Shawarata Ga Ɗalibai

    Abin da na fahimta shi ne, mutane a kowane mataki sun rabu zuwa kashi biyu game da abin da ya shafi karatu. Akwai waɗanda suka yi imani da shi. Akwai kuma waɗanda suka ɗauke shi a matsayin abin da a Nigerian English ake cewa "formalities." Sau da dama akan samu abin da ake kira "conflict of interest" tsakanin masu waɗannan ra'ayoyi guda biyu a kowane mataki. Misali:

    * Yayin da rukunin farko ke ganin dole ne a dage a fahimci karatu yadda ya kamata, rukuni na biyu na ganin wannan ɓata lokaci ne tsantsa.

    * Yayin da rukuni na farko ke ganin cin mutunci da amanar ilimi ne yin sakaka da harkar karatu yadda za a kasa bambance tsakanin masu hazaƙa da ragwaye, rukuni na biyu suna ganin matsa lamba a wannan fuskar ɓata lokaci ne da tsanani na ba gaira ba dalili.

    * Yayin da rukuni na farko ke ganin cewa fahimtar karatu da tarin ilimi na sauya tunani da halaye tare da tasiri ga rayuwar mutum a jimlace, rukuni na biyu na ganin cewa karatu wani shinge ne kawai na katange mutum daga shanawa da walwala.

    Da sauransu, da sauransu.

    Ko ma a wane rukuni ɗalibi ya kasance, babban shawarar da zan iya ba shi, shi ne, duk yadda za a yi ya kare dokokin da aka gindaya game da dukkannin abubuwan da suka shafi ɗalibtarsa ta kowace fuska. Dokoki da ƙa'idojin jarabawa na da babban gurbi a wannan bagire!

    Ba abin mamaki ba ne a samu ɗalibai da ke shafe dukkannin shekarunsu a jami'a ba tare da karanta abin da ake kira "Students Handbook" ba. Za a yi mamaki idan aka ce ba abin mamaki ba ne cewa waɗansu a tsawon shekarunsu na ɗalibtar ba su ma san da wannan kundin dokoki ba, duk kuwa da suna da lokacin zaman hira da abokai, da na kallace-kallace da musayar saƙonni a kafafen sada zumunta da kuma lokaci na musamman na gulma da tsegumi da hanƙoro irin na waɗanda ke son kitson wance alhali ba su da gashin wance.” Ko waɗanda ke karantawa, ba kowa ne ya san cewa karya doka kowace iriya da ta kasance amintacciya ga muhallin da mutum ke wanzuwa na nuni da raunin mutuntaka da dattijantakansa ba.

    Ko babu waɗansu alƙaluma da suka tabbatar da haka, ina iya iƙirarin cewa ɗalibai ɗaiɗaiku ne suka ɗauki rantsuwa da ake ba su a ranar “Rantsar da Sababbin Ɗalibai” a matsayin wani abu mai muhimmanci ko tasiri. Ga da dama daga cikin ɗalibai wannan rana ce ta cancarewa da ɗaukar hotuna... Wannan ya yi kama kai tsaye da halayyar shuwagabanni da ke ɗaukar rantsuwa da ana iya kwatanta ta da mai bin hayaƙi. A lokutan tsegumin ɗalibai, suna iya tattauna ire-iren rantsuwar da shuwagabannin ke ɗauka tare da take su alƙawarurrukan ba kunya ba tsoron Mahalicci, ba tare da su sun tuna nasu rantsuwa da suka ɗauka ba. Ko da yake, shi ya sa Bahaushe ke cewa “laifi tudu ne...”

    Abin da nake so ɗalibai su fahimta shi ne, duk yadda ake tunanin yanayi ya lalace, akwai waɗanda ba sa fitar da rai – waɗanda sun ji sun gani cewa dole sai sun tabbatar da gaskiya bakin rai bakin fama. Za mu iya cewa suna cikin rukuni na farko. Sun san da cewa alƙawarin aikinsu ba mai bin shanun sarki ba ne, face abin tambaya ne a gare su ranar gobe. Suna da ra’ayin cewa karya ƙa’idar aiki cin amanar alƙawari ne. Sannan sun san da cewa “Sanya ido ga ɓarnar ɓata-gari, mataki ne na naƙasawa da kassara ƙwazon mutane nagari.” Misali shi ne yadda wanda ya sha wahalar karatu ka iya samun sakamako guda da mashiririta yayin da aka yi riƙon sakainar kashi ga lamarin jarabawa!

    Wani babban malamin falsafa ya ce: “Karatun babban mataki na waɗanda za su iya ne, kuma suke da tabbacin za su iya ɗin.” Wanda ya yarda ya shiga makaranta, to ya yarda da dokoki da ƙa’idojin da ke cikinta. Waɗannan dokoki kuwa sun shafi ɗalibai da sauran ma’aikata baki ɗaya.

    Babban rashin adalci ne da son kai da zon zuciya da rashin sanin ya-kamata ga ɗalibi ya yi tunanin an zalunce shi yayin da doka ta yi aiki a kansa bayan ya karya ƙa’ida bisa ganganci da ha’inci. Wanda ya goya masa baya kan wannan, shi ne azzalumi ba wanda ya yi yunƙurin dakatar da ba daidai ba. A sauƙaƙe yadda abin yake shi ne, idan aka kau da ido kan ɓata-gari:

    * An karya alƙawarin aiki kai tsaye

    * An ci amanar dokoki da ƙa’idojin aiki

    * An ci amanar al’umma da ƙasa baki ɗaya yayin da ake gina gurɓatacciyar al’umma mara bin ƙa’ida da sanin ya-kamata

    * Ana rage ƙwarin guiwa ga masu hazaƙa

    * Ana wofantar da ƙwazo da zaƙaƙuranci da jajircewa da riƙo da gaskiya

    * Ana ƙoƙarin samar da al’umma mai rayuwa irin ta dabbobi da babu ingantacciyar doka da oda

    Da sauransu, da sauransu.

    Yana da kyau mutum ya san ‘yancinsa sannan ya san ‘yancin waninsa. Yana da kyau mutum ya san mene ne adalci, mene ne kuma zalunci, ya iya bambance adali da azzalumi daga aikin adalci ko zaluncin da zai aiwatar bisa hujja ta ilimi na hankalin tuwo da kuma musamman a fahimtar addinin gaskiya.

    Ɗaya daga cikin hadisan da ake fara koyarwa a makarantun isalamiyoyi da dama na ɗauke da bayanin cewa: “Gaskiya (halal) a bayyane take, ƙarya (haram) a bayyane yake, duk da a tsakaninsu akwai abubuwa masu ruɗani...”

    A bisa wannan, da sauran bayanai da ban zayyano ba nakan ce: “A riƙe gaskiya da amana da zaƙaƙuranci da aikata daidai” yayin da duk aka tambaye ni SHAWARATA GA ƊALIBAI.

    Abu-Ubaida Sani
    07/07/2023

    Shawarata Ga Ɗalibai

    Pages