ta zam harshe na ƙasa lallai da kuwa mun mora,
  Ƙasarmu ko da ta bunƙasa da kuwa ta kere tsara,
  Sai ka ga mun yo fintinkau mun rufe ƙofa ko ta ina.

  Ka leƙƙasashen duniya manya dukka ka dudduba,
  In dai har ka ga ta ci gaba ba tar riƙe harshen wani ba,
  Harshen ilimi harshen mulki ba zai zama harshen bare ba,
  Sai dai harshe na ƙasarta da shi aka aiki ko ta ina.

  Abokai nan zan saka aya in rufe marfin ƙalamina,
  Ga masu biɗar wa yay yi ta Abu-Ubaidatu sunana,
  Na taso a jahar Bauchi, Misau aka binne cibina,
  Ya Jabbaru muna roƙon daɗin albarka ko ta ina.

  author/Sani, A-U.

  journal/Poem
  pdf-https://youtu.be/bkqYdCWZ18E

  paper-https://youtu.be/bkqYdCWZ18E

  Pages