FASIHIYA BINTA LABARAN
(Fati Nijar Da Waƙoƙinta)
Na
Abu-Ubaida Sani
Da
Halima Daura Kabir
Da
Abdullahi Bashir
Tattara waƙoƙin fitacciyar mawaƙiya kamar Fati Nijar ba zai samu cikakken armashi ba har sai an haɗa da tarihin rayuwarta. Makaranta da manazarta da dama za su so jin tarihin mutane irinta. Bugu da ƙari, tarihin zai kasance wata makaranta ga masu karatu. Masu karatu sukan iya cin karo da bayanai ko salailan rayuwa da za su kwaikwaya a wani mataki na neman cigaba a rayuwa.
Shi kuwa tarihin
Fati Nijar za a iya kallon sa ta fuskoki guda biyu. Wannan ya shafi rayuwarta
kafin ta fara waƙa a ɓangare
guda, da kuma rayuwarta a matsayin mawaƙiya a ɗaya ɓangaren.
Tussan bayanai na farko da wannan bincike ya dogara a kansa shi ne “Waƙa a bakin mai ita.” Kayan manazartan sun tsinke a gindin
kaba inda suka shafe tsawon watanni suna tattaunawa da wadda ake rubutun a
kanta a-kai-a-kai. Bayan nan, an nazarci waɗansu
ayyuka da aka gabatar a kan mawaƙiyar a matakin
ilimi daban-daban. Sun haɗa da kundayen digiri da maƙalu da littattafai daban daban. A nan, za mu bi matakan ilimi na nazarin ƙwaƙƙwafi domin
tabbatar da ingancin bayanan da aka tattaro.
