Karar Tsana: Gudumar Dukan Watsattsu

    ... Yayin da na É—aga kai na dubi cakwalkwalin cakwakiyar da duniyar matasantaka ke ciki a yau, sai na tuna maganar malamina a sakandare da yake cewa: “A concentrated mind is never taken away.” Sai kuma na ce da kaina, kenan “A determined mind is never taken away.” A nan sai maganar mahaifiyata ya dawo mini (sai an kula kashi yake É—oyi). Ai kuwa nan na gane cewa, babbar hanyar kauce wa tarkon watattsu shi ne samun gudumar dukansu. Gudumar da ta fi dacewa kuwa ita ce KARAR TSANA. Yayin da mutum ya tsani halinsu da salonsu, to lallai salon nasu ba zai taÉ“a burge shi ba ballantana har ya ji yana ra’ayin É—anawa....



    Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures
    Federal University Gusau, Zamfara
    Phone No: 08133529736
    Email: abuubaidasani5@gmail.com

    Bismillahi a farkon zance,
    Sunan Allah zan yo sawa.

    Na roƙe ka ka ƙaran baiwa,
    Domin waƙar in tsarawa.

    Ƙara salati gun sa Rasulu,
    Manzon nan da ka yo aikowa.

    Har da iyalai nasa a jimla,
    Har da sahabbai su duka kowa.

    Har mabiyansa dukka mutane,
    Kan sunnarsa har ran tsaiwa.

    Dam É—in zance yau ya batse,
    Ambaliya zai yo tasowa.

    Abin da ka ƙunshe yau ya kwance,
    Zai ko baje a gani duka kowa.

    Ran wanka ba É“oyon cibi,
    Yau zancen ba na sakayawa.

    Zan magana ne kan watsattsu,
    Siffofinsu za ni faÉ—owa.

    Ko da ka kalle su da tsafta,
    Sun sa kaya mai burgewa.

    To wannan siffar fenti ce,
    Ga ta usul zan yo zanawa.

    Kar da kuÉ—inta ya ko dame ka,
    Kyan halinta kawai kai tsaiwa.

    Kyawun fuska daban da na zuci,
    Zuci ake so ai dacewa.

    Runtse idonka in ba ka kamarta,
    Siffofinta ka yo ganewa.

    Idan da abinci gabanka ka kau sai,
    Kar da amai kai yo kwazawa.

    Don da ita gwamma ka ga kashi,
    Ko kakin da a kai tofarwa.

    Kai jama’a muni ga kumatu,
    Tamkar bakuru tai cusawa.

    Ga goshi ko abin ban tsoro,
    Kamar jaki sabon haihowa.

    Ga da ma kuwa ba ta da gashi,
    Ga sanƙonta yana haskawa.

    Siffar kanta ya dutsen guga,
    Ya za ai gashi ya tsirowa?

    Hancin nan ya gajeren wando,
    Kamar kwaÉ—on da a kai takawa.

    Hancin nan fa ƙananan ɓewa-
    Tsaf za su iya su wucewa.

    Ina tsammanin ya fi na jaki,
    Musamman yayin numfasawa.

    In ta yi bacci tana minshari,
    Kamar inji aka yo tadawa.

    Shape É—in hancin aka É—auki design,
    Ƙofar fada a kai zanawa.

    Ka ga idonta kamar ‘yar mage?
    Ga su da kwantsa ba wankewa.

    Ga bakinta kamar an yi É“arna-
    Nan da wuƙa ga babbar kabewa.

    Kwatancen bakin ka san ganda?
    Musamman baƙi dake nannaɗewa.

    Ka ga haƙoran kamar katafila,
    Wanda kacarta ta yo tsinkewa.

    Daga nesa ka hanga tamkar kanti,
    Na cokala da ake saidawa.

    Don sun watse ba su da tsari,
    Kamar gyauron da su kai tasowa.

    Na É—an kwan biyu ina ta hasashe,
    Yanzu gare ku ko zan furtawa-

    Kamar harshenta bature ya kalla,
    Farfelarsa ya yo tsarawa.

    Har da ko nata salon karkarwa,
    Yayin gulma da shegen tsiwa.

    Ban ma fara kwatanta giranta,
    Don ko babu da nai dubawa.

    Ka ga wuyanta kamar na aro ne,
    Can ya danƙara bai miƙewa.

    Kunnen nan ko ya faifan goro,
    Wanda samansa ake saidawa.

    Kwatancen cikinta katifar mayu,
    Nan muninta ya yo tarewa.

    Da dai ka san kabarin É—anwada,
    Siffar kenan ba ka rabewa.

    Ka ga ƙafarta ya tsinken bawul,
    Sandar sabulu ta fi shi direwa.

    Sai ma ka dubo daga nesa,
    Kamar lauje sukai bauÉ—ewa.

    Kuturta cuta ce da daga Allah,
    Ita ga ƙazanta tai samowa.

    Gajera ce kuwa ‘yar É—if ga ta,
    Ga shi baƙinta kamar shafawa.

    Tamkar an shafa mata fenti,
    Duna ɓaleri ƙirin aka cewa.

    Ko ƙwan wutarka na nan da haske,
    In ta doso zai yi dushewa.

    Ka ga salon tafiyar ‘yar iskar?
    Ga fa kwatance kai ganewa-

    Ka san ƙaguwa na bauɗewa,
    Salonsu guda a wurin takawa.

    Idan ta yi sauri sukan bambanta,
    Tamkar agwagwa take komawa.

    Ga ko hanunta kamar katako,
    Shi taurinsa daban da na kowa.

    Fatar jikinta irin ta guza ce,
    Sak tsarinsu da nai dubawa.

    Kaushin ƙafarta yana amfani,
    Ta yi bajinta ban É“oyewa.

    Ai wata rana ana kan aiki,
    Ana fasa titi don gyarawa.

    Sai katafilar tasu ta É“aci,
    Ga shi ana son ai ƙarewa.

    Ai ita goganyar da ta taso,
    Wucewa É—ai tai ba dawowa.

    Duk kuwa titin sai da ya É“arje,
    Katafila ranar tai hutawa.

    Ranar an ga abin mamaki,
    Fasonta ko ya burge Turawa.

    Na ji Bature yana gulmarta,
    Cikin Turanci yake furtawa:

    I have never seen a robot,
    So active ya wanan É—an baiwa.

    I thought first it was a gorilla,
    The way na gan shi yana takawa.

    Oh! Technology is advancing,
    Where on earth a kai ƙerawa?

    Ni ko na ce masa is not a robot,
    That is faso je kai dubawa.

    Allah ya yi hani ga mazaje,
    Su taɓi mace ko shafawa.

    Na san taɓinta ko babu halaki,
    Ko alwala ba ya karyawa.

    Idan ba ka farga ba ma ta taɓe ka,
    Gadon bayanka ta yo shafawa.

    Za ka kai bugu ne da sauri,
    Da niyar dai ka yo maujewa.

    Kai a zatonka gwadan-gwale gwada,
    Shi ne bayan ya yi É—alewa.

    Babbar matsala na nan yawunta,
    Idan ƙaddara tai yo gittawa.

    Sai ka ji an ce an yi disaster,
    To yawu ne tai tsittarwa.

    An ce gado tai na fitsari,
    Nan a gado da dare tsulawa.

    Wai da Maliya ba shi da aibu,
    Ruwansa garau akan kurɓawa.

    Sai da uwarta ta tsula fitsari,
    Yai sanadinsa na gurɓacewa.

    Idan ka gan ta kamar goggo ne,
    Shi da ita ba a fa rabewa.

    Na samu ubanta a kwanan baya,
    Ga shi shawara nai bayarwa.

    Ka san yana da kuÉ—i har na banza,
    Amma ga Allah bai godewa.

    Sai dai a tara ba a kyauta,
    Balle zakka bai fiddawa.

    To da ma fa kuÉ—i na haramun,
    Ba albarka mun shaidawa.

    Kullum sai kuka na talauci,
    Babu wadatar zuci daÉ—awa.

    Na ce tun da talauci ya kam mai,
    Ya É—aure shi bai motsawa.

    Ya É—auki É—iya yai gidan dabbobi,
    Ya ce ai biri ya zo saisarwa.

    Amma shegen bai ji batu ba,
    Sai da ƙwaƙwalwa ake ganewa.

    Amma daga baya da na duba,
    Ba shi da laifi nai ganewa.

    Tsoro ya ji in har ya tafi,
    Har shi ma za ai kamewa.

    Ku tare- kutare! Ga tsohon goggo,
    A keji shi za ai dannawa.

    Har daga baya a ƙarfafa zance,
    A nemi haÉ—in guiwar Turawa,

    Su kai shi Amerika su sa É—akin lab,
    Experiment za su yi dubawa.

    Abin dai ya É—aure musu kayi,
    Yadda biri yaka zantawa.

    Ga furucinsa ko sak da mutane,
    Sai dai ba ma’anar kamawa.

    Kai! Da na duba uwar ‘yar banza,
    Sai nai kurum ina ta tunawa.

    Na ga dalilin da ake ta hasashe,
    Ra’in nan da ake zanawa-

    Asalinmu birai ne, sannu-a-sannu-
    Har mu ka zam mun yo sauyawa.

    Har muka samu sifa ta mutane,
    Yanda a yanzu muke duka kowa.

    Tabbas zuriyarsu ce aka duba,
    Wannan theory a kai tsarawa.

    Mu leƙa tarihin danginsu,
    Labari zan yo bayarwa.

    Akwai wani can tsohon kakansu,
    Da Turawa suka yo kamawa.

    Suka kai shi ƙasarsu wanda a sannan,
    Ta fi Amerika ginin burgewa.

    Da ya dube su ya bankama tusa,
    Gininsu da dama yai rugujewa.

    Injinansu duk sunka yi tsatsa,
    Ruwansu na sha yai gurɓacewa.

    Dabbobi da yawa sun mace,
    Wasu da dama sun arcewa.

    ÆŠai daga cikinsu ko shi ne bodari,
    Shi Nijeriya yay yi tahowa.

    Ka san ya shaƙo ita iskar,
    Ita ce yanzu yake fiddawa.

    A nan ne zan ja in dasa aya,
    Kayan haushi nai ƙyalewa.

    Abu-Ubaida wanda ya yi ta,
    ÆŠan Sani ga mai dubawa.

    Garinmu Misau ne can ko na taso,
    Jahar kuwa Bauchi ban É“oyewa.

    Nai godiya kana na ƙara,
    Gare shi Ilahu maƙagin kowa.

    Na yi salati gun manzonmu,
    Da sallallami na yo ƙarawa.

    ÆŠari da shida ne baitocinta,
    Hamdalla na yo ƙarewa.

    Tsokaci

    “Sai an kula kashi yake É—oyi!” Ina tunanin na fara jin wannan karin magana ne wurin mahaifiyata. HaÆ™iÆ™a za a iya cewa wannan batu gaskiya ne. Abin da mutum ya sanya a ransa kawai shi ke damun sa. Misali, yayin da mutum ya Æ™wallafa son wani ko wani abu a ransa, to duk abin da masoyin nasa ya aikata zai kasance abin burgewa a gare shi. Za ta yiwu wannan ne dalilin da ya sa Bahaushe ke cewa: “So mai kau da ganin laifi.” Sani Sabulu ma cewa ya yi: “Ƙauna ba ta gano wahala.” A É“angare guda kuma, yayin da mutum ya É—auki karar tsana ya É—ora wa wani ko wani abu, to kuwa duk wani motsi na abin da ya tsanar nan, zai kasance abin É“acin rai ne a gare shi. A taÆ™aice dai, abin ba zai taÉ“a burge shi ba kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Mai son ganin laifinka, ko da ruwa ka faÉ—a sai ya ce ka ta da Æ™ura.”

    Kalmar watattse a wannan bagire ta zo da manufar duk wanda ya É“ata kuma yake Æ™oÆ™arin É“atarwa. Kenan dai muna iya cewa, watattsiya ita ce wanda ta É“ata kuma take Æ™oÆ™arin É“atarwa. Akan samu irinsu, musamman a yanzu da wakilan sheÉ—an suke Æ™ara yawaita. Ma’ana a zamanin da har saÉ“o ya zama kwalliya da burgewa a cikin al’umma. Rashinsa kuma ya zama Æ™auyanci da rashin wayewa.

     Saboda haka:
    Ƙarya ta zama sinadarin zance
    Ashare-ashare suka zama kwalliya a cikin zance
    Batsa ta zama gishirin zance
    Namiji na iya kiran mace ‘Æ™awata’, kuma ya ce shi ba ‘É—an daudu’ ba ne
    Fitar da tsiraici ga mata ya koma abin yau da kullum
    WaÉ—anda maza suka fi son cuÉ—anya da su, su ne matan da ke yawo da tsiraici waje
    Shaye-shaye ya koma abin ado da nishaÉ—i tsakanin maza da mata
    Kasuwar zina ta yi tashin gwauron zabi
    Yaudara tsakanin ‘yammata da samari ta zama ruwan dare
    Samari da ‘yammata suka zama kurame ga sautin gaskiya, makafi ga walÆ™iyar gaskiya sannan kutare ga karÉ“arta.

    Yayin da haushi zai rufe ka, sai wani ko wata ya riga ka cewa: “Amin” yayin da aka ambaci: “Allah ya sa mu shiga aljanna.” An san cewa imani a zuci yake, amma ko ba komai ai: “Alamun Æ™arfi yana ga mai Æ™iba.” Kuma ma; “Labarin zuciya a tambayi fuska.” To ma wai, me laifin “ko kana da kyau ka Æ™ara da wanka?” A taÆ™aice dai, halayen matasa a yau sai dai a maimaita abin da jakin dawa ya faÉ—i yayin da ya ga na gida, wato: “Allah wadarai naka ya lalace.” Wani Æ™arin kayan haushi shi ne, kowane matashi addu’arsa ita ce samun mata ta gari. Haka ma budurwa addu’arta kenan samun miji na gari. Na taÉ“a ji wani malami yana tambaya: “To wa zai auri waÉ—anda kuka yi ashararanci da su? WaÉ—anda kuka É“ata wa rayuwa, kuka É“ata wa lokaci?”

    Yayin da na É—aga kai na dubi cakwalkwalin cakwakiyar da duniyar matasantaka ke ciki a yau, sai na tuna maganar malamina a sakandare da yake cewa: “A concentrated mind is never taken away.” Sai kuma na ce da kaina, kenan “A determined mind is never taken away.” A nan sai maganar mahaifiyata ya dawo mini (sai an kula kashi yake É—oyi). Ai kuwa nan na gane cewa, babbar hanyar kauce wa tarkon watattsu shi ne samun gudumar dukansu. Gudumar da ta fi dacewa kuwa ita ce KARAR TSANA. Yayin da mutum ya tsani halinsu da salonsu, to lallai salon nasu ba zai taÉ“a burge shi ba ballantana har ya ji yana ra’ayin É—anawa.

    Wannan waÆ™a ban shirya ta kan wata mace takamaimai ba. Sannan babu wanda ta É“ata mini rai kafin na fara rubuta ta. A taÆ™aice dai, na yi Æ™oÆ™arin bayyana matakan da na É—auka wa kaina ne, wanda kuma muka yi tarayya da mutanen da ke jan zaren tunani irin nawa. Wato matakan kau da kai daga aikin banza, da “yanka wa kare ciyawa” da zaman kashe wando da makamantansu. A cikin waÆ™ar, na nuna irin hoton da zuciyata ta É—auka ta adana a matsayin siffar duk wata watsattsiya. Kuma hakan ne ya sanya, dukkanin caffa da zararsu kan kawo wa watana kan zama na banza, da yardar Ubangiji. Daga Æ™arshe sai abin ya kasance: “Ko a jikina wai an tsakuri kakkausa.”

    author/Sani, A-U.

    journal/Poem
    pdf-https://youtu.be/217Rbd-6SA4

    paper-https://youtu.be/217Rbd-6SA4

    Pages