Yaki Da Bara Ta Abu-Ubaida Sani

    YAƘI DA BARA 

    Ta

     Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
    Department of Languages and Cultures,
    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
    ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

    Matashiya

    Tuni bara da roƙo suka kasance tamkar wani ɓangare na al’adun Hausawa a sakamakon ƙaruwar Hausawa mabarata da ake samu. Ba a iya ƙasar Hausa ne Hausawa suke bara ba, har sukan je wasu garuruwa na kusa da na nesa. Wannan al’amari ne da yake ɓata sunan Hausawa a idon abokan zamansu – ko bayan ɗimbin illoli da bara take tattare da su. Wannan waƙa ce da aka shirya domin faɗakarwa ga waɗanda suka ɗauki bara (roƙo) a matsayin sana'a.

    YAƘI DA BARA 

    Bismilla Ubangiji farko na ambace ka,
    Sallu ala Mauhammadin manzo
    Ɗaha naka,
    Alayensa na ha
    ɗa har da sahabu dukka,
    Har mu
    yan ku-ci-ku-ba-mun da muke ta harka,
    Yafe Al-Afuwu sa
    ɓon da mukai gareka.

    Yau magana a kan bara ce ta azazzale ni,
    Kai ne Al-Alimu kama mini don a ji ni,
    Ra-ra-ra na zayyano harshe kar ya ja ni,
    Mai ro
    ƙo da banbaɗa zan so duk ku ji ni,
    Fatana mu tsira don gobe mu samu barka.

    Mece ce bara tukum? Ya aka wagga sabga?
    Ro
    ƙo ne da tambaya mai yi za ya zaga,
    A ba su abinci ko tufa ko naira su
    ƙirga,
    Koko a ta da hannuwa
    ɗai in an ga hanga,
    Sai su wuce hannu fayau babu batun sadakka.

    Mene ne ka sa bara? Ya ci ku tambaye ni,
    Ga jerin silar idan za ku
    ƙida ku bi ni,
    Akwai nakasa a fari zan yo
    ƙarin bayani,
    Kuturta ko kurumta da gurgunta ne tsani,
    Sai a
    ɗale a luluƙa, roƙo za a afka.

    Hausawa suna da camfi zan so ku ji shi,
    Mai baiwa ko nakasa ko tawaya gareshi,
    Allah ya yiwo shi ne yai ro
    ƙo a ba shi,
    Idan kuwa ya
    ƙi yin hakan to hau za ta hau shi,
    Zai ta
    ɓe ya sabbace, kun ji fa wagga hauka.

    Camfin ne ya sa tagwaye suka zamma jari,
    Uwar da ta haifi ‘yan tagwai to ta samu sirri,
    Wai fa hana su saddaka na kawo tujari,
    Ta zaga gari tana baran naira koko gari,
    A ba ta gudun bala’i don wai kar ya auka.

    Sila na bara na biyyu shi ne almajiranci,
    Gudun hijira
    ƙidanya haɗa na huɗun maraici,
    Akwai safara da son rai akwai tsantsar talauci,
    Akwai rabuwar iyaye a aure ba mutunci,
    Sai a rabe a farra
    ƙe har yaya su koka.

    Akwai aure da haihuwar son rai ko jahilci,
    An
    ƙi a tsara tsarin ƙwarai a cikin adalci,
    Yara
    ƙanƙana a tura su bara fatauci,
    Akwai har masu shara gidajen karuwanci,
    Su ke tamba
    ɗewa abin tsoro da shakka.

    Mun yi tara ƙidanmu kar dai lamba ta kuɓce,
    Akwai mutuwa ta zuciya su at cima kwance,
    Ana gado na yin bara tamkar sanna
    a ce,
    Korar
    ɗa ya bar gida koko ɗiya ta macce,
    Dukka sila na yin bara ne, dozin
    ƙidanka.

    Manzo ya faɗi hadith zan yi tuni gare ku,
    Mai tafiya ya yo ice don ya sayar garinku,
    To darajarsa ta wuce masu barar cikinku,
    Fuskar mai bara
    ƙiyama ko ta ga tasku,
    Domin sai
    ƙashi ƙwarangwal ce babu tsoka.

    Mai yi don ya yo kuɗi roƙon garwashi ne,
    Kashedin ar-rasul fa
    ƙat roƙo dai haram ne,
    Sai ga mutum uku ka
    ɗai duk maganar hadith ne,
    Ukun talakan cikinsu sai an samo mutane,
    Sui shaidar ha
    ƙiƙanin ya zamto talakka.

    Hausawa suna da haushi da abin takaici,
    Sun
    ƙi biɗar halaliya sai roƙo da naci,
    An mur
    ɗe wuyar hadith, aya an yi faci,
    An yo fassara dadai son ran makiranci,
    An farlanta yin bara an jera da zakka.

    Manzo zai yi alfahar in ya ga al’umarsa,
    Amma fajiri ina ranar haihuwarsa?
    Ni dai in a nawa ne gwara a yo
    ɓarin sa,
    Ko da ya fito waje gwara a kar
    ɓi ransa,
    Ga shi muna ta girbin abin da mukai ta shuka.

    Bahaushe na da ƙaulin da shi ne yah haɗo shi,
    Idan Allah ya tsaga baki a mutum fa to shi,
    Ba ya hana shi ci da sha don shi ne ya yo shi,
    Kan haka an ta
    ƙarƙare haiƙan babu fashi,
    Bahaushe na ta haihuwar masu bara da
    ɗauka.

    Sun cika titunan ƙasar Hausa fa jarraba ce,
    Har Kudu ma suna zuwa, wannan fallasa ce,
    Wasu a coci ma suke, wannan tamba
    ɗa ce,
    Wassu barin
    ƙasar suke kun san zauɗaka ce,
    Shashashun cikinmu sun sa kimarmu sauka.

    ‘Yan Kudu na ta zolaya roƙon nan sila ce,
    Malam ko a ce aboki kalmar baa ce,
    Ko
    almajiri kawai ba wani kauce-kauce,
    Sui kora da fafarar Hausawa tsiyace,
    Har tsalin zumagiya har da bugu da
    ɗirka.

    Tsummokara jikinsu duk ba zarra na gata,
    Ba wanka ba wanki ba yankan farata,
    Sai
    ƙazuwa da ƙwarƙwata tsabagen ƙazanta,
    Ba bayi matsugguni babu gida a kwanta,
    Sai dai kame-kame nan kangwaye da bukka.

    Akwai ma masu yin hayan yara don su goyo,
    Don a ji tausayin na goyen sam babu wayo,
    Ga yaro mitsittsili ro
    ƙo na ta koyo,
    In ya girma ya
    ƙware maitar ba ta ɓoyo,
    Sai ya
    ɓuge ya rankaya sawu ne ya taka.

    Su ma yara ƙanƙana duk haka za su taso,
    Ba ilmi ba magani ba wanka da soso,
    Su mata a gun bara tabbas babu mai so,
    Sai dai in a yo aro ai
    ɗani a kwanso,
    Ga baiwa marar gata an maishe ta jaka.

    Sun zama karnuka kawai sun koma kucakai,
    Wasu suna da zarrafi sun fa
    ɗa wa son kai,
    Sun hantse a tituna shan rana na sa kai,
    Sun tattara dukiya ga su kamar musakai,
    Har mota suke saya mai safara karauka.

    Wassu suna bara suna ɗan taɓa ɗauke-ɗauke,
    Wassu ana ha
    ɗi da su ƙwaya za a sauke,
    Za su aje su adana har mai su ya
    ɗauke,
    Wassu ko
    yan taadda ne informer a sinke,
    Za su na
    ɗa su zagaya sui sharhi a kanka.

    Yanzu bara tana salo an sirka da ƙarya,
    Za ka ga saurayi tasha ga tari na kaya,
    Zai ce ya fito gari ya yi gamo a baya,
    Yanzu yana bi
    ɗar na mota ne ko ya karya,
    In ka ba shi zagayewa zai yo ya bar ka.

    Wassu suna zuwa masallatai ne su tashi,
    Sui
    ƙaryar wutar balai ce wai ta tashi,
    An musu gobara gidan sai toka da gaushi,
    In ka nemi jin
    ƙwaƙwaf ka yi batun ka bi shi,
    Zai zage ya
    ƙetare don ya guje ganinka.

    Wassu a tituna suke ƙaryar taimako ne,
    Suna cike ramuka kamar dai
    yan agaji ne,
    Idan ba mai ganin su ko sai su yi gefe zaune,
    Idan mota ko ta nufo za su nufo bi
    ɗa ne,
    Sai ka cire ka ba su sunan sun taimake ka.

    Waɗansu salonsu su takardu ne da kati,
    Su ce ma babu lafiya sun zaka assibiti,
    Wassu gidanka za su zo ko su tare a titi,
    Ko a gida na sai da mai ko baki na kanti,
    Take za su yanyame in mota ka faka.

    In ko abinci kas saye yara suts tsare ka,
    Sui maka
    ƙur na mujiya sakkat sun hana ka,
    Mai masa da
    yan bara ruuu za su ishe ka,
    In ma ka yiwo biris ta iya tambayarka,
    Malam ko kana wa almajirrai sadakka?

    In ka saya ka ba su nan to za su kasafta,
    Sui yi gaba su ba ta masar ta ha
    ɗe abarta,
    Ta ba su ku
    ɗi su rarraba saura ribatarta,
    Hakka suke ta zagaye ya zama sanna
    arta,
    Ke
    ɗin har da su bara ɗai ne kunka taka.

    Wanni ko gun siyasa a can ya baje kolinsa,
    Can ne cinsa har da sha can ne sanna’arsa,
    Shi aikinsa media yai ta baje guminsa,
    Yai
    ƙarya ta cin amana don jamiyarsa,
    Allah wadanka ka zamo kaicon al
    umarka.

    Wassu a kan waya suke turowa da saƙo,
    Ko Facebook ko WhatsApp sun maishe su
    ƙoƙo,
    Har lamba na bankuna modern ne a ro
    ƙo,
    Wassu kiran waya kawai za su yi don su mi
    ƙo,
    Sun kwaso matsaltsalu sun jibge wurinka.

    Kuttuna da ɗai kan cikakken saurayi ne,
    Ba ya sana
    a, bai nema, aiki nai zaman ne,
    Kai ka bo
    ƙare kana tashin faɗuwa ne,
    Sai ya taho da
    ɗai kamar neman har da shi ne,
    In kuma ka hana shi to zai yi fushi gare ka.

    Wanni ko kamfani ko matatar haihuwa ce,
    Mata nai guda kaza ‘ya’yan runduna ce,
    Kai ko ka bi sannu don matar ma guda ce,
    Sai ya taho da
    ƙorafin matsaloli ya kwance,
    Kai ka ce gidan akwai fafewa na
    ƙwanka.

    Ni ban ƙi na taimako ware tsiro da gyauro,
    ‘Yan
    ƙarya cikin bara su nika ƙi da horo,
    Sun saka mai ya
    ƙamface dambun ya yi tsoro,
    Su suka sa a yau har marayu ba su moro,
    Su ke cin rabon fa
    ƙirai kafin a farka.

    Mun dai samu mattsala saura mui correction,
    Dole mu janye duk silar kawo confusion,
    Ba sukar a
    ƙida ba condemnation,
    Mur ri
    ƙi gaskiya hadisai muy yo adhesion,
    Kar da mu bar batu na gyara mu
    ɓuge da suka.

    Roƙon nan ya sa mu duk fuskantar derision,
    To mu ha
    ɗe mu sa ƙaimi haiƙan gun repulsion,
    Sannu a hankali batun ro
    ƙo zai corrosion,
    Sai mun
    ɗauki decision mun samar da vision,
    Za mu zamo a tsaftace sak birni na Makka.

    Abin nan ba ya yi sai da hannun itta government,
    Su samar ayyukan yi su kawo development,
    A kakkawo training a kawo improvement,
    Don mun san talauci shi ne duk rudiment,
    Sai tsarmin jahilci idan shi ma ya sirka.

    Aikin malamai kira su ke faɗɗakarwa,
    Ga nan dai hanin hadisai sui fassarawa,
    Sa
    yan media suna babin barbazawa,
    Sai aikin iyaye tarbiyya kulawa,
    Killace
    yan ɗiya gida kalace a girka.

    ‘Yan gudun hijira a al’uma dole a taimake su,
    Bala’i ne ya far musu to mu ji tausayinsu,
    Amma sai a rarrabe kar a shige cikinsu,
    Mu ware gurragurbi nan masu kiran sunansu,
    Za ka ga sun marairaye zamba ce gareka.

    Kowa al’uma rawa nai yai rausayawa,
    A bayar taimako marayu su ai kulawa,
    Zakka in ta zo a yo adalcin rabawa,
    A samu tsaro ya mamaye noma ai kulawa,
    Sai an tara hannuwa za a iya ma jinka.

    Sannu a hankali a sa doka mai hanawa,
    Sai an yo a sannu kar ay yo mur
    ƙushewa,
    Kar a hana su walwala ba za
    ɓin riƙewa,
    Sai an samu adilai gwamnati mai iyawa,
    Don an ba mu arziki sun ka zamo hankaka.

    ‘Yan himman cikinmu Razza’u ka tallafe su,
    Masu barar cikinmu kawo shiriya gare su,
    Raunanan cikinmu hore mana taimakonsu,
    Mahukuntanmu Ar-Rashid gyaro zuciyarsu,
    Kai ke ba da arziki mun ro
    ƙa gare ka.

    Tamat na gode Rabbana nan na doshi boda,
    Kai ne Al-La
    ɗifu kai ne ka saka na ida,
    Ramzi SHATAMAHA za ka iya ka
    ƙida,
    Mai son wa ya yo ku ce mai Abu-Ubaida,
    Ro
    ƙona gare ku fatan samun albarka.

    August, 2026

    Yaƙi Da Bara
    Wakar Yaki Da Bara

    Wakar Yaki Da Bara
    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Yaƙi Da Bara a Kasar Hausa

    Pages