Zogale a Ƙasar Hausa (Magani, Abinci, Tattalin Arziki)
Na
Adamu Rabi’u Bakura
Itaciyar zogale (Moringa oleifera Lam) ta kasance ɗaya daga cikin shahararrun tsirrai da suka samu karɓuwa a duniya, saboda ɗimbin amfaninta a fannoni daban-daban na rayuwar ɗan'adam. Wannan itaciya mai albarka, wadda Allah ya halicce ta da sinadarai masu ban mamaki, ta zama tushen abinci, magani, da kuma tattalin arziki ga al'ummomi da dama, musamman a ƙasar Hausa. A cikin al'adun Hausawa, zogale ba wai kawai itaciya ce da ake dafawa a ci ba. tTana da matsayi na musamman a fannin maganin gargajiya, abin ƙwalama, da kuma hanyar samun kuɗi da ta shafi sana'o'i daban-daban.
Ganin yadda itaciyar zogale take da muhimmanci a rayuwar Hausawa da kuma irin fa'idojin da take ƙunshe da su, wannan littafin ya mayar da hankali a kan bincike da nazarinta a mahangar magungunan gargajiya, abinci, da tattalin arziki. Littafin ya samu jagorancin bayanai daga masana kimiyyar tsirrai, ma’ilmanta a fannin magungunan gargajiya, da kuma manazarta al'adun Hausawa a wurare daban-daban. An yi ƙoƙarin haɗa ilimin gargajiya da kimiyyar zamani domin fito da cikakken hoton darajar wannan itaciya a cikin al'ummar Hausawa.
An raba littafin zuwa babuka huɗu. Babi na farko ya yi magana game da asalin itaciyar zogale da yaɗuwarta a duniya da kuma yadda ta shigo ƙasar Hausa. Ya tabbatar da cewa itaciyar zogale ta samo asali ne daga yankin Kudancin Asiya, musamman ƙasar Indiya da Sirilanka, kuma ta bazu zuwa sassan duniya ta hanyar ciniki da ƙaura. A ɓangare ɗaya kuwa, an yi hasashen hanyoyin zuwan zogale ƙasar Hausa ta hannun mahajjata ko 'yan kasuwa daga Masar, tare da bayyana sunayen da ake kiran ta a yankuna daban-daban na ƙasar Hausa.
Babi na biyu ya kawo itaciyar zogale a matsayin magani. Wannan babi ya yi cikakken bayani game da cututtukan da zogale take magance su. An tattauna a kan cututtuka kamar su ciwon suga, hawan jini, zazzaɓin cizon sauro, ciwon kai, ƙaiƙayin jiki da ido, ciwon haƙora, sanyin ƙashi, da sauransu. Haka kuma, an nazarci yadda ake sarrafa sassan zogale (ganye, 'ya'ya, saiwoyi, da furanni) wajen haɗa magungunan gargajiya, tare da nuna yadda kimiyyar zamani ta tabbatar da ingancin waɗannan magunguna.
Babi na uku ya mayar da hankali a kan gurbin zogale a mahaɗin abinci da ƙwalama. An bayyana yadda ake amfani da zogale wajen haɗa abinci iri-iri kamar dambu, fate, kwaɗo (ɗatu), da miya. An kuma nuna yadda zogale take ɗauke da sinadarai masu gina jiki. Wasu daga, cikinsu sun haɗa da, bitamin, ma'adanan gina jiki, da furotin, waɗanda suke da muhimmanci ga lafiyar jiki, musamman ga mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma yara.
Babi na huɗu shi ne na ƙarshe, wanda ya karkata a kan zogale a muhallin tattalin arziki. Ya yi duba zuwa ga yadda zogale take taka rawa a matsayin hanyar samun kuɗi ta hanyar sana'o'i kamar noman zogale, sayar da ganyen ɗanye, dafaffe, ko busasshe, da kuma sassansa a matsayin mahaɗin magani. An kuma nuna yadda darajar zogale ta hauhawa a kasuwannin duniya, inda ake safarar man 'ya'yanta da garin ganyenta zuwa ƙasashen ƙetare.
Wannan littafin ƙoƙari ne na fitar da hoton muhimmancin zogale a rayuwar Hausawa, tare da bayyana yadda al'adun gargajiya da kimiyyar zamani suka haɗu don inganta lafiyar ɗan'adam da tattalin arzikinsa. Da fatan za a amfana da shi.
