Zamani Zo Mu Tafi: Al'adun Hausawa A Duniyar Intanet

    Tuni intanet ya zama wani ɓangaren rayuwar ‘yan’adam. A yau, ba za a iya ƙiyasin mizanin ɗumbin munanan matsalolin da za su auku ba idan aka ce babu intanet daidai da minti guda. Ɓangarorin ilimi da harsuna da dama sun rungumi alamarin intanet kain-da-nain. Hausa na ɗaya daga cikin harsunan da suke tasowa a duniyar intanet. A zuwa ƙarshen shekarar 2020, akwai a ƙalla manyan kafofin intanet na Hausa guda arba’in da huɗu (44). Lura da haka, ya zama dole a gudanar da nazarce-nazarce a wannan fanni domin daidaita al’amarin wanzuwar Hausa a duniyar intanet. Maƙasudin wannan bincike shi ne nazartar (i) yanaye-yanayen al’adun Hausawa cikin duniyar intanet da (ii) ci gaba da ƙalubalen da ke dabaibaiye da kafafen intanet na Hausa, da kuma (iii) hanyoyi da matakan amfani da intanet wajen bunƙasawa da yayata aladun Hausawa. Farfajiyar binciken ba ta wuce al’adun Hausawa da ke cikin duniyar intanet ba. An yi amfani da manyan hanyoyi biyu domin gudanar da binciken. Hanya ta farko ita ce hira. Ta biyu kuwa ita ce nazarta da ƙwanƙwance ƙunshiyar kafafen intanet kai tsaye. An yi amfani da rain Pulatoriyya (Platonism) wajen gudanar da binciken inda aka ɗauki intanet a matsayin duniya mai zaman kanta wanda kuma al’amuranta ke da alaƙa da abubuwan da ke gudana a duniyar yau da kullum. Sannan an yi amfani da hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Bahaushe cewa “zamani riga ce.” Lallai kuwa ya zama wajibi Hausawa su taka rawar kiɗan zamani domin tabbatar da wakilcinsu a duniyar intanet bai faɗa hannun waɗanda za su masa riƙon sakainar kashi ba. Binciken ya tabbatar da cewa, a yau babu wani alamari da zai iya ci gaba, ya ɗaukaka, duniya ta san shi kuma ta karɓe shi, ba tare da an haɗa da intanet ba. Har ila yau, binciken ya gano cewa, tuni al’adun Hausa suka yaɗu a duniyar intanet. Bayan haka, ya fahimci cewa akwai matsaloli da dama da ke dabaibaye da kasancewar Hausa a duniyar intanet, ciki har da matsalolin da suka shafi ƙarancin ilimin Hausar ga masu gudanar da kafafen intanet na Hausa. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da hukumomi da malamai da manazarta, da su waiwaici al’amarin Hausa a duniyar intanet domin samar da kyakkyawan wakilci.

    Duba cikakken rubutun a nan.

    Pages