Fasihi Da Ya Yi Fice (Alhaji Aminu Ladan Abubakar, ALA)

  Bahaushe na cewa: “Idan ka ji wane ba banza ba!” Duk da cewa ‘yan waɗandan baitoci sun kasance ɗaukani ne kawai game da rayuwar ALA, hakan bai hana su zama wani madubi ba wanda daga cikinsa ana iya hango hoton rayuwarsa a dunƙule. Basirar da Ubangiji ya huwace masa kuwa, tuni ya duƙufa wurin sarrafa ta. Ruwan alƙalaminsa bai daina zuba ba, haka ma ƙararrawar bakinsa ba ta daina kaɗawa ba. A bisa haka ne wannan takarda ke ba da shawarar cewa, a samu wani yunƙuri na musamman domin gudanar da nazarce-nazarce (bayan waɗanda ake yi a makarantu) dangane da waƙoƙin ALA. Hakan zai ba da damar cin gajiyar hikimomin da ke ƙunshe cikinsu, da kuma adana waƙoƙin domin ‘yan gobe.

  aminu ladan abubakar ala
  A farko Ilahu da ke sa ai fice,
  Allah wanda shi ke raba dace,
  A yau niyyata na tsaftace,
  A nan wurinka naf fake neman dace. 

  Mai sama ilimi baiwarka ce,
  Mutum yakan yi hankali ko haukace,    
  Mai duka ji ma niyyarka ce,
  Muddin ka so to sai a kurumce. 

  Ilahu mai gani duk kai ka amince,
  Idan ko ka ga dama sai ya makance,
  Ilahu ko ɗanɗano sai ka amince,
  Idan a yau ka so komai ya sallace. 

  Na aminta arziki bayarwarka ce,
  Na sani kai kake sa a talauce,
  Nittsuwa da fikkira baiwarka ce,
  Nufinka ne ɗan Adam yag gal-galce. 

  Ubangiji sallu ala wanda yai fice,
  Uban Alƙasim da kaa amince,
  Umumi[1] ahlih was sahabi jimlace,
  Ubangiji da duk mabbiyansu jimlace.

  Labari gare ni wanda na tantance,
  Labadiya[2] a dena a zo a ji zance,
  Lallebiyo[3] tsayar taho a urince[4]
  Lafshaka[5] ku samu ku bi shi nitsance. 

  Alƙalam na ɗauka niyya na tsaftace,
  A yau tarihi ne zan yi jerance,
  A kan rayuwar fasihi da yai fice,
  A gaskiya, ilmi da ma a mutunce.

  Da farko Talata ran biyu ga wata ce,
  Da ɗai goma ga watan nineteen ce,
  Daɗo seventy-three haɗa su jimlace,
  Da ɗai haihuwar Ala kun ji kammalce. 

  A Yakasai haihuwarsa ta kasance,
  A Kanon Dabo babban birni fitacce,
  Allo a rubuta tsaf a hardace,
  A ƙarƙashin Malam Tudu yai fice.         

  Nan Tudu na Murtala Primary ce,
  Nineteen eighty-six ya kasance,
  Nineteen ninety-two ya kammalce,
  Nan Kano Dakata Secondary ce. 

  A nineteen eighty-six ya zarce,
  A Dakata ninety-two ya kammalce,
  A two thousand three zo ka ji zance,
  A School of Technology ya kasance. 

  Birnin Kanon Dabo can ya kasance,
  Bakin twenty-seven ya kammalce,
  Ɓangaren design nan ya gwanance,
  Bayan ɗimbin karance-karance.

  Ubangiji yai masa baiwa ta fice,
  Ubangiji ya azurta shi da dace,
  Ussi[6]ko domin shi ya kasance,
  Ubangiji ya kama dare da maraice. 

  Batu na aure kuwa tuni ya cikkace,
  Baiwar ‘ya’ya garai ya azurce,
  Banuna wal banatun akwai su jimlace,
  Bagire na ilmi sunka kasance. 

  Ala a waƙa tuni ya yi fice,
  A nahiya ta Hausa ba a kwatance,
  A jamo’o’in ƙasa ana ta bincike,
  Ayyukansa libraries sun kundance.

  Karamci, mutunci, zuci tsaftace,
  Kamili, fasihi, gwani da yai fice,
  Karsashi, kamala ga manyance,
  Kana da kyan hali kawai a taƙaice. 

  Ai masu gulma kanka sun kunyance,
  A yau masu hassadarka sun layince,
  Af! Masu ƙin ka duk sun lamunce,
  A ƙarshe masu ƙorafi sun amince. 

  Rabbi duniya Ala ya buga dace,
  Rabbana a lahira ka sanya ya dace,
  Rattabin Abu-Ubaida ɗan Sani ce,
  Ramzi MATISHA take a ƙidance.  [1] Wannan kalmar tana da ma’anar: “Gaba ɗaya”, ko “haɗuwar ra’ayi.”

  [2] Wannan Kalmar tana da ma’anar yawon banza.

  [3] Wannan kalmar tana da ma’anar wata wasa da yara suke yi a ruwa. A wasu wurare akan kira wasan da laɓi ko lebi ko a-kori-kada kokuma labis.

  [4] Wannan kalmar tana da ma’anar azalzala ko ƙagauta.

  [5] Wannan kalmar tana da ma’anar: “inuwa mai sanyi.”

  [6] Kalma ce wadda take daidai da kalmar “dalili.”


  author/Sani, A-U.

  journal/Peom
  pdf-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI

  paper-https://youtu.be/bHVaNFCfQuI  Pages