|Articles||Hausa|
Tasirin Fina-finai A Kan Al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi’u Na Musamman a Cikin Fina-finan Hausa
An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo
wajen isar da saƙwanni
ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin
sun shafi ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su
tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon
kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka haɗa da Turawa, da Indiyawa da sauransu.
Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa
suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da ƙwarƙwa
kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da
shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da
_____________________________________________
Na
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
08035605024, 07087765510
Email Address: yagobir@yahoo.co.uk
Da
Abu-Ubaida SANI
Department of Educational Foundations
Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
Phone No. 08133529736
_____________________________________________
Tsakure
An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo
wajen isar da saƙwanni
ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin
sun shafi ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su
tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon
kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka haɗa da Turawa, da Indiyawa da sauransu.
Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa
suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da ƙwarƙwa
kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da
shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da wata sauran alaƙa da al’adun Hausawa. Wannan ya sa
abin ya zama bambaraƙwai
nono da gishiri. Wannan takarda ta tarkato wasu daga cikin ɗabi’u
kamar yadda suke fitowa a cikin waɗannan fina-finai na Hausa. Ɗabi’un sun haɗa
da sutura da magana har ma da halayya. Hakan ya haifar da samuwar wasu miyagun ɗabi’u
tattare da rayuwar al’ummar Hausawa ta yau da kullum.