Duniyata – Ta Abu-Ubaida Sani
  Da kalula a hannuna,
  Da zogi a hannuna,
  Da ciwo a jikana,
  Da ƙunci ƙalbina,
  Na baro duniyata.

  Da zafi a jinina,
  Da haushi ƙirjina,
  Da tunani kayina,
  Da buri zucina,
              Na baro duniyata.

  Da likita gabana,
  Da Tsaure gefena,
  Da Khalid ta samana,
  Da idanu duk kaina,
              Na baro duniyata.

  Na dubi muhallina,
  Wurin dai kwancina,
  Na gane wurin dai na,
  Nai tsam da tunanina,
              Don hango duniyata.

  Zuci ne tai fama,
  Baƙin ciki da nadama,
  Ƙwaƙwalwa ta bi ita ma,
  Duk jiki sai kyarma,
              Na mararin duniyata.

  Rai da ya tumbatsa,
  Zuciyata sai ta matsa,
  Ƙwaƙwalwa ko ta watsa,
  Tun gaban ma in kintsa,
              Tuni na wuce duniyata.

  A duniyar ba mugu,
  Sai dama babu hagu,
  Ba ‘yan uba ko shegu,
  Ba hassada in ka ɗagu,
              Wani abu sai duniyata.

  Ba miskili ko raggo,
  Kowa aiki ya agogo,
  Can gaskiya tai zango,
  Halin ƙwarai yai zango,
              Da lumana a duniyata.

  Idan gari ya waye,
  Duhun dare ya yaye,
  Ka so ganin tsuntsaye,
  Da ke ta yin gewanye,
              Suna waƙe duniyata.

  Idan ka ja numfashi,
  Ya gauraye ka da ƙamshi,
  Idonka yai wani lumshi,
  Saboda daɗin ƙamshi,
              Ku so ganin duniyata.

  A duk gefen hanya,
  Dashe an sassanya,
  Fulawowi ga bishiya,
  Ganyensu lif-lif sun tsaya,
              Ka kwan kallo duniyata.

  Ga gulbi ga ƙorama,
  Gudanar ruwa mai ni’ima,
  Idan ka ta da kai sama,
  Gajimare sun yi laima,
              Dubun ni’ima duniyata.

  Ka kalli namun daji,
  Bayan gari nan jeji,
  Ga nan duwatsu daji,
  Ga itatuwa nan daji,
              Daɗin gani duniyata.

  Idan rana ta tsala,
  Cikin gari da walwala,
  Kowa garin ba matsala,
  Zaman garin ba wahala,
              Da walwala duniyata.

  Fuskar kowa sai fara’a,
  Wadatar zuci da dabi’a,
  Halin ƙwarai ga ɗa’a,
  Matan mazan sun sa’a,
              Zamantakewa duniyata.

  Ba faɗa ba gaba,
  Ba a sata ba fargaba,
  Ba a fashi babu daba,
  Ba ka ga mai laifi ba,
              Ba kurkuku duniyata.

  Kun san aikin ‘yan sanda?
  Suna zaga gida-gida,
  Akwai matsala wanga gida?
  Domin su taimaki gida.
              Ba criminal duniyata.

  Idan dare ya soma,
  Idan ka ta da kai sama,
  Jerin taurari a sama,
  Tsakaninsu ba gardama,
              Kamar al’ummar duniyata.

  Ina cikin jin daɗi,
  A duniya mai daɗi,
  Tamkar mashiyi na maɗi,
  Kwatsam! Katsewar daɗi,
              Sai na baro duniyata.

  Tun kafin na baro ma,
  Nakan ji dai sama-sama,
  Har jiki ya yi dama,
  Zuciya ta shirya ma,
              Don baro duniyata.

  Nan kuwa a hannuna,
  Kamar ruwa ke gudana,
  Na ji sanyi a hannuna,
  Na ƙi motsa jikina,
              Rabina na duniyata.

  Ashe jini ke malala,
  A ƙasa yana dalala,
  Likitoci sun shagala,
  Yayin wannan tultula,
              Ni ko ina duniyata.

  Cike bokiti da ruwa,
  Aka zo don gogewa,
  Ruwan tuni ya rinewa,
  Jini ya yo komawa,
              Sannan na baro duniyata.

  Likitoci sun ruɗe hala,
  Suna tambayar sila,
  Na neman salsala,
  Kawai dai sun wahala,
              Amsa na duniyata.

  In dai taƙaita labari,
  Na dawo duniyar sharri,
  Da ke da ɗumbin garari,
  Ga ko mugun sharri,
              Nitsuwa sai duniyata.

  Wani nawa ya ji ni,
  Ina faman guna-guni,
  Na kushe halin zamani,
  Da yabon duniyata ni,
              Ba na kushen duniyata.

  Ya zo domin tambaya,
  Game da wagga duniya,
  Kawai sai nai dariya,
  Na ta da kai samaniya,
              Niyar zuwa duniyata.

  Zuwanta ai ba wahala,
  Buƙata kawai ka samu sila,
  Kafin ka ankara walla,
  Tuni da kai an lula,
              Sauƙa sai duniyata.

  Ba na buƙatar mota,
  Tafiya babu jigata,
  Kafin ido ya ƙifta,
  Kafin mashi ya gifta,
              Na kai ga duniyata.

  Idan ka harba bindiga,
  Daidai sanda na ruga,
  Kafin harsashi ya shiga,
  Tuni fa ni nakan riga,
              Ƙulewa duniyata.


  Pages