Zamantakewar Hausawa Jiya Da Yau

    Citation: Shehu, M. & Sani, A-U. (2018). Zamantakewar Hausawa Jiya da Yau. In Zulyadaini, B. et el (eds) Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol 6. Pp 274-284. ISSN 2449-0660.


    Zamantakewar Hausawa Jiya Da Yau


    Na 

    Musa SHEHU
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
    0703 131 9454


    Da
    Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures
    Federal University Gusau, Zamfara
    Phone No: 08133529736
      

    Tsakure

    Hausawa kan ce wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba. Haƙiƙa zamantakewar Hausawa a da ta kasance gwanin ban sha’awa. A da, Hausawa sun kasance suna zama ne na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Wannan ne ma ya sanya tsarin muhallin Bahaushe a da bai kasance ramin-kura ba, daga ke sai ‘ya’yanki. A maimakon haka, yakan zauna ne a gida na gandu. Hausawa kan ci abinci tare, su yi aiyuka da tarurruka a tare, da ma dukkan sauran al’amuran yau da kullum. Hakan ya sa duk wanda ya shiga matsala, abin yakan zo da sauƙi domin kuwa ‘yan uwa da abokai da sauran makusanta za su tsaya tsayin daka su ga an shawo kan matsalar. Abin sai dai a ce Allah san barka. Kash! Sannu a hankali an wayi gari wannan tsarin zamantakewa na dusashewa. Tausayin juna da taimakon juna da zumunci da zaman lafiya duk sun ja baya. Son kai da hasada da gaba sun fara maye gurbin zaman lumana da taimakekeniya da aka san Bahaushe da su a da. Wannan takarda tana ɗauke da bitar irin kyakkyawar tsarin zamantakewar Bahaushe ta asali da kuma yadda zamantakewar ke taɓarɓarewa a yau. Sannan daga ƙarshe takardar ta kawo hanyoyin da za su iya taimakawa wajen ɗinke waɗannan ɓaraka da ake samu.

    1.0 Gabatarwa

              Zamantakewa a kowace irin al’umma gona ce mai faɗin gaske, sai dai a yau ana iya cewa, haki na ƙoƙarin yi mata barazana na hana yabanya walwala. Haƙiƙa al’ummar Hausawa sun kasance masu kyakkyawar zamantakewa a tsakanin junansu. Gaskiya da riƙon amana da shi suke kwana suke tashi. Haƙuri da taimakon juna ya zama musu ruwan sha a ji sanyin rayuwa. Biyayya ga magabata da tausaya wa talakawa ga shugabanni ya zama ruwan dare game duniya. Sai dai kuma wannan kyakkyawar zama yana neman taɓarɓarewa a wannan zamani. Saboda haka, manufar da wannan maƙala ita ce, fito da tsarin zamantakewar Hausawa a jiya, da kuma yadda zamantakewar ke ƙoƙarin sukurkucewa a yau. Taɓarɓarewar zamantakewar na da nasaba da rashin gaskiya da riƙon amana da kuma kwaikwayon baƙin al’adu musamman daga finafinai (Al-kanawy, 2000; Ali, 2004; Kiyawa, 2013). A yau, taimakon juna da biyayya ga magabata, da tausaya wa talakawa daga shugabanni, da haƙuri da juna yana neman ya zama tarihi. Ga dai al’amurran nan suna ƙoƙarin taɓarɓarewa a rayuwar Hausawa a yau.
    2.0 Yanayin Zamantakewar Hausawa a Jiya
                Tarihi ya nuna al’umma takan kafu ne a sakamakon wata yarjejeniya tsakanin wasu mutane waɗanda suka taru suka amince da kare kansu daga wasu abubuwan ban tsoro, ko hare-haren abokan gaba, ko namun daji, ko kuma su sauƙaƙa wa kansu wasu wahalolin duniya (Mar, a cikin Gusau 1999). Irin wannan zama na yarjejeniya yakan kawo sahihin haɗin kai da yarda da juna, sannan da taimakon juna. A irin wannan yarjejeniyar zama aka sami wasu mutane daga ƙabilu daban-daban suka haɗa ƙarfi suka samar da al’ummar Hausawa, masu ma’amala da harshe ɗaya wato harshen Hausa, tare da samun daidatuwa ta wajen fannin ɗabi’unsu da al’adunsu da muhallinsu da sauran kayayyakin ayyukansu duk sun zama fanni ɗaya (Gusau, 1999).
                Hausawa tun farko mutane ne da suka tashi da taimako da son juna, da ladabi da biyayya, da tsare gaskiya da riƙon amana, da aikata ɗa’a da tsare haƙƙin shugabanci da maƙwabtaka da sadar da zumunci, da tausayi da sanin ya kamata, da sauran ayyukan alheri iri daban-daban. Kuma su mutane ne masu matuƙar karimci da saurin amincewa da wasu mutane, wato baƙi. Sannan ga sakin fuska da shimfiɗar fuska wadda ake cewa ta fi shimfiɗar tabarma. Mutane ne masu kyakkyawan zamantakewa tsakaninsu da ma sauran baƙi masu shigowa (Bunza, 2012; Maikadara, 2012). Duk da yake cewa, mun san akwai wasu halaye da ɗabi’u munana da ake aikatawa tun wancan lokaci na farkon rayuwar Hausawa, domin Hausawa na cewa, mutum duka ɗan tara ne bai cika goma ba.  A kan haka, za a iya kallon zamantakewar Hausawa zuwa waɗannan rukunnai:
    2.1 Zamantakewa Tsakanin Maƙwabta
                Gusau (1999) ya bayyana cewa, maƙwabtaka ita ce zama wuri guda da mutum dangane da sana’a ko wurin zama. Ba shakka, akwai kyakkyawan zama da ƙaunar juna tsakanin maƙwabci da maƙwabci. Idan wani abin farin ciki ya sami maƙwabci kamar harkar aure ko suna, yakan shaida wa maƙwabcinsa don a taru a yi murna. Haka zalika, idan abin baƙin ciki ne ya samu akan haɗu a jajanta wa juna. Sukan kuma taimaka wa junansu idan wata hidima ta samu domin a rufa wa juna asiri. Maƙwabcin Bahaushe tamkar ɗan’uwansa ne, ya san samu ko rashin maƙwabcinsa. Haka ma ya san farin ciki ko baƙin cikin maƙwabcinsa. Bugu da ƙari, zamantakewar ba ta tsaya a nan ba, galibi idan dare ya yi magidanta sun dawo gida, maƙwabta sukan fito da abincin dare daga gidajensu a zauna a ci tare ana tattauna lamurran da suka shafi rayuwar duniya. Ziyarar mara lafiya, da zuwa jaje ga wanda wani abu na baƙin ciki ya sama, da saƙonnin taya murna, duk Hausawa na gudanar da su ga maƙwabtansu na jini da na zaman unguwa ko gari ko sana’a, saboda ba da haƙuri da nuna tausayawa da taya murna. Idan wani rikici ya ɓarke tsakanin maƙwabta, akan haɗu a tattauna a yi sulhu don samun masalaha.
    Irin wannan kyakkyawar zamantakewa da aka zayyana a sama ita ta sanya aka samu karin maganganun Hausawa daɗanda ke nuni game da zamantakewa ta gari. Sun haɗa da:
    i.                    Mahaƙurci mawadaci
    ii.                  Haƙuri shi ne ribar rayuwa
    iii.                Idan da hali muni kyawo ne
    iv.                Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza
    v.                  Maci amana yana tare da kunya
    vi.                Ɗa na kowa ne
    vii.              Zaman duniya cuɗeni in cuɗe ka
    viii.            Zaman duniya kamar rumbu ne miƙo man in miƙo maka (Ɗanyaya, 2007; Koko, 2011, Malumfashi da Nahuɗe, 2014).
    2.2 Zamantakewa Tsakanin ‘Yan’uwa
              Zamantakewa tsakanin ‘yan’uwa na jini kamar ta maƙwabci da maƙwabci ce. Babu nuna bambanci tsakanin ‘yan’uba. Iyaye mata ko kishiyoyi ba sa nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu. A wani lokaci ma yaro bai gane mahaifiyarsa sai idan ya girma. ‘Yan’uwa kan yawaita sadar da zumunci tsakaninsu ta hanyar ziyartar juna daga lokaci zuwa lokaci. Kamar maƙwabta, su ma ‘ya’uwa kan taru domin taya juna murna ko farin ciki idan wani buki ya samu. ‘Yan’uwa kan yi iya ƙoƙarinsu don ganin ɗan’uwa bai ji kunya ba. Babu yaudara ko cin amana tsakanin ‘yan’uwa. Idan iyayen yara suka rasu, ‘yan’uwa kan ɗauke su suna kulawa da su tamkar su suka haife su ta yadda rayuwarsu za ta inganta ba tare da sun tagayyara ba. Idan wata rashin lafiya ta sami ɗan’uwa, babu maganar ƙyama, ‘yan’uwansa na kusa da ma na nesa kowa yakan kawo tasa gudummuwa domin ganin wannan ɗan’uwa ya sami cikakkiyar lafiya (Gumel, 1999; Maikada, 2012).
    2.3 Zamantakewa Tsakanin Masu Mulki da Talakawa
                Haƙiƙa akwai kyakkyawar zamantakewa ta fahimtar juna a tsakanin masu mulki ko sarakuna da talakawansu. Abin da aka sani tun can azal a rayuwar Hausawa, sarki ko shugaba mutum ne wanda a koyaushe yake ƙoƙarin tsare mutuncin sarautarsa ko shugabancinsa ta hanyar riƙe talakawansa da kyawo, ya ɗora su kan tafarki madaidaici wanda zai amfani rayuwarsu. Yakan sa ido ya ga cewa, zalunci da cin amana da rashin gaskiya ko yaudara bai wanzu tsakanin talakawansa ba. Yakan kare mutuncinsu ga dukkan wani abu da zai kawo tarnaƙi ga rayuwarsu. Shugabanni kan sa ido ga baƙi masu shigowa cikin gari don gudun saukar da ɓara-gurbi. Haka ma a ɓangaren talakawa, akwai ɗa’a da ladabi da biyayya zuwa ga shugabanni. Sukan kuma taimake su wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa da kawo arziki da wadata a cikin ƙasa. Haka kuma sarakuna sukan nemi shawarar talakawansu a cikin al’amurra daban-daban domin tabbatar da adalci ga jama’arsu.

    2.4 Zamantakewa Tsakanin Malamai da Ɗalibai
                Malamai dai a cikin kowace al’umma su ne masu ilmantar da jama’a maza da mata, yara da manya sanin hanyoyin rayuwa tagari, da koya musu halaye masu nagarta, da nuna musu munanan halaye don su kauce wa faɗawa a ciki. Sannan su ilmantar da mutane ilimin addini da na zamani wanda zai shiryar da su zuwa ga rayuwar duniya da na gobe. Malami shi ne mai koya wa yara ƙima da girmama iyayensu, da yadda za su yi musu ɗa’a da biyayya, da kuma yadda za su yi kyakkyawar hulɗa da sauran jama’a. Su kuwa ɗalibai suna matuƙar girmama malamansu da yi musu ɗa’a da biyayya da kauce wa duk wani abu da zai sosa rayuwarsu. Sukan kuma ƙudurta kyakkyawar niyya game da malamansu. Ba su cin zarafin malamai ko yi da su, balle ma a gabansu. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take gudana tsakanin malamai da ɗalibansu. Bugu da ƙari, ko da ilimin zamani ya shigo ƙasar Hausa aka fara samun malamai da ɗalibai ‘yan ƙasa, wannan kyakkyawan tsarin zamantakewa tsakanin malaman zamani da ɗalibansu bai sauya ba. Gumel, (1999) da Bunza, (2012) sun nuna cewa, a wancan lokaci, malaman sukan ɗauki ɗaliban kamar ‘ya’yansu na cikinsu. Haka su ma ɗaliban sukan yi wa malaman ladabi tamakar iyayen da suka haife su. Akwai girmamawa da tsare haƙƙin juna tsakaninsu.
    2.5 Zamantakewa Tsakanin Mawadata da Talakawa
                Masu iya magana na cewa, kowa am mutum mutane ash shi. Zamantakewa tsakanin mai shi da mara shi abu ne gwanin ban sha’awa a ƙasar Hausa. Mawadata ba su walaƙanta talakawa, hasali ma sukan jawo su ga jiki domin su ma su sami albarkar dukiyar. A wasu lokuta, mawadata sukan rarraba wa talakawa jarin da za su gudanar da kasuwanci domin kowanensu ya amfana. Idan wata lalura ta sami talaka wanda ya shafi aure ko suna da makamantansu, talaka yakan kai kukarsa ga masu shi kuma a share masa hawaye gwargwadon iko. Su kuwa talakawa sukan kasance masu ɗa’a da biyayya da gaskiya da riƙon amanar dukiyar da masu shi suka damƙa masu. Idan wata hidima ta samu mai shi, za ka tarar talakawa sun taru a ƙofar gidan mai shi don su taya shi murna idan abin farin ciki ne. Idan kuma akasin farin ciki ne ya auku, nan ma talakawan sukan taru domin taya shi juyayi da jajanta masa. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take tsakanin masu arziki da talakawa a ƙasar Hausa, sai dai ɗan abin da ba a rasa ba na saɓani na yau da gobe. Da ma Hausawa na cewa, mutum duka ɗan tara ne bai cika goma ba.
    2.6 Zamantakewa Tsakanin Ma’aurata
              Haƙiƙa akwai kyakkyawar yanayin zamantakewa tsakanin miji da matarsa a ƙasar Hausa. Miji yakan yi iya ƙoƙarinsa na ganin ya tsare haƙƙin matarsa da ke bisa kansa. Yakan kula da ci da sha da lafiyar matarsa da sauran lalurorin yau da kullum gwargwadon hali. Yakan kauce ma wasu munanan halaye na cin zarafi ga matarsa ko waɗanda al’ada ba ta amince da su ba. Bugu da ƙari, miji kan sa hannu wajen tarbiyyantar da yaran da suka haifa don ganin sun rayu bisa turba tagari da yanayin zamantakewar duniya. Ita ma matar takan yi ƙoƙarin tsare haƙƙin mijinta da ya rataya a wuyanta (Bugaje, 2013). Takan kasance mai ɗa’a da biyayya ga miji da rashin ƙetare iyakokinsa. Ita ce mai kula da harkokin gida na yau da gobe, da tsaftar yara da ba su tarbiyya tagari. Mace kan yi haƙuri da mijinta da tausaya masa game da harkokin rayuwa (CCF, 2009; Sani da Abdullahi, 2016). Idan wata matsala ta shiga a tsakaninsu, sukan taushe zuciyarsu ga hana aikata ɗanyen hukunci. Wannan ne ya sa yawaitar sakin aure bai samu gindin zama a tsakanin Hausawa ba. Haƙuri kusan shi ne jigon zamantakewar mata da miji, tare da bai wa juna shawara don samun mafita a rayuwa (Gada, 2014). Sai dai akwai masana da manazarta da suke ganin cewa, tun asali da ma Bahaushe mai yawan sakin aure ne.
    2.7 Zamantakewa Tsakanin Iyaye da ‘Ya’yansu
              A koyaushe burin mahaifa ko uwaye bai wuce ganin ‘ya’yansu sun tashi cikin halaye masu kyau da nagarta. Saboda haka suke koya musu ɗa’a da ladabi da biyayya da bin kyakkyawar turba don su ribanci rayuwarsu, al’umma ma ta amfana da su. Uwaye sukan sanya yaransu makaranta irin ta addinin musulunci da ta zamani. Sukan nuna musu muhimmancin gaskiya da riƙon amana domin aiki da su. Sa’annan kuma da illar ƙarya da cin amana domin su kauce musu. Sukan kuma nuna musu amfanin zumunci da ‘yan uwantaka ta hanyar yawaita aikensu a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki. Akan koya musu sanin darajar mutane da girmama su, ba wai sai iyayensu kawai ba. Saboda haka ne ‘ya’ya sukan kasance masu biyayya da jinƙan iyayensu tun suna yara har zuwa girmansu (Bunza, 2012).
                A taƙaice, ana iya kallon yanayin zamantakewar Hausawa a jiya da wasu kyawawan abubuwa da al’ada da addini suka amince da su da kuma masu aikata su.
                        i.             Gaskiya da riƙon amana
                      ii.             Zumunci da ziyartar ‘yan’uwa
                    iii.            Tsare haƙƙin maƙwabtaka
                    iv.            Taimako da tausaya wa juna
                      v.             Ladabi da biyayya ga shugabanni
                    vi.             Girmama na gaba
                  vii.            Adalcin shugabanni ga talakawa
                viii.            Tsare haƙƙin talakawa ga masu mulki
                    ix.            Haƙuri da yafe wa juna
    Duk da cewa har yau akan samu waɗannan al’adu masu kyau wurin Hausawa, sai dai abin ba kamar yadda yake da ba.
    3.0 Taɓarɓarewar Zamantakewar Hausawa a Yau
              Sanin kowa ne cewa, matsayin zamantakewar Hausawa ya kai inda ya kai a yau. Kyakkyawar tsarin zamantakewa da aka sani ga Hausawa a da, a yanzu ya ɗauki sabon salo na koma baya. Kusan kowane rukunin tsarin zamantakewar Hausawa da aka ambata a baya, an sami taɓarwarewarsa a yau.
                Kyakkyawar zamantakewa da ke tsakanin maƙwabta a da, ya fara yin nisa a yau. Sau da yawa za ka iske ba a ga-maciji tsakanin maƙwabci da maƙwabci, kowa ya kama mai fisshe shi. Maganar maƙwabta su haɗu kowa ya fito da abinci a ci tare ya zama tarihi a yau, kowa ya yi gabansa. Sai maƙwabta su share mako ɗaya ba su yi ido huɗu da juna ba balle a yi maganar gaisawa, sai dai idan an yi kiciɓis da juna a bisa hanya. Hatta ‘ya’yan maƙwabtan da suke  haɗuwa musamman da dare domin gudanar da wasanni, ya sha ruwa a yau, kowane maigida ya ja babbar ƙofa ya rufe ‘ya’yansa a cikin gida. Maƙwabci bai san halin da maƙwabcinsa yake ciki ba, na farin ciki ko akasinsa, balle su taimaka wa juna da shawara wajen samun maslaha a rayuwa.  Sau da yawa za ka iske maƙwabta na ta husuma a kan iyakokin gida ko haraba har zuwa wajen masu shari’a. Ga dai al’amurra nan sun cakuɗe sai dai Allah ya gyara.
                Shi kuwa harkar zamantakewa tsakanin ‘yan’uwa a yau ya zama abin da ya zama. Babu zumunci da taimakon juna, balle riƙon aman. Kowa ya kama gabansa, kansa kawai ya sani sai ‘ya’yansa. A yau, idan iyaye suka mutu suka bar marayu sai ‘yan’uwa su sa musu ido suna taggayara, babu ilimin addini balle na zamani, ba su samun tarbiyya balle su amfani kansu da al’umma baki ɗaya. A yau idan ba ka da abin hannunka, babu ɗan’uwa mai kusantarka domin ba a samun komai wurinka. Hatta shawara a kan wasu al’amurra na rayuwa ba a yi da kai balle ka san halin da ‘yan’uwa suke. Su kuwa ‘yan’uwa masu abin hannunsu sun keɓe kansu ba su buƙatar kowa ya ziyarce su don gudun  a  aza musu lalura.
                Zamantakewa tsakanin masu mulki da talakawa kuwa ya sauya fasali a yau. A maimakon kare haƙƙin talakawa da mutuncinsu, masu mulki sun sanya ƙafa sun shure wannan ɗawainiya da ya ratayu a kansu. Sun kasa tsare mutuncin talakawa, sai cin amana da danne haƙƙoƙinsu da ma barazana ga rayukansu.  Masu mulki sun ƙi su jawo talakawansu ga jiki domin sanin halin da suke ciki. A dalilin haka, su kuwa talakawa sun bijire ba su ganin mutunci da darajar masu mulki balle su yi musu biyayya. Talakawa sai muguwar addu’a suke yi wa masu mulki saboda danne haƙƙoƙinsu da ake yi. Zamantakewa ya taɓarɓare ta yadda sai an kashe haki kafin yabanya ya sami walwala.
    3.1 Dalilan Taɓarɓarewar Zamantakewar Hausawa a Yau
                A bayanin da ya gabata, an bayyana cewa, kyakkyawar yanayin zamantakewar Hausawa a jiya ya samu gindin zama ne saboda riƙo da wasu ɗabi’u da al’ada da addini suka amince da su, kamar gaskiya da riƙon amana, zumunci, haƙuri, taimakon juna, da makamantansu. A duk lokacin da al’umma suka rasa ire-iren waɗannan al’adu, ko suka yi rauni a rayuwarsu, tilas halin zamantakewar wannan al’umma ya taɓarɓare. Wasu daga cikin abubuwan da nake ganin sun taimaka wajen haifar da wannan taɓarɓarewa na zamantakewar Hausawa a yau sun haɗa da:
    3.1.1 Yawaitar Zalunci
    Saɓanin inda aka fito, a yau galibin al’ummar Hausawa burinsu bai wuce tara abin duniya ko ta halin-ƙaƙa (halat ko haram). Masu kuɗi sun rage taimakon na ƙasa gare su. Su kuwa masu mulki sai danne haƙƙin talakawa idan sun shigo hannunsu. Shugabannin yanzu sun daina wakiltar talakawansu, babban burin akasarinsu shi ne su wawari dukiyar talakawa da suka shigo hannunsu a matsayin amana ta yadda ko bayan sun sauka ba za su talauce ba daga su har jikokinsu. A kan haka, a yau matsananciyar adawa ta wanzu tsakanin shugabanni da waɗanda ake shugabanta, sai kallon-kallo ake yi wa juna. A yau, a gida guda ma idan wani abin amfani ya shigo hannun wani daga cikin gidan wanda za a raba kowa ya amfana, sai ka iske wannan da kayan ya shigo hannunsa ya wawuri wanda ya fi na saura.      
    3.1.2 Rashin Haƙuri da Juriya
    A yau rashin haƙuri da juriya ya yi tasiri ainun a tsakanin al’ummar Hausawa. Tashin hankula ya yawaita a tsakanin ma’aurata, koyaushe sai an yi sulhu saboda yawan faɗace-faɗace. {arin tabbatar da wannan zance shi ne, a leƙa kotunan alƙalai za a ga yawan ƙararrakin da ake shigarwa a kowane yini waɗanda suka shafi ma’aurata ne (Gusau 1991). Zawarawa sun yawaita a kowane sashe na gari. A unguwa ɗaya sai ka sami zawarawa bila’adadin an sako su, wanda galibi saboda rashin haƙuri da juriya ne. Ko a baya-bayan nan ma, hukumar Hisba ta kano ta fitar da ƙididdigan yawaitar zaurawa da ake samu.
    3.1.3 Zamani (Samuwar Intanet da Finafinai)
    Idan aka yi la’akari da muhawarar masana da manazarta a kan alfanu da koma baya da fina-finai suke samar wa, za a iya cewa, fina-finan Hausa sun kasance hanjin jimina, akwai na ci a kwai na zubarwa. Haƙiƙa fina-finan suna taimakawa ta ɓangarori da dama. Ali, (2004) ya ce, a tsawon ƙarnuka biyu da suke wuce, samuwar fina-finan Hausa shi ne hanyar haɓaka tattalin arziki mafi girma da ya samu ga al’ummar Hausawa. Sai dai duk da haka, manazarta irin su; Iyan-tama, (2004) da Alkanawy, (2000) suna ganin samuwar finafinan Hausa yana da illa ga al’ummar Hausawa.
    Daga cikin illolin finafinan akwai ɓatar da al’ada. Al’adar kuwa ta haɗa da zamantakewa. Samuwar finafinan ya sanya Hausawa kwaikwayon salon rayuwar wasu al’ummu na daban, kamar Turawa da Indiyawa. Wato an mance da irin zamantakewar Hausawa na cuɗe-ni-inp-cuɗe-ka (Chamo, 2004; Ɗangambo, 2013; Guibi da Bakori, 2013). Kiyawa, (2013) ya nuna cewa, finafinan sun ci karo da addinin Musulunci sannan suna rusa ruhin auratayya da zamantakewa ta gari. Sannan akwai tarin manazarta da suke da wannan ra’ayi (finafinai sun taka rawargani wurin taɓarɓarewar zamantakewa ta gari). Sun haɗa da: Mwani da Ƙanƙara, (2013) da Mai’aduwa, (2013) da Sulaiman (2013) da Ɗan Maigoro, (2013) da Gwammaja, (2013) da Abdullahi da Maidabino, (2013) da Inuwa, (2013).
    A ɗaya ɓangaren kuma, samuwar intanet ta shagaltar da da dama daga cikin Hausawa, musamman matasa. Ta wannan kafa sukan ɗauki ɗabi’u daban-daban na baƙin al’ummu musamman Turawa. Sauran illolin kafar sun haɗa da yaɗa muguwar farfaganda da jita-jita, da ɓata lokaci da kuma kalle-kallen batsa (‘Yartsakuwa, 2017).
    3.1.4 Rashin Gaskiya da Amana
    ‘Yan kasuwa sun bijire wa gaskiya, sai son cin amana da yaudara da cin ɓatacciyar riba da ɓoye abubuwan sayarwa sai sun yi tsada. A yau, idan mai dukiya ya jawo talaka cikin arzikinsa domin kowa ya amfana, sai talakan ya sa rashin gaskiya da cuta, ko kuma shi mai arzikin ya riƙa danne haƙƙin yaron nasa. A yau idan ka ba wani saƙon kaya ko kuɗi ya kai ma wani wuri ko ya adana maka har na tsawon wani lokaci, sai ya ci amanarka ya ƙi kai saƙon ko ya salwantar da ajiyar da ka ba shi. A yau mai gaskiya bai cika tasiri a mafi yawan kotunan shari’ummu ba, sai dai wanda ya fi ƙarfin ba da abin hannunsa. Mata ta ci amanar mijinta, miji ya ci amanar matarsa. Masu mulki da shugabanni sun murje ido sun yi babakere da handamar dukiyar talakawa da aka ba su amana. Babu gaskiya da amana tsakanin abokai da ‘yan uwa, ga abubuwa nan dai duk sun taɓarɓare. Ba manufata ba ne da wannan bayanai cewa, babu kyakkyawar zamantakewa baki ɗaya a ƙasar Hausa a yau ba, sai dai don yin hannunka-mai-sanda ga al’ummarmu domin a farga ta yadda za a shawo kan matsalar tun abin bai yi muni sosai ba. Maikadara, (2012) ya yi tsokaci kan wasu daga cikin halayen rashin gaskiya da ke faruwa a yau.
    4.0 Hanyoyin Farfaɗo da Zamantakewar Hausawa
              Haƙiƙa za a iya cewa, taɓarɓarewar da zamantakewar Hausawa ta yi a yau bai yi munin da za a kasa samar da hanyoyin da za a warware matsalar ba muddin an himmatu da gaskiya. Dole iyaye su farga wajen cusa kyakkyawar tarbiyya tagari a zukatan ‘ya’yansu ta yadda za su rayu bisa turba madaidaiciya da za ta amfani al’umma, kamar gaskiya da mana, ladabi da biyayya ga na gaba, sai kuma uwa-uba haƙuri wanda aka ce shi ne gishirin zaman duniya.
                Su kuwa malamai tilas su taka irin tasu rawa wajen gargaɗi a kan hani da horo na koyarwar addini da al’ada a kan irin zalunce-zaluncen da ya yi katutu a rayuwarmu ta yau. Haka zalika su ci gaba da bayyana wa jama’a irin mummunar sakamakon da ke tattare da aikata miyagun ɗabi’u da al’adau ga masu aikata su. Har wa yau, dole gwamnati ta sanya ido ga harkokin shari’a ta yadda za a daidaita adalci ga kowa, da kuma hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba. Su kuwa sauran mutane kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa da halayyanrsa ta yadda rayuwarmu za ta sake komawa ga turba mai tsarki da muka gada daga magabatan da suka wuce.
    5.0 Kammalawa
              Zamantakewa abu ne da ya shafi illahirin rayuwar mutane, idan ya inganta, rayuwar al’umma ce za ta kyautatu, idan kuma ya lalace, rayuwar al’umma ce za ta taɓarɓare baki ɗaya. A taƙaice ana iya cewa, tun asali al’ummar Hausawa suna da ingantaccen tsari na zamantakewa a tsakaninsu da kuma sauran jama’a masu maƙwabtaka da su. Sai dai kuma, babban abin takaici a yau shi ne, wannan kyakkyawar halayya tana fuskantar gagarumar barazana na taɓarɓarewa. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda son kai da kwaɗayin tara abin duniya, da rashin gaskiya da amana da haƙuri da ya mamaye al’ummarmu ta wannan zamani. Sai dai ana cewa, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba, ma’ana za a iya bin wasu hanyoyi da aka ambata a baya wataƙila a shawon kan matsalar ta yadda al’ummarmu za ta sake ginuwa kamar inda aka fito.

    Manazarta
    Abdullahi, I. da Maidabino, I. B. (2013). Rawar da fina-finan hausa suke takawa wajen ɓata al’adun Hausawa: Nazari daga fina-finai biyu Ƙara’i da Babban Yaro. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Alhassan, H. da wasu  (1982) Zaman  Hausawa.  Islamic Publications Bureau, Mushin, Lagos
    Ali, B. (2004). Historical reɓiew of films and Hausa drama, and their impact on the origin, development and growth of the Hausa home ɓidious in Kano. In Adamu, A. U. et al (eds). Hausa Home Videous: Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino Publishers.
    Al-kanawy, A. S. (2004). Fina-finan Hausa: Faɗakarwa ko shagaltarwa? In Adamu, A. U. et al (eds). Hausa Home Videous: Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino Publishers.
    Bugaje, H. M. (2013), Tarbiyya da Zamantakewar Hausawa: Jiya da Yau.” Mu}alar da aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar adua, Katsina.
    Bunza, A.M. (2006)  Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited, Surulere  Lagos.
    Bunza, U.A. (2012), “Tarbiyya a Cikin Adabin Hausa: Tsokaci da Karin Magana.” Mu}alar da aka buga a cikin Kada Journal of Liberal Arts, Ɓol: 7 No. 1, Faculty of Arts, Kaduna State University, Kaduna.
    C.N.H.N.   (1981)   Rayuwar   Hausawa.  Littafin  da  Cibiyar  Nazarin   Harsunan  Nijeriya Jami’ar Bayero Kano ta wallafa.
    Chamo, I.Y. (2004) “Tasirin  Al’adun  Turawa  a  cikin  Finafinan  Hausa”. A cikin Hausa Home Videos: Technology, Economy,  and Society,  Jami’ar Bayero Kano.
    Countries and their Cultures Forum (CCF), (2009). Hausa. Retrieɓed on 21 September 2016 from: http://www.city-data.com/forum/ - world-forums
    Ɗan gambo, H. A. (2013). Gurɓacewar al’adun hausa a yau: Dalilansu da hanyoyin magance su. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    [anyaya, B. M. (2007). “Karin Maganar Hausa.” Sakkwato: Makarantar Hausa.
    Ɗan Maigoro, A. (2013). Tashin gwauron zabin fina-finan Hausa da taɓarɓarewar al’adun Hausawa a goshin ƙarni na 21. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Gada, N. M. (2014). Kutsen baƙin al’adu cikin hidimar aure a Sakkwato. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
    Guibi, I. I. da Bakori, A. D. (2013). Rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen ruguza al’adun Hausawa. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Gumel, (1992). Tarbiyya da [angoginta a Wa}o}in Baka na Hausa”. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Afirka da Al’adu,   Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
    Gusau, S.M.  (1999)  “Tarbiyya  a  Idon  Bahaushe” A cikin Algaita Journal of Hausa Studies. Jami’ar Bayero Kano. Ɓolume 1 No 1.
    Gwammaje, K. D. (2013). Kitso da ƙwarƙwata: Wakilcin al’adun Hausawa a fina-finan Hausa. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Inuwa, U. A. (2013). Kutsen baƙin al’adu cikin fina-finan Hausa da yadda suke gurɓata al’adun Bahaushe. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Iyan-tama, H. L. (2004). Matsayin fina-finan Hausa a Musulunci. In Adamu, A. U. et al (eds). Hausa Home Videous: Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino Publishers.
    Ka’oje, U. I.  (2006)  Tarbiyya  a  Ƙagaggun  Labaran  Hausa : Nazari  kan  ‘Ya’yan  Hutu na Malama  Bilkisu  Funtuwa. Kundin  digirin  farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
    Kiyawa, H. A. (2013). Tsokaci a kan wasu matsalolin fina-finan Hausa wajen ɓata tarbiyya. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Koko, H. S. (2011). Hausa Cikin Hausa. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Sakkwato: Nijeriya.
    Magaji, A. (1999)  “Kunya  da  Mutunta Mutane a Al’adar Bahaushe” A cikin Algaita Journal of Hausa Studies, Jami’ar Bayero Kano.
    Mai’aduwa, A. A. (2013). Taɓarɓarewar al’adun Hausawa a yau: Nazari a kan fina-finan Hausa. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Maikadara, I. B. (2012). “Tarbiyya a Rubutattun Wa}o}in Hausa na {arni na Ashirin. Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Malumfashi, I. & Nahuce, M.I. (2014). Kamusun Karin Maganar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media Services.
    Mwani, J. A. L. da Ƙanƙara, I. S. (2013). The role of films in moral decadence among Hausa yourth and the emergence of ƙauraye miscreant actiɓities in Katsina. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    Ƙamusun Hausa (2006). Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero Kano
    Sani, A-U. & Abdullahi, M. (2016). Global Growing Impact of Hausa and the Need for its Documentation. Being a paper presented at the 29th Annual Conference of Linguistic Association of Nigeria (LAN) on Language and Linguistic Diɓersity: Documentation and Reɓitalization of Minority Languages for Sustainable Development, at the University of Jos, Plateau State, from 5th to 9th December, 2016
    Sulaiman, A. I. (2013). Ta’addancin fyaɗe a fina-finan Hausa: Tsokaci kan tasirin fina-finan hausa ga taɓarɓarewar al’adu yau. A cikin Bunza, A. M. da wasu (editoci). Exepts of International Seminar (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa). Zariya: Ahmadu Bello University Press.
    ‘Yartsakuwa, U. D. (2017). Zumunci a yanar gizo: harshen sadarwa tsakanin matasa a shafin whatsapp. Kundin nemen digirin farko (B.A Hausa) a ƙarƙashin Sashen Nazarin Harshunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.


    Pages