Pi: Yadda Za Ku Dawo Da Akawun Ɗinku Na Pi Bayan Kun Manta Kalmar Sirri (Password)

  author/Abu-Ubaida Sani

  pdf-https://drive.google.com/file/d/1ryLauLA8iScU2uKIph2hHuds834awcl8/view?usp=sharing

  paper-https://drive.google.com/file/d/1ryLauLA8iScU2uKIph2hHuds834awcl8/view?usp=sharing

  Idan kun mance kalmar sirrinku wanda hakan ya sa ba za ku iya hawa kan akawun ɗinku na Pi ba, to ga yadda za ku dawo da shi cikin sauƙi

  1. Ku Sauƙe Manhajar Pi
  Ku sauƙe manhajar Pi a kan wayarku.

  2. Ku Buɗe Sannan Ku Ɗanna Kan "Continue" (Ci Gaba)
  Idan kuka buɗe shafin farko na manhajar, za ku ga wurin da aka saka Continue with Facebook, a ƙasa kuma aka saka Continue with phone number. Wato ka buɗe da Facebook ko da lambar waya. A nan, za mu nuna muku yadda za ku buɗe da lambar waya ne. Duba hoton da ke ƙasa:
  Continue with phone number

  3. Zaɓi ƙasar da kuke sannan ku sanya lambar wayarku
  Kamar yadda za ku gani a hoton da ke ƙasa, shafe zai buɗe a kan manhajar inda za a buƙaci ku zaɓi ƙasar da kuke, sannan ku saka lambar wayarku. Sai ku zaɓi ƙasarku (misali Nijeriya), a ƙasa kuma ku saka lambar waya. Duba misali a hoton da ke ƙasa:
  Forgot pi password
  4. Danna kan "Password forgotten?" (Shin an mance kalmar sirri?)
  Duma misali cikin hoton da ke ƙasa:
  How To Recover Your Pi Account
  5. Danna kan RECOVER ACCOUNT (MAIDO DA AKAWUN)
  Duba misali cikin hoton da ke ƙasa:
  How To Recover Your Pi Account
  6. Ƙasa da Lambar Waya
  Zaɓi ƙasar da kake domin ka samu lambar ƙasa da ta dace da lambar wayarka (misali, na Nijeriya ita ce +234). Daga nan sai ka saka lambar wayarka wacce da ita ka buɗe Pi. Sai ka danna kan SUBMIT (TURA). Duba misali a ƙasa:
  How To Recover Your Pi Account


  6. Zaɓi ƙasar da kake son tura saƙon SMS
  A wannan gaɓa, za a buƙaci ka tura saƙon SMS ta amfani da lambar da ka buɗe Pi zuwa lambar wata ƙsa. Za ka ga jerin sunayen ƙasashe, USA ke farko. Idan kana Nijeriya ne, to ka zaɓi ƙasar Israel domin saƙo ya fi tafiya zuwa lambar Israel ɗin da wuri. Dun ƙasar da ka zaɓa, to lambar ƙasar za a gabatar maka domin ka tura mata saƙon SMS. Duba misali a ƙasa:
  How To Recover Your Pi Account

  Idan ka zaɓi Israel, zai kasance kamar haka:
  How To Recover Your Pi Account
  7. Idan layin wayar da ka buɗe Pi ɗin da shi yana kan wayar da kake mining ɗin Pi, to kai tsaye za ka tura saƙon ta amfani da wayar. Idan ma layin na kan wata waya ce daban, nan ma za ka iya tura saƙo ta amfani da waccar wayar.
  Idan lambar da ka buɗe Pi da shi na kan wayar da kake mining ɗin Pi ɗin, to ka danna inda aka rubuta OPEN SMS. Daga nan zai kai ka wurin tura saƙon SMS na kan wayarka, inda za ka tura wa lambar Israel waɗansu lambobin sirri da za a ba ka. Duba misali a ƙasa:
  How To Recover Your Pi Account

  Idan lambar wayar da ka yi amfani da ita wajen rajistar Pi na kan wata waya daban, to ka danna inda aka rubuta Manual Instructions  (kada ka danna OPEN SMS). Duba misali:
  How To Recover Your Pi Account
  Daga nan shafi zai buɗe ɗauke da lambar wayar da za a tura wa saƙo, da kuma waɗansu lambobin sirri (Test of the SMS) waɗanda su ne za a tura wa lambar. Kada a manta, a tabbatar da cewa an yi amfani da lambar da aka buɗe Pi ne wajen tura saƙon.
  How To Recover Your Pi Account

  8. Bayan ka tura saƙon, kai tsaye Manhajar Pi zai maka jagora inda za ka saka sabuwar kalmar sirrinka (new password)Duba hoto da ke ƙasa:
  How to recover your Pi account


  A LURA: Dole ne sabuwar kalmar sirrin (password) ta kasance ta ƙunshi babban baƙi da ƙaramin baƙi da kuma lamba, sannan dole ta kasance ta kai harrufa takwas. Misali abcd1234 ba daidai ba ne saboda babu babban baƙi ciki. Haka ma ABCD1234 ba daidai ba ne domin babu ƙaramin baƙi ciki. Amma ABCd1234 da abcD123 duk daidai ne domin sun ƙunshi babban baƙi da ƙaramin baƙi da lamba, sannan sun kai 8.

  Pages