Ranar Ƙin Dillanci

   Ranar Ƙin Dillanci

  Motar da nake ciki baƙaƙen gilasai gare ta waɗanda ake yi wa kirari da fa’illan takun tarahu... Gaba tsaro, baya tsaro... Kai! Mulki da daɗi!

  Atishawar da na yi ta katse mini tunani. “Yarhamakalla ranka ya daɗe.” Mai tuƙa ni ya faɗa duk da ban ambaci komai ba. Na ci gaba da kallon talakawa da ke gefen hanya. Wasu na faɗin: “Sai ka yi takwas...” Wasu na cewa: “Ba ma yi...!” Jami’an tsaro kuwa na famar musu korar kare. “Htch” na sake. “Kai! A wannan lokacin korona?” Na raya a zuciyata. Na daidaita zaman takunkumin da ke fuskata.

  “Htch! Htch! Htch!” Daga jeranton atishawa sai na ɓarke da tari mai tsanani. Cikin gaggawa ɗan sandan da ke zaune gefen mai zaman banza ya sadar zuwa sauran motocin da ke cikin taragon rakiyata: “Honorable is in unsual situation. Do you copy?

  Idanuwana suka daina kallon komai sai wasu baƙaƙen halittu masu jajayen idanuwa mai kama da garwashi. Gabana ya ba da ras! Ɗayansu ya daka mini tsawa: “Ciro rayinka da kanka!” Sautin muryar ya fi rugugin araduNan na ji wani abin da ba zan iya fasalta shi ba. Tamkar dai duka jijiyoyin jikina sun tsittsinke. Kowane ƙofar gashin jikina kuma kamar an soka allura.

  Mutanen nan suka matso. Kowannensu yana hucin wuta mai tsananin zafi. Suka fara tsintar wani farin abu da ya warwatse a jikina. Ciran kowane ɗayansu ya fi yankan wuƙa zafi. Na fara buge-buge da wafce-wafce. Na jiƙe wandona da fitsari.

  Ban sani ba ashe mun iso gidan gwamnati. Likitocina na kewaye da ni yayin da ake ta rirriƙe ni. Sai dai ina... ƙaddara ta riga fata. Kafin a yi wani yunƙuri na ce ga garinku nan! Wai korona ce ta kashe ni, don haka ba za a mini wanka ba.

  Baƙaƙen mutanen suka nufi sama da farin abin da suka tsittsince a jikina bayan sun lulluɓe da wani bargo baƙi mai zafi da ƙayoyi. Can sai ga su sun dawo da abin dai riƙe hannuwansu. Sai ga ƙasa ta buɗe. Suka luluƙa ciki da shi.

  ***

  Yanzu kam ba na iya motsi, amma ina jin duk maganganu da ake yi kusa da ni. Ga mamakina, kowa sai ya fara baya-baya da ni. Ko mai tuƙa ni a mota da yake ɗan ga-ni-kashe-ni gare ni, sai ya ja baya. Amma ba damuwa... Na san ko da waɗannan sun ƙi ni, matana da ‘ya’yana ba za su ƙi ni ba, musamman amaryata Zee.

  Kafin in gama tunani kuwa sai ga su. Daga nesa suka tsaya. Uwar gidata tana ta faman share hawaye. Zee kuwa, kamar ba ta damu ba. Ta zaro wayarta ta ɗauki hotona daga nesa. Wani likita da ke kusa da su ya ce: “Hajiya za ku iya tafiya. Kun san yanayin wannan cuta...” Ba musu suka juya suka nufi hanyar fita. Na yi mamaki! Zee ba ke ce kika ce za ki so ni rai da mutuwa ba? Amma ko na tambaya ba ta ji na. Wayyo ni! Kowa na gudun taɓa ni tamkar wata annoba. Waɗanda za su saka ni a leda sai da suka yi wata shiga kamar doduna. Aka tsattsaya a tazara aka mini salla. Aka doshi maƙabrta da ni. Hankalina ya ƙara tashi.

  ***

  Na hango kabarin da aka tona. Wuta ce ke ci a ciki tamkar gobarar daji. Na fara kururuwa. Duk da haka ba sa ji na. Ba dama in yi motsi. Da aka matso kusa, na hango macizai da kunamai a ciki. Tsananin tashin hankali ya sa na fara tunanin halayyana tun daga yarinta har zuwa yau. Sai yanzu na gane annabi-ya-faku. Yau ne kaɗai na yarda da cewa ƙarshen alewa ƙasa. Aikina na ƙarshe yaudara ce. Na tuna kalamaina na ƙarshe ga talakawa: “Mun fitar da maƙudan kuɗi domin yaƙi da korona...” A haƙiƙanin gaskiya kuwa kwarona farin ciki muka yi da zuwanta. Dalili shi ne ta samar mana da hanyar ƙafar ungulu da kuɗaɗe cikin ruwan sanyi.

  Na tuna adadin dukiyata. Ni da kaina abin ya ba ni takaici. Na kasa gane da ko ni wawa ne ko mahaukaci? Haƙiƙa dukiyata ta kai in ci da mutane ɗari na tsawon shekaru ɗari. Kash! Ban yi aikin neman lada da ita ba sai ma ƙoƙarin neman ƙari da nake yi. Wai me ya toshe min ƙwaƙalwa ne? Lallai ko “duniya mai idanu a tsakar ka.” Ko ba komai dai na san iyalaina za su yi ta sadaka da ita da sunana. Ladan zai biyo ni kabari.

  Na ci gaba da kururwa yayin da balbalin bala’in da ke fita daga ciki ya fara bugna. Su ba sa kallon komai. Suka turbuɗe ni. Suka watse. Kabari kuwa ya matse ni. Na ji wani tashin hankalin da ya fi ƙarfin tunani. A nan na tuno da dukkanin labaran da nake ji game da rayuwa bayan mutuwa. Kaico! Da-na-sani ƙeya ce!

  ***

  Wani baƙin mutum mai ban firgici riƙe da ƙatuwar guduma ya bayyana tare da wata ƙara mai rikitarwa. Ya tambaye ni cikin murya mai kaushi: “Wane ne Ubangijinka?” Ruɗewa da razana suka ɗauke duk wani sani nawa. Ya danƙara mini gudumar hannunsa sai da na nutse cikin ƙasa. Ƙasa kuwa ta watso ni waje... Ashe da gaske ne a lahira ba a mutuwa.

  ***

  Yau a matsayin fatalwa na fito. Kai tsaye na nufi gidana, wato gidan gwamnati. Burina shi ne in ga me ya dakatar da iyalaina ba su fara sadaka da dukiyata ba ko zan samu sauƙi? Na wuce ta babban ɗakin taron da ke gefen gidan gwamnati. Na tuna lokutan da aka yi ta gayyata na tarurrukan gwangwajewa. Ina ma a ce zan iya musu wa’azi?

  Na ɗan leƙa ɗakin taron. A dandamalin da ke sama sai ga babban ɗana Abba da yarinyar nan da na hana shi aura. Suna taka rawa ana musu yayyafin kuɗi. Kamar in je in tsinke shi da mari, sai kuma na tuna ni fatalwa ce. Cikin takaici na ƙarasa gidan gwamnati. Na dudduba amma iyalaina ba sa nan. Sati biyu kacal ashe har an maye gurbina! Na kuwa gane wanda aka sanya. Wani tsohon abokin gabana ne da ake kira Alhaji Nera.

  Alhaji Nera na tare da wata mata cikin ɗakin hutu. Na kunna kai ciki domin kallon ƙwaƙwaf. Me zan gani? Matata ce Zee ke kishingiɗe gefen Alhaji Nera. “Kai shege ne.” Ta faɗa yayin da ta ba shi hannu suka tafa cikin shewa. Ta ci gaba da magana: “Ka ga dabarar nan ta yi. Ko wa dai ya san koronar ce ta kashe shi. Amma babu wanda zai yi tunanin ina ya same ta. Ni da kaina na sanya masa takunkumin a fuska lokacin da zai fita.” Ta ja numfashi.

  “Hmm...” Alhaji ya katse ta: “Yanzu dai ba wannan ba... kin san dai gadonsa ina da Kaso talatin. Rayuwa kuwa za mu ci gaba kamar yadda muka fara da ke...” “Wallahi Alhaji ka cika zalama.” Ta katse shi. Suka sake tafawa cikin shewa... Ashe da matata aka haɗa baki aka ga bayana? Banza ba ta kai zomo kasuwa. Da ma na san da walakin goro a miya. Ba don kuɗina ba kaɗai take zaƙewa a soyayyata.

  ***

  A sabon gidan da uwargidata ta saya na sake tarar da sabon tashin hankali. Ɗakin yana cike da mata yara da manya. Na gane fuskokin mafi yawa daga cikinsu. Su ne uwargidan tawa ta sha fama da ni kan in bi musu hakkinsu game da mutuncinsu da aka ci ta hanyar fyaɗe. Ta daɗe tana bi na domin mayar da hankali kan fitar da doka ta musamman game da fyaɗen. A lokacin ba shi ne a gabana ba. Idan jifa ta wuce kaina, to ta faɗa kan uban kowa. Wasu daga cikin waɗanda aka yi wa fyaɗen, baƙin ciki ne ya kashe su.

  Ina shiga ɗakin wasu daga cikinsu suka taso. Ashe su ma fatalwowi ne. Na yi ƙoƙarin fita da gudu. Suka kama hannuna na dama. Cikin firgici da gigicewa na fara ƙoƙarin ƙwacewa. Kowacce daga cikinsu na ƙorarin mini magana:

  “Alhaji lafiya?”

  “Alhaji”

  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”

  “Alhaji lafiya?”

  A hankali sai na ji muryoyinsu na juyewa suna komawa irin na uwargidata.

  ***

  Firgigit! Na farka daga bacci. Tana riƙe da hannun nawa tana mini nasiha kamar yadda ta saba. Duk da yanayin sanyin ɗakin, na jiƙe shirgif da gumi. Da sauƙowana daga gado na yi sujada don gode wa Allah da ya nuna mini gaskiya tsirararta. Na ji tamkar na mutu ne da gaske na dawo. To ai gani ga wane ma ya ishi wane tsoron Allah ballantana ni da na ga zahiri.

  Na kira mai tsara mini rubuce-rubuce. Na karanta jawabin da ya rubuta mini game da kuɗin korona. Na yi ajiyar zuciya. Na dube shi na ce: “Ka je ka tsara mini jawabin da zan gabatar wa ‘yan majalisu da kwamishinonina. Ƙumshiyar jawabin ya kasance wa’azi ne. Takensa kuwa ya zamto cewa mu ji tsoron Allah, domin akwai ranar ƙin dillanci.

  author/Sani, A-U., Usman, U. Yahaya, S.

  journal/Short Creative Story

  pdf-abu-ubaida.com


  paper-abu-ubaida.com

  Pages