Adashen Ƙauna 4 (A): Kwarjinin Ash’ab  1. 1.      Alhamdulillah mahaliccina,
   Sarkin da ke da cikar mulki.

   2.      Kai ke halitta ya Allah,
   Iri-iri wuce mamaki.

   3.      Kai ka yo halittal bil Adama,
   Har da Humaira ɗiyar kirki.

   4.      Ƙaran basira ya Allah,
   In tsara zancen daki da daki.

   5.      Daɗo salati ga manzona,
   Muhammad Aminu mai tsarki.


   6.      Haɗa da alaye har ma-
   Sahabu da ba sa raki.

   7.      Saka da sauran muminnai,
   Mabiyansa daidai a tafarki.

   8.      Yau tambaya ce na ɗauko,
   Humaira zan yo a gare ki.

   9.      Humaira yaushe zan gan ki?
   Yaushe zan gan ni gabanki?

   10.  Yaushe rai zai yo sanyi?
   Yaushe zan rage tunaninki?

   11.  Sai ki ga ni na yo kasaƙe,
   Na tsunduma faman kallon ki.

   12.  A a fili ba sai can a tunani,
   A duniyarta na je gun ki.

   13.  Wani loton ko da ina tafiya,
   Ni ɗai murmushi za ni saki.

   14.  Idan ko hakan nan ya faru,
   To tabbas na tuno ki.

   15.  Humaira wai kin san me ne?
   Kullum nakan yi mafarkinki.

   16.  Na gan ki kan karagar mulki,
   Ga fadawa na gefenki.

   17.  Kanki da hular zinari,
   Da alkyabbar gwal a jikinki.

   18.  Yaushe za ki daina gizo ne?
   Ga kowa in daina ganinki?

   19.  Wai ko kin san mene ne?
   To a kullum sai na kalle ki.

   20.  Da zarar an gilma haka nan,
   Sai na ga ai sak tamkarki.

   21.  Da na duba haka nan sosai,
   Sai na ga ai sam-sam ba ki.

   22.  Wai yaushe zan saba ne-
   In daina kyarma a gabanki?

   23.  Humaira yaushe zan goge-
   Daga wannan kwarjini naki?

   24.  A’isha wai yaushe ne ne-
   Zan daina tsoron kallon ki?

   25.  Ash’ab wai sai yaushe ne-
   Zan bar tsoron haibarki?

   26.  Humaira wai me ya saka ne-
   Na kasa kimanta surarki?

   27.  A’isha wai me ne dalilin-
   Na kasa ƙiyasta kyawunki?

   28.  Ash’ab yaya kika yi ne-
   Ki tsara takun sawunki?

   29.  Kamar a Ingila kinka yi kwas,
   Salon tafiyar ban mamaki.

   30.  Hummy wai yaya ne kam-
   Na ƙagu da kallin fuskarki?

   31.  Wai kin san farar madara?
   Da wuya ta kai ya idanunki.

   32.  Baƙin ciki ko ya daidaita,
   Ya ƙara fito da idanunki.

   33.  Kyawu na nan ga girarki,
   Nan sama na idanunki.

   34.  Baƙinsa fa shi ke burge ni,
   Yai kyau da hasken fuskarki.

   35.  My One kin ma san me ne?
   Kyawu sai ma hancinki.

   36.  Ba don ikon Allah ba-
   Na ce yin sa da mamaki.

   37.  Da ɗan Adam ne ke yin sa,
   Sai an taru a yo naki.

   38.  Sai injiniyoyi sun taru,
   Tun daga Cana har Taki.

   39.  Tsawonsa ya ma me zan ce?
   Kawai dai dogon hancinki.

   40.  Ya so da ya wuce baki,
   A ɗan sama amma yai birki.

   41.  Watakil ya yo kishi ne,
   Da tsantsar kyawun bakinki.

   42.  A duniya akwai kaligirafas,
   Sun iya zanen mamaki.

   43.  Amma dukka gwanintarsu,
   Ba mai zanen bakinki.

   44.  Ko na ga zane mai kyawu,
   Bakin ba ya kai naki.

   45.  Kin ga dai tsukakke ne,
   Daidai girman fuskarki.

   46.  Kyan ma sai kin yo magana,
   Kin bayyana jerin haƙoranki.

   47.  Fararen nan sun yi sahu,
   Tamkar a Ka’aba gaban Sarki.

   48.  Tsawonsu ɗaya haka ƙirarsu,
   Haskensu na daɗa kyawunki.

   49.  Hummy wai kin san me ne?
   Halan in yi research kan ki.

   50.  Kin san me zan gano ko?
   Dalilan kyan murmushinki.

   51.  Zan bincika wai ko dai-
   A iya koyon murmushinki?

   52.  Watakila a buɗe jami’a,
   A damƙa dukanta a hannunki.

   53.  Kwas za a riƙa koyarwa,
   Na kwaikwayon murmushinki.

   54.  Hakan zai taimaki mataye,
   Halan sui kyau ya kwatan naki.

   55.  Kai! Ina! Ko kwatan-kwata,
   Sai dai sui ta kwatancen ki.

   56.  Ah! Na ko gano sirri-
   Da ke ƙara salon kyanki.

   57.  Sirrin na ga kumatunki,
   Zubinsu daidai fuskarki.

   58.  Tamkar ki ce kika zaɓa,
   Mai kyawun kika ba kanki.

   59.  Hmm! Wai kin san mene ne?
   Na ruɗe bisa gashinki.

   60.  Baƙinsa, tsawonsa, yalƙinsa,
   Ga sheƙi da yake kanki.

   61.  Humaira aiki zan ba ki,
   Ina so ki ɗaga hannunki.

   62.  Kin duba kyawun fatarki-
   Ya na ga kina mamaki?

   63.  Hummy ba ni da kalma,
   Na suranta kamanninki.

   64.  Sai dai kawai zan ce,
   Kamar kanti aka ɗauko ki.

   65.  Fara ce ke kyakkyawa ce,
   Doguwa a kwatancen ki.

   66.  Mai sura ta cikar haiba,
   Da kwarjinin ban mamaki.

   67.  Rana na yin murna,
   Yayin da Humaira ke ɗaki.

   68.  Dalili haskenta na raguwa,
   Idan yai arba da haskenki.

   69.  Wata na san kyakkyawa ce,
   Amma ko tana kishin ki.

   70.  Ranar sha huɗu ta yi ado,
   Kwance wa tai da ganin ki.

   71.  Ran nan na sha mamaki,
   Hanyar dawowa aiki.

   72.  Wani ɗawisu ke tinƙaho,
   Can daga nesa ya hango ki.

   73.  Sai na ga jiki nai yai sanyi,
   Nan fa ya tsaya kallon ki.

   74.  Har kika gilma ta gabansa,
   Yana taf fushi ga mamaki.

   75.  A nan ya ruga ga madubi,
   Ya tsaya gabansa cikin haki.

   76.  Ya kalli kansa ya tuna ki,
   Cikin haushi ya yiwo tsaki.
              

  Pages