Waƙar Ranar Mawaƙa – Ta Abu-Ubaida  Waƙar da aka shirya domin shiga gasar waƙa ta Ƙungiyar Marubuta Waƙoƙin Hausa Reshen Jihar Bauchi, wanda aka gabatar ranar 12-12-1439AH a ɗakin taro na Gwani Mukhtar da ke cikin fadar Mai Martaba Sarkin Misau

  1.0 Gabatarwa

  An shirya wannan waƙa domin shiga gasar da Ƙungiyar Marubuta Waƙoƙin Hausa Reshen Jihar Bauchi ta shirya wanda za a gabatar ranar 12-12-1439AH. Da yake dokar gasar ta nuna za a waƙe waƙa ne, sai wannan takarda ta ga dacewar taɓo abin da ya daɗe yana ci wa marubuta waƙoƙi da ma masu rerawa tuwo a ƙwarya. Wannan abu kuwa shi ne kushe da tsangwama da suke samu daga al’umma ta ɓangarori daban-daban. A bisa wannan ne kuma aka ƙulla zaren tunanin waƙar.
  A cikinta an yi ƙoƙarin kawo muhimmancin waƙa har kimanin guda ashirin da uku. Gudun kada a yi ta bugun jaki ba tare da an bugi taiki ba, sai aka yi ƙoƙarin nuna cewa, waƙa hanjin jimina ce, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Da ma dai Bahaushe na cewa: “Kowane allazi da nasa amanu.” Saboda haka, an yi ƙoƙarin bayyana cewa, waƙa na iya kasancewa ta ƙwarai yayin da kawai aka yi amfani da kalamai da kuma manufa nagari. Koma bayan haka kuwa, sai dai a ce, Allah ya kyauta!

  2.0 Waƙar ‘Amfanin Waƙa’

  1.         Wahidun da shi ke sa a yo fice,                                 
  Wanda ko shi ne ke kawo dace,
  Wahidun daɗo salati ga fitacce,                     
  Wa ahlihi sahabu dukka jimlace,

  2.         Allah ɗora ni a hanyarka ta dace,
  Ana rawa ɗan makaɗi ko zai fice,
  A yau jigon da ni na ƙwanƙwance,
  Amfani na waƙa ni za ni fayyace.

  3.         Ƙabila idan harshenta yam mace,                  
  Ƙarancin mawaƙa ne da bincike,
  Ƙorafi akan isar da shi sirrance,                     
  Ƙunshe cikin azanci fasahar zance.
                        
               
  4.         A ba da nishaɗi waƙa hanya ce,
  A fanni na ilimi ma ko tai fice,
  Ai a faɗɗakarwa waƙa gwana ce,
  Akan wa’azantar da waƙa tabbace.

  5.         Rumbun kalmomi waƙa ta kasance,
  Ranar da sunka ɓace ga su killace,
  Rumbu ko take na al’adu tabbace,
  Ran da ake nema to ga su taskace.

  6.         Da waƙa har akan sa zuci ta huce,
  Da ɗai a bi daidai bayan an kauce,
  Da ran mawaƙi ya zamo a ƙuntace,
  Da ya zube ga waƙa sai fa ya mance.

  7.         Akan ma kafa hujja da waƙa ga zance,
   “Ai ma ma’anar kaza, kaza ta kasance-
  Ai ko duba wane kaza ma hakka ya ce,
  A duba waƙarsa kaza a kuwa tantance.”

  8.         A inda ma ake jin nauyin a yi zance,
  Akan saka shi waƙa a isar kaikaice,
  A da, da yanzu duk waƙa ta kasance,
  Arziki da hanyar samun masarufi ce.

  9.         Ka duba yanzu waƙa tamkar sana’a ce,
  Ka san ko ba riba sai ribar zuba zance,
  Kuma a siyasa yau ita babbar jigo ce,
  Kasuwa ta farfaganda ko dillaliya ce,

  10.       A nan harshe waƙa tamkar maƙera ce,
  Akan ƙeƙƙera ƙira amma fa na zance,
  Akan koyar da harshe kenan a taƙaice,
  A sigar waƙa, ga salon sarƙafa zance,

  11.       Ga masu kasuwa ko tallafi ta kasance,
  Gama cikinta ne ake ta tallace-tallace,
  Ga sauran ɓangarorin adabi na zance,
  Gami da rubutacce ko matallafiya ce.

  12.       A farko dai karan kanta ta kasance,
  A ɓangare na adabin baka da rubuce,
  A cikin labarai waƙa takan kasance,
  Akan ko rera ta don a ƙayata zance.

  13.       Bincika tatsuniya ka gan ta tabbace,
  Bibiyi wasanni ciki waƙa ta yi fice,
  Bukukuwan Hausa ko waƙa fitila ce,
  Ba ta zama baya fim [1]a zamanance.

  14        Akan rera waƙa don aikace-aikace,
  Aikin noma, kitso, daɓe ka ji zance,
  A sannan ita hanyar saka tarbiya ce,
  Akan tsara ga yara sannan a yi dace.

  15.       Takan zamo ita hanyar yaɗawa ce,
  Takan baza harshe a duniya yai fice,
  Ta kan kasance ko hanya ta yabo ce,
  Tarihi har wa yau waƙa kan kundace.

  16.       Akan bayyano nufi a gwamnatance,
  Ai nuni ga yadda shirin zai kasance,
  Ashirin da ukku ne na kawo a taƙaice,
  Amfani fa na waƙa mu ƙara bincike.

  17.       Rayuwarmu waƙa babbar hikima ce,
  Ruwa biyu gare ta ko takan gurɓace,
  Ranar da anka yo mummunan zance-
  Ranar an ɗauki alhaki, babbar illa ce.

  18.       A taƙaice waƙa kenan takan kasance,
  A matsayi na hanya ta kai wa ga dace,
  A fa gefe guda ko sila ta kaucewa ce,
  Allah dai ya sa Musulmai mu yi dace.

  19.       Ga tambaya, shin ka san ita iri-iri ce?
  Ga jeranton rukunen mui ta binkice:
  Gargajiya waƙa fa a fari ta kasance,
  Ga ta ga wasanni da aikace-aikace.

  20.       Akwai ta gargajiya ta bakka wacce,
  Ake da buƙatar kayan kiɗi a taƙaice,
  Akwai ko rubutatta da ake rubuce,
  Akwai ko ta zamani ta situdiyo ce,

  21.       Sannan waɗan nan da munka lisafce,
  Su ma sun fa rarrabu iri-iri a taƙaice,
  Sai ka je ka duba don ƙara binkice,
  Sansani na fagen waƙa faɗi yalwace.

  22.       Akwai farin jini ga mawaƙi da yin fice,
  Allah ko ya ba shi falsafar haɗa zance,
  Ai idan ka ɗai taɓo shi ka shiga zance,
  Amon wuta da harshen taragon zance.

  23.       Rabbana du’a’ina ga kai ka amince,
  Rabbana dukan mawaƙanmu su dace,
  Rabbi rahhamarka ba su, su ni’imce,
  Ranar da za a tsaya za ko a tantance.


  24.       Wanda ka cin duddugensu har da yafice,
  Wahabu ka shirya shi hanyarka ta dace,
  Wanda ko ya fanɗare sa shi ya galgalce,
  Wahabu mu da shi tsakaninmu dangace.[2]

  25.       A ce masu tsangwamar sun layince,
  A ce masu ƙorafin ko sun wayince,
  A ce masu ƙin jininmu sun amince,
  Ai ko za a ɗau ilimi haƙiƙa tabbace.

  26.       Ƙaramin mawaƙi nake ɗa gun sani,
  Ƙanƙani Abu-Ubaida mai so ya sani,
  Ƙasata Misau ne ko can aka san ni,
  Ƙarƙashin Jahar Bauchi ta kasance.

  27.       A SHATALAMƊA ne na wallafa ta,
  A kawo gyaran kuren da ke a cikinta,
  Ashirin da bakkwai yawan baitukanta,
  Alhamdulilla tamat nan na cike zance.

  3.0 Taƙaitaccen Sharhi

  Waƙar ta kasance mai zubin ƙwar huɗu. Adadin baitukanta ashirin da bakwai ne (27). An buɗe waƙar ne da yabon Ubangiji da kuma salati ga Manzo. Sannan tana da babban amsa amo na ‘ce’. Daga farko za a iya zaton waƙar mai zubi guda ne ta siffar amsa amo, musamman yayin da aka yi la’akari da yadda aka yi amfani da ‘ce’ a matsayin ƙafiyarta tun daga baiti na farko har zuwa na ashirin da biyar (25). Sai dai yayin da aka dubi baiti na ashirin da shida (26) da kuma na ashirin da bakwai (27), sai a ga cewa, lallai ƙafiyar ‘ce’ ta kasance ne kawai babban amsa amo. Lura da wannan bayani kuwa, ƙaramin amsa amo da aka fi yin amfani da shi cikin waƙar shi ne ‘ce’. An yi amfani da wasu ƙananan amsa amo, wato ‘ni’ a baiti na ashirin da shida (26) da kuma ‘ta’ a baiti na ashirin da bakwai (27).
  Baya haka, an yi amfani da wasu salailai cikin waƙar. Ɗaya daga ciki shi ne salon wasa da harshe. Misalin wannan salo ya zo a baiti na tara (9) inda aka kawo kalmomin riba (haram) da kuma riba(r) (halal) a ɗango na huɗu. Akwai kuma wurare da aka yi amfani da karin magana da kuma salon magana. Misali a baiti na biyu (2), an yi amfani da karin maganar da Bahaushe ke cewa: “Kowa ma ya yi rawa balle ɗan makaɗi?” A baiti na ashirin da ɗaya (21) kuwa, an yi amfani da salon abuntawa, inda aka bayyana tarin ilimi da ke ɓangaren waƙa a matsayin fili wanda ke da faɗi da yalwa.
  A baiti na ashirin da huɗu (24), an yi amfani da baƙar addu’a. A cikin baitin an yi mummunar fata ga waɗanda suka ƙi shiryuwa. An yi amfani da kalmomi masu sauƙi a matsayin tubalan ginin waƙar. Sannan ba a sanya kurman baƙi ba. Wannan ne kuma ya sa waƙar ta kasance mai sauƙin ganewa ga mai karatu. Wani salo da aka yi amfani da shi kuma shi ne, tabbatar da zubi guda na harufan da ke buɗe ɗangwayen kowane baiti. Yayin da aka ɗauki abajadan farkon baitukan, za a fahimci cewa rubutu aka yi, wato an rubuta: “WAƘAR DA AKA GABATAR A GASAR WAƘA.”
  Kamar yadda aro ya kasance abincin harshe, an yi amfani da salon aron kalmomi a cikin wannan waƙa. An yi wannan aro ne musamman daga kalmomin Ingilishi da kuma na Larabci. Misali, a baiti na goma sha uku (13) an yi amfani da kalmar Ingilishi ta‘fim’ (sai dai an riga da an Hausantar da wannan kalma). Kalmomin Larabci kuwa, tun a baiti na farko za a fara tsintar misalansu, kamar su ‘Wahidun’ da ‘ahlihi’ da dai sauran makamantansu.
  Kamar yadda aka bayyana a gabatarwa, babban jigon waƙar shi ne fito da amfanin waƙa, domin ƙarfafa wa marubuta da masu rera waƙoƙi (da ke kan hanyar daidai) guiwa. Da ma dai sun daɗe suna shan tsangwama daga al’umma. Irin wannan tsangwamar ce ma ta sa Fati da Kamis suka nuna ƙorafinsu a cikin waƙarsu mai suna Ranar Ɗaya ga Watan Ɗaya. Suna cewa:

  Sai a ce kar ka auri mai waƙa,
  Mace ko namijinsu su duka,
  Maroƙa ne baƙar harka,
  Ba a bambance mu gun ƙyama.

  Fati wai don muna waƙar,
  Aka sa mu cikin sahun shirkar,
  Iko daga Rabbana Ƙadir,
  Waƙa ta zam abin ƙyama.

  A gaba kuwa, har suke nuna cewa, kyawun waƙa ko rashin kyawunta ya danganci yadda aka samar da ita. Suna cewa:
  Waƙa na kai mutum fa wuta,
  Idan a cikinta yai wauta,
  Tana kuma kai shi aljannata,
  Idan a cikinta yai salama.

  Ko me ka faɗi cikin waƙa,
  Da shi za ai hukuncinka,
  In alkairi ka sassaƙa,
  In sharri ne da shi shi ma.

  A cikin wani lamari mai kama da wannan, ga bisa dukkan alamu Aminu Ladan Abubakar (ALA) da sauran ‘yan ɗaninsa sun kai bango ga turar da ake musa, wanda har suka fitar da waƙa mai suna HASBUNALLAHU… A cikinta sun yi baƙar addu’a ga masu tsangwamar su da hana su sakat. Suna cewa:
  Muna da maƙƙiya wanda ka yarda mun ka gan su,
  Akwai na ɓoye wanda kawai Rabbi kai ka san su,
  Rugurguje shirinsu ka maida shi bissa kansu,
  Da sun kira ka Allah don miƙa buƙatunsu,
  Ka juyar da buƙatunsu ya Zuljalalu.

  Cutar Gloria har cholera gami da tension,
  Cutar hawan jini har Typhoid in addition,
  Cuta ta kuturta da makanta a conclusion,
  Cuta ta ƙanjamau mai hana ɗan Adam emotion,
  Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

  Cuta ta Asthma da Koshorko ka sa gare su,
  Cutar Pneumonia da ƙarzuwa cikin jikinsu,
  Ciwo na karkare da kurkunu ka sa gare su,
  Cutar Malaria Feɓer sa ka kassara su.
  Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

  Cuta ta Anthraɗ Allah sa a jikkunansu,
  Cuta ta Glaucoma a sa a maganansu,
  Cuta ta Trachoma maƙala wa ijjiyarsu,
  Ka mai da su kurame ka ɗoɗe maganansu,
  Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

  A cikin waƙar, sun nuna irin salon tsangwama da ake musu wanda har ta kai sun kasance tamkar jemagu a cikin al’umma. Ga dai abin da suke cewa:

  Ya mai tsare halitta mun zo ka taimake mu,
  Ka ba mu kariya kar wani ɗa ya addabe mu,
  Allahu kai katanga ta tsari ga magautanmu,
  Masu bibiyar ɓatanci ga sana’unmu,

  Mun zamma sai ka ce jemagu da iyalanmu,
  Mun zamma mujiya a cikin jinsin yarenmu,
  Suna ta cin amanar bayinka cikin hammu,
  Sun shigga innuwar al’adu addininmu,
  Allahu don isarka da mu kai kaƙ ƙage mu,
  Ka ba mu kariya don ƙaunar Abu Batulu.

  Bayan wannan babban jigo da ya shafi bayyana alfanun waƙa, akwai wasu ƙananan jigogi da suka danganci bayanin waƙa karan kanta, musamman rukunnenta. Sannan an bayyana irin baiwa da mawaƙi ke da shi musamman ta fuskar fasahar sarrafa zance. A ƙarshen waƙar kuwa, an yi amfani da wasu salailai da suka shafi rufewa. Sun haɗa da bayyana sunan mawaƙi, da bayyana ramzi da yawan baituka. Daga ƙarshe kuma an rufe da godiya ga Ubangiji da kuma ambaton tamat!

  4.0 Kammalawa

  Haƙiƙa za a iya cewa, gasar da wannan ƙungiya mai albarka ta sanya ya kasance sara ne kan gaɓa. Dalili kuwa shi ne, yayin da marubucin waƙa ya tabbatar da ɗimbin amfanin da take da shi, to sai dai ya kasance maganar da Bahaushe ke yi: “Sara da sassaƙa ba ya hana gamji toho.” Fata dai ita ce, Allah ya shiryar da marubuta waƙoƙi kan hanya madaidaiciya tare da karkata bakin alƙalummansu zuwa rubuta kalaman da suka kasance masu soyuwa a gare shi.
  [1] Kalmar fim a nan na nufin finafinan Hausa a matsayin wani ɓangare da adabin Bahaushe na zamani.
  [2] Dangace a nan na nufin sanya danga, wato katangewa.

  Popular Posts

  Popular Posts

  Popular Posts

  Pages