Yadda Za Ku Gyara Pi Wallet Ɗinku Da Ya Daina Aiki Ta Amfani Da Passphrase Ɗinku (Pi Network)

  YADDA ZA KU DAWO DA PI WALLET ƊINKU IDAN PASSPHRASE ƊINKU YA DAINA AIKI

  Pioneers ɗin Pi Netwok da dama sun yi koken cewa passphrase ɗinsu ba ya aiki ko ya daina aiki. Idan dai a baya phassphrase ɗin na aiki, to akwai yadda za ku iya gyara shi. Ku bi matakan da aka zayyano a ƙasa dalla-dalla domin magance matsalar.

  1. A ɓangaren saitunan wayarku (settings), ku tabbatar da cewa an kashe Private DNS (wato an saka shi a OFF). A ƙasa an kawo bayanin yadda za ku yi:

  a. A wayarku, ku buɗe wurin saituna (settings).
  b. Ku danna kan network and internet >>> Advanced >>> Private DNS. Idan kuka kasa samo shi, to ku nemi "Private DNS." (ta hanyar amfani da search). Idan har yanzu kuka kasa samun sa, to ku naimi taimakon masana wayar.  c. Ku zaɓi Private DNS Mode: OFF.  2. Ku kashe manhajar burawuzar Pi (Pi Browser App), sannan ku sake shiga ciki ta hanyar Pi App Menu >>> Pi browser.  Yanzu sai ku sake gwada buɗe pi wallet ɗinku ta amfani da private passphrase ɗinku.  👉 Idan kuka kammala wannan, to a cikin saitunan wayarku (phone settings), ku zaɓi Private DNS Mode: AUTOMATIC
  Pages