Ba Su Da Direction - (A Rubuce)

   Waƙa hanya ce ta ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Amma kash! Idan aka yi la'akari da waƙoƙin Hausa na zamani a yau musamman waɗanda matasa suke ribibin karkata gare su, sai a tarar babu wani ilimantarwa ko faɗakarwa da suke yi. Kai, sam ma "Ba Su Da Direction!"

  Da fari na sako Rab Sarkin creation
  Wanda ke halitta ya sanya mata motion
  A zuciya ya sa feelings ya ƙaro da emotion,
  Ya sanyo sense organs domin sensation,
  Ga reflex action, jiki ya yo reaction. 

  Don ya nuna mun gaza muke excretion,
  Su kam ga 'yan uwanmu har da menstruation,
  Ya wanzar da rayuwa ya ƙaddara extinction,
  Ko ban mun gushe akwai ran resurrection.

  Yi salati gun Rasulu ƙaro salvation,
  Sa da iyalansa har sahabu in addition,
  Da wanda kan tafarkinsa ne mu kai retention. 

  'Yar magana zan faɗa ina son attention,
  Sai an bar motion ko duk locomotion,
  An ba ni hankali da full concentration. 

  Mawaƙan zamani ku biyo ni cikin caution,
  Allah ya yo mu daban-daban da faction,
  Waɗansu na invention ko su tsara fiction,
  Waɗansu ba ƙwaƙwalar yin imagination. 

  Baiwa ce an ka ba ku mai kuma limitation,
  A kan ku bi turbar ƙwarai sai ku kai divination,
  To ku san ko waƙar an fi ku ideation,
  An fi ku tsara baituka da kai information,
  An fi ku a hangen nesa miƙaƙƙen perception,
  An fi ku ko style balle a fagen diction,
  Kalamanku kaɗan ne kamar an sa ration. 

  Ba ku da tsarin ƙwarai, ba organization,
  Ba hikimar zance da za ku yi oration,
  Duk batunku maimaici babu variation, 

  Kun ƙware ne kawai a shiga da ke seduction,
  Shigar haram ta batsa wai don attraction,
  Mata su tsuke ƙugu su sasshafo lotion,
  Su zo suna fitsara wai sun iya action,
  Su rinƙa gantsaro ƙirji don ku san ovation,
  Sai kiɗda bin sa ne zuci ke corruption.

  Ba kwa research balle investigation,
  Batunku babu illimi ko sabon notion,
  Ba kwa sanar da mu tarihin nation,
  Ba kwa taimako a fannin education,
  Ba ku gane kun gaza sai a competition. 

  Kai Hausa hip-hop, ku zo ku amsa question,
  “Da so samu ne” bara in yo quotation,
  Wane saƙo ya isar, mene intention?
  To a cikin “Chass”, me za ai emulation?
  Ko “a ƙame ƙam”? Mata ke imitation. 

  Matsalar constitution ba wani regulation,
  Sai ku ɓata tarbiyya gare ku ba conviction,
  In baicin haka da yanzu ba ku function,
  Kun cancanci kora total expulsion,
  Kowane nation gare ku ai ejection,
  A bi ku ma da eho bayan eviction.

  Ko ba komai cikinku da exception,
  Kai Aku Mai Magana congratulation,
  Kana batu na hankali kana kawo motion,
  Kana so a yi gyara kana orientation,
  Kakan nuno issues sannan ka yo suggestion,
  Kakan taɓa har leaders domin su yo correction,
  Da kamarka duk ake ba wani contention.

  Gare ku ‘yar nasiha ku kau da opposition,
  Ai muna da deen da ya zo da regulation,
  Mu tittina ayoyi da akka yi revelation,
  Ga ko nan hadisai an yo narration,
  Akwai wuta da janna, an bar mana option,
  Mu daina biye duniya akwai implication,
  Kamar yau za mu gushe kan realization,
  ɗebe mu sai kabari end of discussion,
  Za mu amsa tambaya tough examination,
  In mun ci mun haye, mu samu ventilation.
  In kuwa mun gaza highest frustration.

  In za ku yo waƙa to ku samu vision,
  A ce akwai intention a ce kuna da mission,
  Baitukan ku bayar domin observation,
  Akwai massana, ku yo consultation,
  Duk baitukan sai su sam purification,
  Har mutan ƙwarai za su yo appreciation.

  Allah taimaka mu yi preparation,
  Guzzuri na taqwa aya ta yi mention,
  Mu kauce ruɗin sheɗan ko manipulation,
  Ka sa mu a aljanna mu samu relaxation.

  A za a iya sauraren sautin waƙar a nan.

  Pages