Post Page Advertisement [Top]

|Articles||Hausa|

Kwatanci Tsakanin Tsakanin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’Na
Abu-Ubaida SANI
Department of Educational Foundations
Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
Phone No. 08133529736
Email Adress: abuubaidasani5@gmail.com
  
Da
 
Mansur Abdullahi
Department of Hausa Studies
College of Education, Ikere-Ekiti
Phone No: 08034402746

Tsakure
Waƙar Lalura da kuma Tabban Haƙiƙan tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dalilai da yawa sun
nuna hakan, musamman idan aka yi la’akari da cewa dukkaninsu an gina su ne kan jigon wa’azi. Sannan baki ɗayansu wallafar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ne. baya ga kamanceceniya ta waɗannan ɓangarori, baitoci da dama a cikin waƙoƙin biyu tagwaye ne ta fuskar abin da suke jan hankali zuwa gare shi. Sai dai bayan wannan kamanceceniya, aikin ya kawo bambance-bambance tsakanin waƙoƙin biyu. Baya ga haka, aikin ya kawo shawarwari game da yanda waƙoƙin biyu za su kasance masu amfanarwa ga ɗalibai da ma sauran al’umma baki ɗaya. Ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi shi ne nazartar waƙoƙin tare da gane saƙonnin da suka ƙunsa, ba sauraro ko karatu domin nishaɗi ba kawai.Adds You May Like