Adashen Ƙauna 4 (B): Halayen A’isha Humaira
  1. 1.      Nai godiya ga maƙagina,
   Da ya sa Humaira na same ki.

   2.      Wace bauta na yo mai kyawo ne,
   Wane aiki nai shin me tsarki?

   3.      Da Allah ya duba buƙatuna-
   A ciki ya ba ni ƙaunarki?

   4.      Humaira wai kin san mene?
   Na sam naso na halinki.


   5.      A da ina kallon kaina,
   Ɗa nake mai halin kirki.

   6.      Ban san ina fa da aibu ba,
   Humaira sai da na same ki.

   7.      A nan na ga kyawun halaye,
   Na gyara nawa irin naki.

   8.      Da farko dai ba kya gulma,
   Don ke kin riƙe bakinki.

   9.      Ba ka giba ba zunɗe,
   Wannan ba ya a halinki.

   10.  Wurin wani ba kya yi da wani,
   Zaɓar kyawun halinki.

   11.  Wurin wata ba kya yi da wata,
   Wannan ma na shaide ki.

   12.  Wurin wata ba kya yi da wani,
   Kowa ma na shaidan ki.

   13.  Wurin wani ba kya yi da wata,
   An ciri tuta an ba ki.

   14.  A’isha wai kin san me ne?
   Kin shero ni da kunyarki.

   15.  Da ma dai Manzo ya sa,
   Kunya cikin addininki.

   16.  Ash’ab kin ma san me ne?
   Kin burgen da kawaicinki.

   17.  Malam ya furta hadisi,
   Ko nan sai da na tuno ki.

   18.  Ya ce kawaici shi ne,
   Cikon halayen kirki.

   19.  A’isha na fara ƙaunar ki,
   Tun da na gane riƙon kanki.

   20.  Ba kit taba kula mazaje ba,
   Kin riƙe dokar Sarkinki.

   21.  Wayyo! Ni kam na faɗo,
   Zan yo zancen nan gun ki.

   22.  A baya na so soyayya,
   Ɗan ɗis ne sha kuruminki.

   23.  Sai kuma hali ya bambanta,
   Silan alfarmar samun ki.

   24.  Hani ga Allah baiwa ce,
   Na ga misali ni kanki.

   25.  To don Allah yafe min,
   Na dai daidaita tafarki.

   26.  Humaira ko da suturarki,
   Na nuna kyawon halinki.

   27.  Hijaban nan dogi naki,
   Da ke rufe sura ta jikinki.

   28.  Kaurinsu ya ko cancanta,
   Daidai umarnin Manzonki.

   29.  Duhunsu ya cika ƙima,
   Ya nuna tsarkin halinki.

   30.  Da a ce dukka Musulma,
   Tana shiga fasalin taki.

   31.  Do alfasha za ta ragu,
   Za a samu mutan kirki.

   32.  Wasu ko na sanya hijabi,
   Amma sun kauce tafarki.

   33.  A fili su nuna na ƙwarai ne,
   A zuci ko a sha mamaki.

   34.  Ke dai kin kauce wannan,
   Allah shi za ya biya ki.

   35.  Humaira mene ne sirri?
   36.  Sinadari na nutsuwarki?

   37.  Ciwon mace ai sai mace,
   Zan nemo alfarmarki-

   38.  Ki sanya aji na musamman,
   Domin koya kalamanki.

   39.  Yadda kike tsaro zance,
   Don mata su yi koyin ki.

   40.  Su ma ko sa ɗan burge,
   Ko sa kwaikwayi halinki.

   41.  Humaira riƙon addininki,
   Shi ne ya ƙaran ƙaunarki.

   42.  Kamun kai da ibadarki,
   Na kasa gane tamkarki.

   43.  Ba ma salla ga kari ba-
   Kushu’in yayin sallarki.

   44.  Nafilfilin da kike tashi,
   Sun ƙara mini ƙaunarki.

   45.  Kin san na miki sunaye,
   Har jaruma na kira ki.

   46.  Duba nai ga ibadarki,
   Azumi jiki ne a gare ki.

   47.  Kyautar da kike yi Hummy,
   Na nuna kyawon halin ki.

   48.  Sadakar nan da kika saba,
   Allah yi za ya biya ki.

   49.  Saliha da na ce ran nan,
   Siffa ce ta ɗabi’unki.

   50.  Kamila da na sanya maki,
   Daidai ne da salo naki.

   51.  Mumina da na ce ko da ke,
   Sharhi ne na ibadunki.

   52.  Natsattsiya na laƙa miki,
   Daidai ne da kamalarki.

   53.  Zance na ƙwarai sadaka ne,
   Ya zan ƙiyasta ladanki?

   54.  Ash’ab wai yaya akai ne-
   Hassada ba ta tsarinki?

   55.  A’isha mene ne sirrin-
   Baƙin hali ba ya ranki?

   56.  Humaira ya kika soma ne-
   Ganin waɗai bai tsarinki?

   57.  Hummy yaya kinka yi ne-
   Ƙyashi ba ya layinki?

   58.  Humaira yaya kika soma-
                       Saurin fushi bai damun ki?

   59.  Hajiya mene mafari ne?
   Abin wani bai damun ki?

   60.  Ke dai kin kama halali,
   Haram ba ya a ajandarki.

   61.  Ina ƙaunar ki Humaira,
   Musamman domin zumuntarki.

   62.  Halin nan na ziyararki,
   Ya ƙara cusan ƙaunarki.

   63.  Fara’arki Babbar Yarinya,
   Ta ƙara sa ni ina son ki.

   64.  Humaira daure da waɗannan,
   Kar da ki sauya halin kirki.

   65.  Da kin haka Allah zai so ki,
   Albarka ko yana ba ki.

   66.  Ki yi mana addu’a kullum,
   Da ke da ni masoyinki.

   67.  Iyaye da ‘yan uwanmu duka,
   Da dukka musulmai ‘yan kirki.

  Pages