Yadda Za Ku Yi Amfani Da Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Da Ke Aiki A Kan Kowace Kwamfuta

    Bayan karanta wannan rubutu, ana sa ran ku iya amfani da baƙaƙen Hausa masu ƙugiya (Ƙƙ Ɓɓ Ɗɗ) da ba sa ba da matsala a kan kowace na'ura (kwamfuta, waya, intanet, da sauransu).


    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya

    Yadda Za Ku Yi Amfani Da "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya" Masu Aiki A Kan Kowace Kwamfuta Ko Waya

    Matashiya

    Rubutun Hausa na amfani da waɗansu baƙaƙe na musamman da ake kira "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya." Manyan baƙaƙe masu ƙugiya su ne "Ƙ", "Ɗ", da "Ɓ". Su kuma ƙananan sun kasance kamar haka: "ƙ", "ɗ", da "ɓ". Kasancewar keyboard ɗin kwamfuta bai zo da waɗannan baƙaƙe ba, a bisa dole ake bin matakan samar da su. Waɗansu daga cikin yunƙuri da aka yi na samar da hanyoyin rubuta baƙaƙe masu ƙugiya a na'urori sun yi nasara sannan sun samu karɓuwa.

    Tsarin rubutun Rabi'at da Abdallah su ne suka fi fice a matsayin hanyoyin rubuta Hausa tare da baƙaƙe masu ƙugiya. A dukkannin hanyoyin biyu, akan girke (installing) tsarin rubutun (fonts) a kan na'ura a matsayin Tsarin Rubutu (fonts style). Idan aka girke tsarin rubutun Rabi'at a kwamfuta sannan aka zaɓe shi yayin yin rubutu, kai tsaye za a riƙa yin amfani da waɗannan baƙaƙe:

    i. "X" zai ba da "Ɗ"
    ii. "Q" zai ba da "Ƙ"
    iii. "V" zai ba da "Ɓ"
    (Haka ma abin yake ga ƙananan baƙaƙe).

    Ga tsarin rubutun Abdalla kuwa:

    i. "SHIFT + {" zai ba da "Ƙ"
    ii. "SHIFT + }" zai ba da "ƙ"

    iii. "SHIFT + [" zai ba da "Ɗ"
    iv. "SHIFT + ]" zai ba da "ɗ"

    v. "SHIFT + |" zai ba da "Ɓ"
    vi. "SHIFT + ~" zai ba da "ɓ"

    Naƙasu

    i. Kwamfuta ba za ta iya gane waɗaɗannan baƙaƙe ba har sai idan an girke mata tsarin rubutun a kanta.
    ii. Idan aka ɗora rubutun a wata kwamfutar da ba ta da wannan tsari, to rubutun zai ɓaci.
    iii. Idan aka ɗora wannan rubutu a intanet, to zai ɓaci.
    iv. Dole ne mai rubutu ya riƙa sauyawa tsakanin tsarin rubutu daban-daban idan abin da yake rubutawa ya ƙunshi Hausa da Ingilishi da kuma alamomin rubutu na musamman.

    Cigaba Da Ka Samu

    Abin farin ciki shi ne, kamfanin Microsoft  sun zo da mafita mai sauƙi ga wannan matsala. Akan kira tsarin baƙaƙe masu ƙugiya da suka kawo da suna "Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari" (ma'ana dai waɗanda za a iya amfani da su a kan kowace na'ura).

    Domin amfani da wannan cigaba da aka samu a kwamfutarku, ku bi matakan da aka zayyana a ƙasa:

    i. Je zuwa "Control Panel"
    ii. Buɗe "Language Region" (Ku yi amfani da wurin searching domin nemo shi). Duba hoto a ƙasa:
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    iii. A cikin language region ɗin ku dubo jerin sunayen harsuna
    iv. Daga cikin jerin sunayen harsunan, ku zaɓi "Hausa (Latin-Nigeria)"

    LURA: Nau'ukan Hausa da ke wurin sun haɗa da "Hausa "Latin-Nigeria", "Hausa (Latin-Niger)", da "Hausa (Latin-Ghana)"

    v. Ku danna "Save".

    Shi ke nan!

    Aiki Da Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari A Kan Kwamfuta

    i. Idan kuka buɗe fayil ɗin Microsoft domin fara rubutu, to ku nemo inda aka rubuta "ENG" a "taskbar" na kwamfutar (ko dai a sama ko a ƙasa ko a gefe, ya danganta da inta "taskbar" ɗin kwamfutarku yake).
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    ii. Ku danna kan "ENG" ɗin inda za ku ga wannan:
    HAU Hausa (Latin)
    Hausa Keyboard
    iii. Ku danna kansa
    iv. Yanzu wurin da da aka rubuta "ENG" za ku ga ya koma "HAU"
    Baƙaƙen Hausa Masu Ƙugiya Gama-Gari
    Aiki ya yi!

    Yayin rubuta baƙaƙe masu ƙugiya, ku yi amfani da:

    i. "ALT GR + K" zai ba da "Ƙ"
    ii. "ALT GR + X" zai ba da "Ɗ"
    iii. "ALT GR + V" zai ba da "Ɓ"

    Haka ma ga ƙananan baƙaƙe:

    i. "alt gr + k" zai ba da "ƙ"
    ii. "alt gr + x" zai ba da "ɗ"
    iii. "alt gr + v" zai ba da "ɓ"

    Idan kuna da tambaya ku rubuta a wurin "Comment" da ke ƙasa.

     author/Abu-Ubaida Sani

    journal/Hausa Orthography

    Pages