Mu Yi Haƙuri (Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Daga Ɓoyayyen Marubuci - Ta Abu-Ubaida Sani
  Da fari zan sako Allah ne Mahaliccin mu,
  Mai ba mu kariya da  ke amsa buƙatunmu,
  Da mun yi addu’a zai amsa mana roƙonmu,
  Ƙaro daɗin basira Allah a ƙwaƙwalenmu,
            Mu tsara baituka tsaf ba tare da aibi ba.

  Allah ƙaro salati ga shi dai manzonmu,
  Haɗa da dukka sauran sabban manzonmu,
  Har da alaye da tabi’ai magabatanmu,
  Ka ba mu kariya Jalla tsare imaninmu,
            Mu zamma masu gaskiya ba ɗai musu ba.

  A yau dai zance ne tsubi-tsubi gare mu,
  Sai dai babu lokaci na haska zuciyarmu,
  Za mu tsakuro ne kaɗan na ƙwaƙwalwarmu,
  Sai dai fatar da mun kai a gane madosarmu,
            Ba a karanta kawai matsayin labari ba.

  Akwai damuwa guda da ta mamaye ƙalbinmu,
  Jama’armu ga shi har yau sun kasa fahimtarmu,
  Sun kasa fassaran ƙwarai ga halin nan namu,
  Wannan ya sa a yau muke feɗe salailanmu,
            A rayuwa na tare bai kyauttu da zargi ba.

  Wanda ya ce shi to ba shi ba ne gare mu,
  “Man ƙala ana…” zance daga manzonmu,
  Wannan dalili kenan na rurrufe zancenmu,
  Za dai mu ba da labari kaɗan daga harkarmu,
            Da fatan a fahimta ba a karanta a aje ba.

  Shigar mu jami’ar nan farko na rayuwarmu,
  Mun ƙwallafa ƙaunar ‘yan kwas a zuciyarmu,
  Mun ka fara nemo su don haɗi na kanmu,
  Da mun tarar guda ƙauna ko jinin jikinmu,
            Amma a wagga hali ba mu samu haɗin kai ba.

  A nan sabon nazari ya zo ga zuciyarmu,
  Mun ka iske H.O.D. domin ya taimake mu,
  A nan ya ba mu lambobin duk ‘yan uwanmu,
  Har 2go sannan muka bi ‘yan uwanmu,
            Abin baƙin ciki sam ba a nuna haɗin kai ba.

  Da anka yo gwajin farko ag gare mu,
  Waɗanda sunka faɗi sun fi addadinmu,
  Wani har ya tambaye ni menene abin damu?
  Ya ga na damu, gashi ko twenty  na samu,
            Na ce me amfani nai ‘yan uwa ba su samu ba?

  Bayan mun fara ɗan sabo da waɗansunmu,
  Har littafansu muke karɓa ‘yan uwanmu,
  Mu kofe musu note  daga namu don su samu,
  Idan ko har assignment aka bayar gare mu,
            Ba za mu yi mu bar saura ba su samuba.

  A kwan a tashi mun samo haɗi na kanmu,
  Tutorial group muka sa don ya agaje mu,
  Ashe wani sabon artabu ne hakan gare mu,
  Zuwan ganin-dama ake ta yi gare mu,
            Amma muka jure ba mu nuna fusata ba.

  Bayan tutorial ko wassu su iske mu,
  Su ba da uzzururrukan ƙarya ag gare mu,
  Dole muj jiyo kunya gunsu ‘yan uwanmu,
  Mu ɓata lokacin da ya dace da karatunmu,
            Duk wannan ba ya sa gobe su gyara ba.

  Wasu har suna jin haushi ma gare mu,
  Ganin yadda muke ɓarna na lokacinmu,
  Mu ko tausayi ya hana nuna zuciyarmu,
  Daɗinta ma a sannan ba  jama’a tuli gare mu,
            Sai dai a zuciya ba mu so a rinƙa yin haka ba.

  A sa’ilin ko ba sisters  a tsakanin mu,
  Mahaɗarmu conɓocation  sannan marabarmu,
  Baban dalilinmu a nan shi ne filosofinmu,
  A taimakon brothers  ba tsangwama gare mu,
            Ba kamar na sisters  da za a ba wa sharhi ba.

  Mun riga a da can mun sa wa zukatanmu,
  Mun biye wa tsantsar kunya da ke jininmu,
  Ba mu iyya ko da kallon ‘yan uwanmu,
  Walau a kan hanya ne ko suna gabanmu,
            Tsangwamar da hakka ya ja ba ƙarama ce ba.

  Kullum in mun ka dawo hostel matsuguninmu,
  Abokai ka ɓulɓulowa da ƙorafi gare mu,
  Wai mun ido huɗɗu da su mun kau da kanmu,
  Ga shi ba mu rantsuwa don mun hani ga kanmu,
            Haka suke taffiya ba tare da sun yarda ba.

  A yau da gobe har jama’a su kai yawa gare mu,
  Waya a kan waya har ya yo yawa gare mu,
  Ko mun yo bayanin haka ba a tausayin mu,
  An manta da ko mu ma akwai aiki gabanmu,
            Mun zi mu karɓi takarda ba mu yi bauta ba.

  Duba an kasa gane ajistin da ke gare mu,
  Dan mun ce ba mu sani ba sai a tsangwame mu,
  Wai mun sani ba mu son koyar da ‘yan uwanmu,
  Mu ma fa ɗalibai ne sai an koyar mu samu,
            Mutane muke ba a haife mu da sani ba.

  A ƙarshe rayuwa ta fara tsaurara gare mu,
  Zaman school  gaba ɗaya yaf fice a kanmu,
  Akwai ma lokacin da muka ɗauki tarkacenmu,
  Ana fa jarrabawa muka koma garinmu,
            Ba don hakan ba ko da rai bai huta ba.

  Halan wani zai ga kamar raki gare mu,
  Mu ko mun ga ma ɗunbin na ƙoƙarinmu,
  Mun yi juriya kuma mun danne zuciyarmu,
  Don har malamai na ba da shawara gare mu,
            Bai kyautu mai ka  a ce ya samu ɗai ka ba.

  Babu lokacin hutu sam a ajandunmu,
  Lokacin morokon  wane na karatunmu,
  Lokacin ƙara’in wance na assamenmu,*
  Lokacin kallon ball wane tuttoriyanmu,*
            Sun cinye lokacinsu namu ba su ƙyale ba.

  Duk waɗanga hali mun danne zukatanmu,
  Sai kwatsam ko ga shi an ta da zuciyarmu,
  Rainin hankali wayo an ka yo gare mu,
  Sai dai mun ba da shawara a birni na tunaninmu,
            Gemun da ba fari, ba a sa masa lalle ba.

  Ku yi haƙƙuri da mu sisters, gare mu,
  Za mu so sannan idan kun ka fahimce mu,
  Ilahu ya sani darajar ku ag gurinmu,
  Ku ne wayayun ƙwarai mu ag gurinmu,
            Ba masu tantama da hukuncin Allah ba.

  Hankalinku ne ya sa kuka kama zukatanmu,
  Kun tsare mutucinku ta koyarwar manzonmu,
  Masu taƙamar wayewa dabbobi ne gare mu,
  Sun bijirce wa tarbiyyar addini al’adunmu,
            Za su yi da-na-sani ba ko da nisa ba.

  Ubaida martabarki da girma take gare mu,
  Ko don fa sunanki da ya kama zuciyarmu,
  Sumayya ƙoƙarinki ne ya kama hankalinmu,
  Tarbiyya irin taki da shiga ta addininmu,
            Da ikon Rabbana rayuwa ba ta muku ciwo ba.

  Sa’adatu kin zamo kamar ‘yar uwa gare mu,
  Ƙoƙari a rayuwarki ya kama hankalinmu,
  A’isha haƙiƙa kina a tunaninmu,
  Kina da son karatu da tambaya gare mu,
            Ya Allah ya ba ku janna ba da hisabi ba.

  Ku miƙa gaisuwar nan ga elder sistarmu,
  Zamanta gidan aure ya sa ta zama antinmu,
  Ku ci gaba da kauce wa dukkanin haramu,
  Za ku kai ga nassara ga dukkanin alamu,
            Ba wai burgewa a jami’a kawai ba.

  Su ce da mu ƙauyawa mu ce su batsattsu,
  Su ce da mu primitiɓe mu ce su watsattsu,
  Hulɗa da mu su yanke ga Jalla tasu ta datsu,
  Ko dai su tuba duniya ko kabari su matsu,
            Manzo ya nuna haka ba ƙirƙira nake ba.

  Duk wacce ke tunƙaho wai ita ta waye,
  Tana da samari tuli har tana tawaye,
  Tsaya rayuwa ta ja buƙatarsu ta janye,
  Ta zam tamkar matatta bayan ga ta a raye,
            Wanda bai bi Allah ba, ba ya ga da daɗi ba.

  Wasu lokuta muna ba ku sharwarinmu,
  Mu ma muna biɗa ko shawara ku ba mu,
  Hakka ne zaman tare don cika burinmu,
  Allah ya ba mu sa’a ya ƙara taimakon mu,
            Ya sanya wagga boko ba a banza za mu yo ba.

  Arba’in ne baitukanta mun yi accumulation,
  Sadaukarwa ga sisters ne da sun ka yo adhesion,
  Waɗanda su ga Allah ne sun ka yo retention,
  A kan shi kaɗai yake ba da acƙuisition,
            Allah da mu da su duka ka ba mu cigaba.

  Pages